GARKUWA PART 3

Umaymah kuwa Abba da Lamiɗo ta kira ta gayawa.
Kusan duk a tare suka iso.
A tsakiyar falon suka sameta.
Tana yayyarfa hannunta tare da cewa.
“Na ji daɗi zan zama tsuntsuwar Boleru zanyi ta firewa kamar jirgi”.
Sai kuma ta kalli Sheykh da yake ta karanto Ayatul shifa yana tofa mata. Dariya tayi tare da cewa.
“Kai bar ɓata lokacin ka a kaina ai al’haƙine kuikuyo ya dawo kaina wayyo ni Halima naga ta kaina”.
Da sauri Rumaisa ta iso gareta ihu tasa tare da kururuwar ganin yadda kafafunta duk suka zama cingil-cingil kamar na tsuntsuwar ladin kogii.
Da sauri Rumaisa tace.
“Dan Allah Affan mu kaita gidan bokan ya karya sihirin”.
Cikin tarin takaici da zubda hawaye Affan yace.
“Banza mahaukaciya gafalelliya ni nan Affan babu gidan wani mushirkin mugun kafurin bokan da zanje.
Anayi mata addu’o’in kina batun aje gidan boka”.
Cikin ihu tace.
“Abba dan Allah mu kaita”.
Da sauri Abba yace.
“In kika sake kirana kika haɗani da Allah dan inje inda zan tsaɓa mishi zan tsine miki shasha mara hankali”.
Sheykh ne ya ɗan kalleta cikin sanyi yace.
“Aunty Rumaisa ki bari ki nitsu muyi mata addu’a in sha Allah zata samu lfy”.
Da sauri tace.
“An ƙi ɗin sabida ba uwarka bace ai shiyasa zakace haka”.
Sai kuma ta zaro wayarta ta kira bokan bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga cikin kurma ihu da kururuwa yace.
“Nima ƙonewa nakeyi, ita kuma a haka zataci gaba da rayuwa ita ba mutumba ita ba tsuntsuwar Boleru ba, zata zama aya ta yadda duk wanda ya ganta sai ya tambayi mai tayi. Domin dama shi mugunta ɗan aikene yakan iya dawowa wurin wanda ya aikeshi.
Sai kuma ya kurma ihu da ƙarfi.
A nan ya faɗi yana burburwa.
Ya shiga gudu yana kwaɓe kayansa yana cewa wuta na ƙonashi ya zama mahaukaci tubran.
Ita kuwa Rumaisa kamo Hannun Hajia Mama tayi suka tafi Part ɗin ta.
Lamiɗo kuwa kai ya jinnina tare da cewa.
“Ƙarshen mugu kena”.
Sheykh kuwa da Mamey da sauri suka zauna gefen Affan dayake kuka kamar ya haɗiyi zuciya cikin sanyi Sheykh yace.
“Affan kayi haƙuri ka bar kuka in Sha Allah zamu dage da addu’a zata samu lfy”.
Cikin shassheƙan kuka. Ya tashi yabi bayansu.
Sabida ita dai uwa duk yadda take uwace.
Abba kam juyawa yayi ya fita ko a jikinsa.
Domin shi tausayin Affan ne kawai ke cinsa a rai.
Lamiɗo da Gimbiya Aminatu da Galadima ma kwaffa kawai sukayi suka fita.
Umaymah kuwa cikin zafin zuciya tace.
“Wlh Ni dai ko duk zaku yafe mata ni ba yafewa zanyi ba”.
Da sauri Sheykh ya kalleta idonshi cike da hawaye.
Sai kuma ya kalli Mamma da Aunty Rahma dasu Yah Jafar da suma suke cewa basu yafe mata ba.
Jin an kira sallan magriba ne yasa duk suka miƙe suka tafi masallaci.
Ana idar da sallan Isha’i Sheykh ya nufi Part ɗin Hajia Mama kuka sosai ya sameta tanayi Affan na gefenta shima kukan yakeyi
Addu’o’in ya rinƙa tofa mata.
Har saida yaga tayi bacci kana ya fita.
har yaje bakin ƙofar fita sai kuma ya juyo jin Affan ya ruggumeshi ta baya yana kuka tare da cewa.
“Ngd matuƙa Hamma Jabeer Allah ya bar zumunci da ƙauna”.
Cikin rauni yace.
“Amin Amin Affan”.
Daga nan suka fita kowa yayi Part ɗinsa.
Hira sosai sukayi ranar hirar yaushe gamo kusan sai gab da kiran sallan forko kana duk suka tashi sukayo al’wala sukayi ta nafila suna godewa Allah.
Washe gari da safe gaba ɗayansu suna falon Abba ya shigo.
Suna gaisawa yana kallon Umaymah dake mishi dariya ƙasa-ƙasa.
Hajia Mama kuwa da taimakon addu’o’in da Sheykh yake mata hankalinta ya ɗan dai-dai-ta yadda zata fi jin ciwo da zafin sauyawar halittarta, da gaba ɗaya yanzu kafafunta sun zama na tsuntsuwar ladin kogi, yatsun hannunta kuma sun zama fiffizgewa tsuntsuwar Boleru, idanunta kuwa kamar na tsuntsuwar Duji sunyi ƙuru-ƙuru tamkar an taka kwaɗo.
Wannan al’amarin yasa Lugga da saƙo mutanen masarartar Joɗa shigowa sunayi mata kallon sabuwar halitta masu dariya nayi.
Tsananin tsoron Allah ya wadaci zuƙatan mata da mazan Masarautar.
Bayan Aunty Juwairiyya ta dawone take suffantawa su Mamma yadda Allah ya maida Hajia Mama.
Sosai jikinsu yayi tsanyi.
Umaymah ce ta ɗan kalli Shatu da yanzu ta fito wonka cikin shirin baccinta.
“Naji kamar Jazlaan ke kiranki”.
Umaymah ta faɗa cikin kulawa.
Da sauri tace to kana ta miƙe ta funi Side ɗinsa.
A falo ta sameshi gaban steps ɗin hawa wurin Dinning area.
Hannunshi na cikin zirin zirin igiyoyi dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Daimond.
Wanda a ciki yake liƙe da CCTV camera ta sama wanda da wuya mutun ya iya ganeshi.
Ruggume shi tayi ta baya tare da cewa.
“I miss you so much Sheykh Malam akarmakallu Dr Hamma Jabeer”.
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi kana ya juyo ya ruggumeta.
A hankali tasa tafin sawunta saman rumfar sawunshi kana tasa hannun ta saƙalo wuyanshi.
Ya zama tana lafe a jikinsa.
A hankali ya fara taku a haka ya nufi Bedroom.
Suna shiga ya maida ƙofar ya rufe.
Da cikin tsokana tace.
“Yah Sheykh Haroon”.
Baki ya ɗan taɓe tare da cewa.
“Wannan jarabebben tun yaushe yaja Ƴar mutane suka shiga ɗakin nan suka rufe ko kunya babu”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Mutun da matarsa”.
A hankali ya sunkuyo kan gadon ya kwantar da ita tare da yi mata rumfa da ƙirjinshi kana yace.
“Okay to ai nima gani da matata”.
Da sauri tace.
“Yah Sheykh jego nakeyi, kwana Afreen goma kacal fa”.
Hancinsa ya manna da wuyarta tare da cewa.
“Eh mu samo mata ƙanwa ko ƙani mu samu irin tagwayen Nana Faɗima”.
Da sauri tace.
“Uhum wuya”.
Kissing lips ɗin ta yayi tare da cewa.
“Ke ai yar baiwa ce nine zanke mana laulayi da naƙuda”.
Murmushi tayi tare dasa tafin hannunta ta tallabe kanshi a hankali tace.
“Harda naƙudar ma Yah Sheykh”.
Da sauri yace.
“Sosai ma kuwa ai na Afreen ɗinma ni nayi naƙudar ke ba kallonki kikeyi hankali konceba..”.
Dariya mai sauti tayi sabida lbarta mata yadda yaji a lokacin da karayar da yayi ya ƙara da cewa.
“Mata kuna jin azabar duniya akan hayhuwa bamu da abinda zamuyi muku kuji sanyi sai kyautata muku da nuna muku soyayya in kuna matsayin matanmu iyaye kuwa ayi musu biyayya da tausayawa da kulawa shine kaɗai tukuicin wahalarsu dan bazamu taɓa iya biyansu ba inaji kamar ko wuta Mamey tace in shiga zan shiga dan biyayya sabida azabar da naji wanda nasa irinshi koma fiye da haka taji.
In matsayin yarane kuma mu jiƙansu mu sosu mu kula da amanarsu da Allah ya bamu”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Yauwa niko Yah Sheykh inada tambaya”.
Rigarta ya fara turawa sama yana shafa cikinta tare da cewa.
“Allah yasa na sani Boɗɗona”.
Juyowa tayi ta ɗan kalleshi tare da yin murmushi kana tace.
“In sha Allah ma ka sani”.
Murmushi yayi tare dasa yatsarshi cikin hudar jibiyarta tare da cewa.
“Uhum ina jinki”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Yauwa Dr dama ina son kayi min ƙarin bayani ne kan batun laulayi cikin Afreen da kai tayi.”
Murmushi yayi tare da cewa.
“To ina jinki tambayi in baki amsa in na sani”.
Muskutawa tayi ta fuskanceshi da kyau tare da cewa.
“Bayanin sanadin faruwar haka.
Nake son sani.
Don yana da kyeu mugane dalilin hakan.
Shin yawan shaƙuwace da soyayya tsakanin ma’aurata kawai ke sa hakan ya faru.
Ko kuma wani biology ne na Ubangiji?.
Yake sa miji yayiwa matarsa laulayin ciki a wasu lokuta?”.
Murmushi mai cike da shauƙi yayi tare da cewa.
“Eh wato kina son kiji ba’asin miki laulayi ko irin kin huta ɗin nan”.
Kai ta gyaɗa mishi tare da cewa.
“Eh mana kaga in zakayi ta mana laulayi da naƙuda to ko duk shekara zan haihu ba matsala.”
Lakace hancinta yayi tare da cewa.
“Uhum”.
Kiss ta manna mishi a goshinsa tare da cewa.
“Dan Allah gaya min”.
Zamanshi ya gyara kana yace.
“Toh Aish ba yawan shuƙuwa ko soyayya ba ne ke sa miji yayiwa matarsa laulayi.
Asali ma ai dangantakar ba tsakanin matar da mijin ba ne.
Dangantakar tsakanin ɗan ne da ubansa.”