GARKUWA PART 3

“Ina bukatar in baka umarni kayi wani abu, ban saniba ko zaka iya min biyayya ko bazaka iyaba”.
Cikin sauri ya kalli Mamey da tace.
“Ni umarni nake so in baka”.
Da rarrafe ya ƙara matsosu cikin rawan murya yace.
“Abba matuƙar dai abin da zaka sani bai saɓawa umarnin Ubangiji da tsarin Addinin Musulunci ba, in sha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka da izinin Ubangiji.”
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe cikin yanayin gamsuwa.
Shi kuwa a hankali ya kamo hannun Mamey, cikin sanyi ya had’a su ya tallafe haɓarshi sai ga hawaye shar-shar suna kwaranya murya na rawa yace.
“Tsawon shekaru goma sha uku ina kuka dare da rana kuka na cikin zuciya, ina so in ganki da idona ma Allah bai bani Dama ba.
Nakanji wani irin daɗi na musamman in Umaymah ta bani umarnin inyi abu kai tsaye, sai inji kamar ban rasa uwar da zata tirsasani yin abinda ya dace ba.
Mameyna bani umarni da izinin ubangiji zanbi zan miki biyayya”.
A hankali tasa hannunta tsakiyar kanshi tare da cewa.
“Allah yayi maka al’barka”.
Da sauri yace “Amin”. kana ya kallesu yace.
“Menene umarninku?.”
Kusan a tare suka haɗa baki wurin cewa.
“Umarninmu shine ka amshi mulkin Masarautar Joɗa, da Lamiɗo yake son yin murabus, ka yarda ka mulki masarautar Joɗa domin kawo gyara da tsari irin na addinin musulunci, Ni Umarnine kai tsaye nake baka”.
Mamey ta kare zancen.
Abba kuwa cewa yayi.
“Ni kuwa al’farma nake nema”.
Abun ya zo mishi amatuk’ar bazata amman kuma saidai umarnin iyaye ya wuce wasa.
Wani irin kukane mai rauni ya kwace mishi, take hawaye ya soma kwarara akan fuskarsa, cikin raunanniyar murya yace.
“Mamey zanyi na amince zan mulki masarautar Joɗa, Abba kaima kace umarnine kawai na amince zanyi muddin hakan zai saku farin ciki”.
Cikin tsananin jin daɗi suka ɗaura hannunsu a kanshi tare da sa mishi al’barka.
Sai kawai ya kife kansa bisa cinyar Mamey murya na rawa yace.
“Kuyi min addu’a da bakunanku masu al’barka, ku roƙa min Allah ya bani ikon zama adalin shugaba mai tausayin al’ummar sa, ku roƙa min Allah ya bani ƙarfin zuciyar yin mulkin, sannan ku roƙa min Allah yasa
kada giyar mulki ta bugar dani, ta sani danasanin muku biyayya ranar gobe kiyama, ku roƙa min Allah yasa talakawa suyi farin ciki da alfahari dani a matsayin shugaban su”.
Ya ilahi ya mujibadda’awati.
Su kansu su Abba tausayin shi ya rufesu, domin yanzu suka gano abinda yasa yake tsoron mulki da gudunsa.
Cikin sanyi sukayi ta jero mishi addu’o’i.
Yana amsawa da.
“Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati”.
Daga nan Abba yayi ta bashi baki da bashi ƙarfin guiwa.
Dole sai kiran sallan la’asar ne yasa suka fito suka nufi masallaci.
Bayan kuma sun idar da Sallah’n sun fitone.
Abba ya sanarwa Lamiɗo da Galadima yadda sukayi.
Sujjadar godiyar Allah Lamiɗo yayi sabida baiyi zaton abun zaizo da sauƙi haka ba.
Shi kuwa Sheykh Part ɗinsa ya koma.
Junainah da Mimi yaran Aunty Juwairiyya ya wuce a falo,
har yaje bakin ƙofar shiga falonshi ya juyo yace.
“Junainah zo”.
Da sauri tace “To”
ta biyo bayanshi.
A falon ya tsaya a hankali yace.
“Ina Adda Shatu ?”.
Cikin sanyi tace.
“Tana ɗakinta”.
Da sauri yace.
“Kuka takeyi ne?”.
Kai ta ɗan gyaɗa mishi alaman “Eh”
Uhummm kawai yace kana yace.
“Jeki”.
Ƙarfe tara dai-dai na dare ya fito daga Bathroom ɗinsa cikin shirin bacci.
Shiru yayi jiyo muryar Afreen nata kuka a falo.
Da sauri ya jawo al’kyabba ya ɗaura akan men sleeping dress d’in dake jikinsa.
Direct parlor’n ya fito.
“Ummi lfy kuwa meke damunta?”.
Yace yana zama kusa da Ummin.
Cikin damuwa Ummi tace.
“Wlh tun ɗazu kuka takeyi,
to uwar kuma Maman ba ruwa, saboda tun shekaran jiya bata wani ci abincin kirki ba”.
Cikin ɓacin rai yasa hannunshi ya amshi Afreen, daketa wawure-wawuren hannunta tana kaiwa baki alamun yunwa.
A kafaɗarsa ya saɓa ta tare da miƙewa ya nufi Bedroom ɗin Shatu.
Ita kuwa Shatu tsananin ciwon kai da alamun zazzaɓin da take jine yasa.
Take turawa Ummi Afreen ita, kuwa sai tsotsan take so.
Sabida ba’a barta tasha yadda take buƙata ba.
Cikin takaici ya tura ƙofar ɗakin tare da yin sallama, sounding a bit harsh yace.
“Assalamu alaikum, ke ina kike?”
Shiru yayi saboda hangota da yayi akan sallaya, ta fuskanci al’ƙibila da alamun salla takeyi ko tayi ta idar.
Rai a haɗe ya zauna abakin gadon yana mai jijjiga Afreen daketa ƙananan kuka, tare da tsotsar yatsarta babba da ciccila ƙafa.
Bisa kafaɗarshi ya sakata yana ɗan jijjigata da hura mata iska a kunnenta.
A take ta fara sauƙe ajiyar zuciya don dama kukan harda rikicin yin bacci.
Da sauri ya juyo kanshi yana kallon Shatu jin kamar shessheƙan kuka take sauƙewa.
Ai kuwa kukan takeyi ta ɗaga hannunta sama kaɗan tana addu’o’in.
A hankali ya juyo ya ƙara matsowa gareta,
cikin tarin takaici ya dawo bakin gadon ya zauna,
wani irin dogon numfashi mai nauyi ya sauƙe kana cikin takaici murya a daburce yace.
“Kuka! Kuka!! Kuka!!! kikeyi har yau har yanzu, duk kukan da kikayi a can bai isheki ba? Duk kukan nuna mishi soyayyan da kikayi bai isheki ba, sai kin dawo min cikin gidana kina min kuka? kina tauye min haƙƙina dana ƴata akan wani can banzan ɓarawo!”.
Da sauri ta juyo ta kalleshi, hawaye na zubo mata ta zuba mishi ido.
Wani irin maƙoƙon kishine da baƙin ciki ya tokare masa wuya, a fizge da ɗan ƙarfi yace.
“In ma ni bakya sona! baki da lokaci na! Bakya buƙatar ganina! Bare ki sauƙe haƙƙina dake kanki,
ai ita dai Afreen ƴar kice kuma tana da haƙƙin ta a kanki ko?
In kuma kinajin duk kin tsanemu ne baza ki iya rayuwa damu da bamu haƙƙinmu ba, dan Allah ki gaya min ba sai kin zauna kina ta min kuka a cikin gida, kina cutar min da yarinya da yunwa ba, sannan kina tayar min da hankali ba,
Ki faɗa min in bakya sona,
In sama miki salama kije can ki auri shi wanda kike so ɗin!!!”
Ya ƙare maganar da ƙarfi. Cike da fushi da zafin kishi.
Wanda har Ummi dake falon ta jiyoshi.
Karo na forko kenan a rayuwar aure su da Shatu da taji yana mata faɗa haka.
Jin hakanne kuma yasa da sauri ta kamo hannun Junainah suka tafi ɗakinsu.
Ita kuwa Shatu cikin rauni ta zuba mishi ido tana mamakin fusatarsa da kalaman da yakeyi.
Shi kuwa Sheykh cikin takaici yace.
“Na sani ai dama ni na sani bawai sona kikeyi ba, dole akayi miki ko? dama shi kikeso!
Wannan abun shi nake gudu da tsoron auren matar da ba sonka takeyi ba.
Amman ba matsala kiyi ta sonshi.
Nima ina da masu sona, kuma zan aurosu, su kuma kular min da ƴata”.
Idanunta da ta zuba masa tad’an lumshe, cikin rawar murya tace.
“Yah Sheyk…”.
Da sauri cikin fushi da zafin kishin ganin son Ba’ana ne yasata wannan kukan.
A faɗa ce ya daga mata hannu cikin tsawa yace.
“Da Allah rufe min baki”.
Yana faɗin hakan ya juya ya fita daga d’akin, still rungume da Afreen akan shoulder dinshi.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce.
Cikin tafasan zuciya ya kwantar da ita can ƙarshen gadon nasa.
Kana a hankali ya miƙe ya zauna sabida azaban tafasar da zuciyarsa keyi.
Ita kuwa Shatu wasu hawayene, masu sanyi suka zubo mata.
Musamman da ta fahimci cewar, zafin kishine ya birkita mata salihin mijinta.
A hankali ta miƙe tsaye, tare da soma takawa ta shige Bathroom.
Ruwan ɗumi kawai ta watsa tare da yin Brush kana ta fito daga cikin toilet ɗin.
Turaren Oud mai daɗin ƙamshi ta shafa ajikinta.
Tare da zura wata royal blue sleeping gown ajikinta mai adon net.
Yayinda kuma har yanzu ta kasa tsaida hawayen dake kwance acikin idanunta.