GARKUWA PART 3

Da sauri Ummey da Inna Amarya suka nufi cikin jirgin bayan sunyi sallama da Abboi.
Basu tafiba saida sukaga tashin jirginsu.
Ƙarshe biyar da rabi jirginsu ya sauƙa cikin Ɓadamaya International airport. riƙe da jakukkunan kayansu suka fito, Junainah na gaba.
Tanata murmushin jin daɗi.
A haka suka iso asalin inda masu taryar matafiyan suke.
Yah Salmanu ku wanda shida Junaidu ne sukazo taryarsu cikin motar Yah Salmanu wanda tuni shima ya samu aikinsa, cikin Ɓadamaya an bashi gida da mota.
Wani irin tsalle Junainah tayi tare da rabkawa Junaidun kira wanda ta hangoshi yanata ɗan dube-dube alamun neman ta inda suke.
Jiyo muryar ta, A tare suka juyo shida Yah Salmanu.
Wani irin murmushi mai cike da tarin jin daɗin Junaidu yayi tare da nufo inda suke gadan-gadan.
Ita kuwa Junainah da gudu ta iso gabanshi, sai kuma ta tsaya tare da sakin murmushi bata abka jikinshi ba kamar yadda takeyi da can baya.
Wani irin murmushi Yah Salmanu yayi tare da cewa.
“Oyoyo My Junnu Allah sarki nesa mai raba masoya, watoma Junaidu kawai kika sani banda ni ko?”.
Cikin jin kunya alamun shekara ɗaya nan data ƙara cikin shekarunta yanzu ta zama yar shekaru goma sha uku hankali da nitsuwa da kunya sun fara zuwar mata, cikin jin kunya tace.
“A a Yah Salmanu na ganka mana”.
Sai kuma ta kalli Junaidu daya karkata kai yana kallonta cikin sanyi yace.
“I miss you very very sorry so much my Junainah”.
Cikin rufe ido tace.
“I miss You to Yah Junaidu, ya jikinka ka worke ko?”.
Da sauri yace.
“Alhamdulillah garauma kuwa”.
Shi kuwa Salmanu da sauri ya isa gabansu Bappa jakukkunansu ya amsa, haka yasa shima Junaidu yayi maza ya amshi na hannun Ummey tare da cewa.
“Oyoyo Ummey na Bappanmu Inna Amarya sannunku da hanya”.
Kusan a tare sukace yauwa.
“Sannu Junaidu”.
Sai kuma Bappa ya kallesu tare da cewa.
“Masha Allah Junaidu na ya girma.”
Ummey kuwa Salmanu ta kalla tare da cewa.
“Kai sannu Salmanu ya bayan rabuwa?”.
Cikin girmamawa yace.
“Alhamdulillah Ummey na munata kewarku Rugar Bani gaba ɗaya”.
Bappa ne ya jinjina kai tare da cewa.
“Muma muna cannedai Amman munata kewarku”.
Ɗaga nan suka nufi inda motar Salmanu take.
Suna shiga suka nufi Rugar Bani.
Kafin a kira mangriba dai sun isa.
Anayin sallan magriba da isha’i matan Rugar Bani suka rinƙa shigowa sunayiwa su Ummey sannu da dawowa da ganin amaryarsu.
Junaidu kuwa ana idar da salla ya dawo nanfa yaja Junainah gefa kaɗan cikin gidan sunata hira, tana bashi lbrin ahlin Abboi yayinda sosai yanzu faransaci ya kama bakinta.
A nan masarautar Joɗa kuwa.
Ana idar da sallan isha’i suna fitowa a kan hanyar komawarsu cikin gidane.
Lamiɗo keyiwa Sheykh batun zuwansu Rugar Bani da Umaymah ta gaya mishi.
Ɗan juyowa yayi ya kalli Lamiɗo jin yana cewa.
“In Allah ya kaimu goben da safe fadawa da bayi zasuyi muku rakiya, ka kuma ɗauki Jalal da Jamil da Umminku”.
Cikin kwaɓe fuska yace.
“Bana wani buƙatar rakiyar bayi da fadawa da hadimai.
Kuma Jamil da Jalal duk yanzu bana son yawonsu na aamu suɗan fara meda hankalinsu sosai kan aiyukansu sun rage zaman gida da yawace-yawace kuma ma ni tafiyata ta sirrice, bana ma son asan Aisha bata gida bare asan inda take, sabida gsky wanna Hankakar Hajia Mama mai farin gaba bakin baya sata iyasa aje can Rugar ayi mata komai, badon dole bama bazata jeba, sabida rugar ba tsaro.”
Jinjina kai Lamiɗo yayi cikin gamsuwa da zancenshi yace.
“Eh to wannan ma hakane ba matsala kuyi tafiyar sirrin ammanfa zakuje da Ummi”.
Kai ya gyaɗa alamun to daga nan sukayi sallama.
Yana shiga falon ya samu ba kowa.
Falonshi ya wuce a nan ya samu Shatu kwance bisa kujera.
Matsawa kusa da ita yayi tare da cewa.
“Ya dai Aish lfy kuwa yau ba hira ina Ummi ina Juwairiyya?”.
Ido ta lumshe tare da cewa.
“Wlh Ummi zazzaɓin mura ke damunta”.
Cikin kula yace.
“Assha subahanallahi tasha mgni kuwa?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh tasha har tayi baccima”.
“Toh Allah ya sauƙa”.
Yace yana zare al’kyabbar jikinshi.
Amin Amin.
Tace tana tashi zaune.
Gefenta ya zauna ganin haka ta ɗan gyara zamanta tasa mishi abinci ya fara ci.
A hankali ta kalli wayarta dake gefenshi ganin ta kawo haske alamun ana kiranta.
Miƙo mata wayar yayi.
Junaidu tace tare da amsa kiran.
Cikin dariya yace.
“Adda Shatu na rigaki ganinsu yau kam gani ga Junainah na, ga Ummey ga Bappa munata hirarmu sanyin hunturu na kaɗamu ga farin wata, Adda Shatu farin cikin Rugar Bani ya dawo kamar yadda kika sani a da can baya”.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah Junaidu nima in sha Allah gobe iwar haka muna tare da yardar Allah, ina my Junnu”.
Da sauri Junainah dake c
jinsu tace.
“Gani nan Addana”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ina Ummey na?”.
“Gata can cikin baƙi”
Junaidun ya bata amsa.
Daga nan ta katse kiran.
Ta juyo da sauri ta kalli Sheykh dake cin abinci.
“Alhamdulillah Hamma Jabeer su Ummey sun iso”.
Cikin sakin fuska yace.
“Masha Allah, Alhamdulillah”.
Da sauri tace.
“Gobe sammako zamuyi ko”.
Ajiye spoon ɗin hannunshi yayi sabida ya ƙoshi gyatsa yayi tare da hamdala kana a hankali yace.
“Aishhhhhhhh ya za’ayi muyi sammako, kin matanta gobe jumma’a ne?
Sai munyi sallan Jumma’a sai mu tafi ko? Please kada kice komai kin ji kiyi haƙuri sai munyi sallan”.
Cikin rashin iya masa jayaya tace.
“To Allah ya kaimu Lokacin”.
“Amin Amin”. Yace
Daren ranar sosai Shatu ta sama mishi gamsuwa iya gamsuwa.
Sai da komai ya lafa kuma ta narke mishi, tare da kamo hannusa ta ɗaura kan ɗan cikin nata daya tattare ya koma gefe ya bawa iyayen nashi dama.
Da sauri ya tashi zaune yana sauƙe numfashin.
Tafin hannunshi ya kife kan cikin.
tare da fara murza wurin a hankali yana dai-dai-ta kwanciyar yaron yana mgn a hankali.
“Afwan Ƴar al’barka gyara kwanciyarki ko, kada ki wahal da Amminki, yauwa yarinyar kirki, Allah ya miki al’barka ya fito dake duniya lfy ya tsareki da kariyarsa ya al’barkaci rayuwar ki ya raya mana ke bisa imani yauwa Kekkyawar jikar Mamey da Ummey”.
Murmushi sosai takeyi ganin yadda yake kalamai masu daɗi akan cikin a hankali tace.
“Yah Sheykh bafa jinka yakeba”.
Murmushi yayi tare da kissing cikin kana a hankali yace.
“Ita Kekkyawar mgn tana tasiri akan shuke-shuken fulawima hakama akan yaron ciki, musamman da mahaifinshi ko mahaifiyarshi, bakyajin duk sanda nake masa mgn yakanyi ta jujjuyawa”.
Ya ƙarashe mgnar yana lakace hancinta.
Daga nan dai yaje yayi wonka haka itama.
Ummi kam sosai mura yayi mata rubdugu.
Washe gari ranar jumma’a kuwa, gaba ɗaya Shatu gani take lokacin baya gudu ta gama shirinta.
Bayan an idar da sallan Jumma’a.
Sheykh ya nufo Side ɗinsa, su Jamil na biye dashi a baya.
Yana shiga ya samu Shatu a falo tana zaune gaban Ummi dake kwance bisa kujera ɓare mgni takeyi tana bata.
Sara kuma nacan kitchen tanayi musu girki.
Cikin sauri ya wuce falonsa jim kaɗan kuma ya fito.
Da sauri ya kalli Ummi tare da cewa.
“La! Ummi bar mgnin nan yanzu zamu tafi Valli dake in duba miki wani mgnin”.
Da sauri Shatu ta kalleshi jin yadda yake mgn kamar hankalinsa a tashe,
Shi kuwa Jamil ya kalla tare da cewa.
“Yi maza kaje ka kira min Baba Ado direba”.
Da sauri Jamil yace to kana ya juya ya fita.
Jalal kuwa Dinning area ya nufa riƙe da waya a kunne yana mgn da Hibba.
Ummi kuwa, to kawai tace.
Shi kuwa Sheykh cikin kula da alamun sauri da gaggawa yace.
“Aish zo”.
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.