GARKUWA PART 3

Cikin tarin jin daɗi Abbansu Sheykh ya matso kusa da Bappa da Abboi murya cike da tarin jin daɗi yace.
“Bappa Abboi dama duk al’ummar Rugar Bani da Rugar Arɗo Babayo ngd matuƙa Ubangiji yayi muka sakayya da gidan al’ljanna mafi ƙololuwa girma.
Shatu Allah ya dafa miki ya tsareki dake da ahlinka”.
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Shi kuwa Bappa Sheykh ya kalla tare da cewa.
“Muhammad Ngd matuƙa Allah ya saka da al’khairi da kulawarka Alhamdulillah ga mahaifiyarku da ƙanwarku Allah ya bamu aron rai da lfy da ikon dawo muku dasu lfy”.
Cikin jin daɗi Ummey tace.
“Bappa dani dasu ya kamata muyi godiya ba kuba kun gama min komai a duniya musamman Alhaji Abboi da matarsa Dedde sun min karar bani yar su duk da tarin son da sukeyi mata, suka amince muka dawo da ita nan, kana suka bawa Jabeer na aurenta.”
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu tare da cewa.
“Kin min komai kin juya min Jabeer daga bauɗeɗɗen mutun zuwa dai-daice gashi yanzu har fara’a yakeyi ga Jalal na shima ya zama mai fara’a Jamil kuma ya nitsu.
Sai dai yanayin Affan nane ke min ciwo a rai, Affan ka dena kuka kajiko Shalelen Mamey”.
Cikin rauni Affan ya matsota ɗaura kanshi bisa cinyarta yayi tare da sakin kuka.
Gaba ɗaya kowa yasan takaicin abinda mahaifiyarsa tayine yake sashi kukan.
A hankali Lamiɗo yace.
“Kayi shiru Affan ita rayuwa kowa abinda ya shuka zai girba”.
Daga nan dai kuma akayi gaishe-gaishe.
Kana mazan duk suka tafi masallaci.
Matan masarautar Joɗa kuwa irinsu Gimbiya Saudatu da Gimbiya Aminatu dasu Mom da Samira duk ko wacce ta koma part ɗin ta cike da al’hinin sharrin ɗan Adam.
Matan kuma duk kowa tai al’wala sukayi salla, kana suka sake fitowa falo suka zauna suna cin abinci.
Affan kuwa Part ɗin shi ya koma ganin tashin hankali da yake cikine yasa Mami meda hankalinta gareshi.
Shi kuwa Rumaisa yayarshi ya kira tana ɗagawa yace.
“Uhummm tunda kullum kece kike zuga Hajia Mama kuna cutar waɗanda basu damu da kuba sai ki shirya kizo kiga halin da Mama ke ciki na girbar aiyukanta data shuka”.
Cikin tashin hankali Rumaisa tace.
“Affan m..”
Bai bari ta ida zancenta ba ya katse kiran.
Su Sheykh kuwa dasu Haroon falon Sheykh Suka wuce.
Bayan anyi sallan la’asar ne,
Dedde ta kalli Ummey cikin kula tace.
“Toh Ummeyn Shatu mu zamu koma Rugar Bani, sai jibi zamu koma Cameroon da izinin ubangiji Allah ya kiyaye gaba ya tsaremu”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Yanzu-yanzu zaku tafine?”.
Cikin nitsuwa Dedde tace.
“Eh ai su tuni ma sun shiga mota nida su Khadijah suke jira”.
Da sauri Umaymah tace.
“Ayyah ni kuwa ina son ku gaisa da Sittinmu da Jadda kafin ku tafi”.
Da sauri Mamma tace.
“Ai sun iso suna Part ɗin Lamiɗo.
Amman yanzu zasu iso”.
Da sauri Shatu tace.
“Toh Dedde am ki ɗan jira ku gaisa mana”.
Suna cikin mgnar Sitti da Jadda suka shigo.
Allah sarki iyaye sai gashi Ummey a tsakiyarsu suna kuka gaba ɗayansu an rasa mai rarrashin wani.
A hankali Sheykh da Haroon suka shigo falon cikin tsiya Sheykh yace.
“Toh Alhamdulillah Jadda ni dai burina ya cika ko yau in kana son tafi ka gaida na gaba tunda kaga Mamey na ta dawo ta sameku cikar farin cikinta kusa mata al’barka”.
Dariya sukayi baki ɗayansu kana su Dedde suka matso aka gaggaisa.
Sannan Jadda ya fita ya koma wurin su Lamiɗo.
Cikin sanyi Shatu ta kalli Deddenta Aunty Amina Hafsi Khadijah waɗanda duk suke cikin shirin tafiya.
A hankali tace.
“Allah sarki da mu ƙara kwana mana, yanzu kuma in kun tafi shikenan sai yaushe ni na zama a nan ina gefe duk ƴan uwa suna Cameroon”.
Da sauri Ummi tace.
“Kema kina tare da yan uwanki ga Ummeynki ta dawo kusa dake ga kuma Junainah gani ga Hibba”.
Da sauri suka kalli Jamil da ke cewa.
“Kuma zan auro mana Khadijah ma ta dawo nan zaku bani ita ai ko Dedde”.
Ya ƙare mgnar cikin yanayinsa na wasa da dariya da kowa.
Murmushi Dedde tayi tare da cewa.
“Ai an baka ma Jamilu”.
Dariya mai sauti yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Junainah kuwa a hankali ta matso kusa da Ya Giɗi tare da cewa.
“Ummey ni dai zan tafi tare dasu Yah Giɗi ban gaji da ganinsu ba”.
Cikin jin kewar juna Ummey tace.
“Kije Junainah nima in Sitti na da Jadda sun tafi zamuzo tasu Mamma”.
Da sauri tace to.
Kana ta kalli Shatu da tai shiru tana kallonta tare da cewa.
“Kada ki damu Addana nima zanke zuwa masarautar Joɗa”.
Da sauri Jalal yace.
“Zaki dawo dai Junnu gamu ga Abbanmu ga Adda Shatunki ga Ummey”.
Da sauri ta kalli Sheykh tare da cewa.
“Toh Yan Junaidun fa”.
Dariya mai sauti Sheykh ya ɗan yi tare da cewa.
“Shima zai dawo nan”.
Nan dai suka fito gaba dayansu dan yiwa su Dedde rakiya.
Jadda kuwa harda kuka yayi yana yiwa su Abboi da Bappa godiya.
A hankali Salmanu wanda yazo wurin ɗan Hafsi ne ya ɗan matso kusa da Ummey ƙasa yayi da murya tare da cewa.
“Ummey ki roƙa min su Abboi a bar mana Hafsi mana”.
Dariya Ummey tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kuce duk ma zamu kwasosu mu dawo nan dasu”.
Da sauri Salmanu ya shiga mota.
Shi kuwa Yah Al’ameen gefen Shatu ya ɗan kalla tare da yafitota.
Bayan Sheykh suna ɗan ratsa a hankali yace.
“Wannan ƙawar taki Rafi’a fa, da batunta yasa su Abboi zuwa gobe zasuje su zanta da manyanta sai jibi zamu koma”.
Cike da mamaki tace.
“Lahh Yah Al’ameen ashe mgnar taku har ta kankama”.
Da sauri yace.
“Ke da Allah ni kada kimin shele”.
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
“Toh sai na gaya ma kowa yaji”.
Da sauri ya biyota ita kuwa cikin dariya tace.
“Ummey ashe Yah Al’ameen da Rafi’a munahikai ne soyayyar sirri sukeyi”.
Dariya Sheykh yayi tare da juya mata ido alamun ai kema soyayyar sirri kikayi.
Haka dai suka shiga motocin suka tafi cikin farin ciki da kewar juna.
Cike da farin ciki suka koma cikin falon.
Da sauri Umaymah ta amshi wayarta da Ishma ke miƙa mata.
Amsa kiran tai da sauri ganin Abbansu Sheykh ne.
“Assalamu alaikum Abban Jazlaan”.
Da sauri Abba dake part ɗin shi ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Toh wai Umaymah ni sai yaushe zan samu in gaisa da Yayar takune kun taru kun riƙe min ita da hira”.
Dariya mai sauti Umaymah tayi tare da cewa.
“A a sai mun koma mana”.
Da sauri yace.
“A a dan Allah kada muyi haka dake, kinga yara na cike nan ki kirata gefe kice mata ina kiranta”.
Murmushi tai tare da cewa.
“Nawa zaka biya”.
Dariyar jin daɗi yayi tare da cewa.
“Kujerar hajji tayi miki”.
Da sauri tace.
“Sosai ma kuwa yanzu kuwa zan cika aiki”.
Tana gama wayar ta yafito Mamey suka tafi ɗakin Ummi ta gaya mata.
Cikin jin kunya Mamey tace.
“A’a kinga dama ke tsiyarki yawane da ita Khadijah ya da girmana kuma ana cike yarana da jikoki ku wani kawo min batun inje gareshi”.
Dariya Umaymah tayi tare da cewa.
“Toh shike nan ni dai yar aikece.
Cikin yanayin tarin shaƙuwarsu ta ya da ƙanwa Mamey tace.
“To ai dai ya bari sai dare ko”.
Da sauri Umaymah tace.
“Ohoh anaso ana kaiwa kasuwa”.
Hararan wasa tayi mata kana ta fito.
Nanfa sukaci gaba da hira.
Ana gab da kiran sallan magriba.
Suka juyo ehu da kururuwar Hajia Mama da faɗe-faɗen da takeyi.
Da sauri Sheykh ya nufi ɗakin daya rufeta, yana buɗeta.
Ta fito tanata yayyarfa hannunta tare da cewa.
“Wayyoooooooo zan zama tsuntsuwar Boleru”.
Da sauri yabi bayanta tuni ta iso falo.
Tana kaɗan yatsun hannunta da sun fara komawa na tsuntsuwar Boleru.
Cikin tsoro da mamaki da tausayi Mamey tace.
“Innalillahi Jabeer kamanninta fa na sauyawa”.
Da sauri ya iso, yana mai kara wayarshi a kunne sabida kiran da yayiwa Affan.
Yana ɗagawa yace.
“Affan kazo kayi maza kazo”.
Cikin tashin hankali da tsoro Affan yace.
“Toh”.
Yana fitowa yayi kiciɓis da Rumaisa a tare suka nufi.
Part ɗin Sheykhhhh.