GARKUWA PART 3

Yanzuma tsaye take a gabanshi yana zaune bisa kujera yana lumshe da ido yana bitar addu’arsa cikin suratul Anfal.
Cikin tsiwa da mamyancen son girma tace.
“Daddy ba Kai nakewa mgna ba”.
Da yake haka suke kiransa kasan cewar sunan babansu gareshi.
Tsaki taja tare da cewa.
“Ina maka mgn ka manna min hauka ina ka ajiye min System na”.
A hankali ya buɗe idonshi ya kalleta, kasan cewar yaje ƙarshen surar.
Murya can ƙasa yace.
“Kifa dena min ihu a kaina, nace miki ban ɗauka ba, bana da shine da zan ɗauki taki argar ma”.
Cikin hatsala tace.
“Ni kake cewa ina ihu Daddy ni mahaukaciyace da zakace ina maka ihu a kai.
Wlh ka fito min da abuna”.
Bakinshi ya taɓe tare da cewa.
“Masifeffiya ba sai kiyi ta yiba”.
Yana faɗin haka ya meda kanshi ya jingine ya lumshe ido alamun zaici gaba da bitar sa.
Aifa ina wuta ta faɗa ciki.
Cikin son girma da tsiwa tasa hannu ta dungure mishi kai cikin ɗaga murya tace.
“Nice ma masifeffiyar ko Daddy, sabida raini”.
Murmushi mai yalwa Sheykh yayi jiyo yadda taketa masifan.
Shi kuwa Jabeer sai yayi mgn kona kusa dashi bai jiba.
Cikin dariya yace.
“Wai Afreen kam meyasa takeda neman rigimane?”.
Da sauri Shatu dake gabanshi tana rage mishi kayan jikinshi tayi kwaffa tare da cewa.
“J baya fa jin mgn wlh shike tsokanarta ƙasa-ƙasa”.
Murmushi Sheykh yayi sabida yana matuƙar jin daɗin sunan da take kiran Jabeer ɗin.
In ba ya ƙureta ba da wuya ta kirashi da cikekkin sunanshi sai dai tace (J) ko kuma Mahmoud.
Cikin ɗan ɗaga murya yace.
“Afreen wai me nene kam?”.
Ya ƙare mgnar yana juyowa ya fito falo.
Da sauri itama Shatu ta biyo bayanshi.
Ita kuwa Afreen dake ta sababi ita ɗaya da sauri ta nufi falon Side ɗinsa da yanzu an bunkasa masa shi akwai ƙofar shigama ta gefe.
Murya na rawa ido na zubda hawaye tace.
Assalamu alaikum.
Cikin nitsuwa ya zauna bisa kujera tare da ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya.
Tare da cewa.
“Wa alaikassalam shigo”.
Ya ƙare mgnar da sanin in ba yace ta shigoba nan zata tsaya.
A hankali ta shigo gefenshi kusa da Shatu ta durƙusa tare da fara mgnar murya na rawa tace.
“Abeey ai Daddy ne ya ɓoye min System ɗina, na tambayeshi kuma yace wai ina mishi ihu a kai, wai ni mahaukaciyace fitsarerriya wai.”
Danne murmushin sa yayi tare da cewa.
“Jabeeer!”.
Da sauri ya miƙe cikin tsananin biyayya ya shigo bayan yayi sallama an bashi izinin shiga.
Gefen Afreen ya tsuguna tare da yin ƙasa da kansa a hankali yace.
“Na’am Abeey”.
Cikin tarin son yaron yace.
“Me yasa zakace mata fitsarerriya?”.
Cikin tanƙwashe wuya yace.
“Abeey ihu take min a kai kuma bitar hadda nakeyi”.
Da sauri yace.
“Na’am wato dai ka gaya mata hakan?”.
A hankali yace.
“Eh”.
Cikin danne dariyarsa yace.
“Bata haƙuri”.
Da sauri ya ɗan juyo ya kalli Afreen cikin sanyi da ladab yace.
“Kiyi Aunty Afreen bazan ƙaraba”.
Cikin yanayin son ɗan uwantaka tace.
“Na yafe”.
Wani irin murmushi yayi tare da cewa.
“Ina system ɗin nata?”.
Cikin sanyi yace.
” Bappa nefa ya ɗauka ya tafi Part ɗin. Mamey dashi.
Shine Khausar kuma tace mata nine na ɗauka”.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
“Toh kinji ko Mamina a rinƙa bincike kafin ayi masifa ko!.”
Daga nan ya sallamesu suka fita.
Jawo Shatu yayi ya ruggumeta gam-gam a jikinshi cikin tarin farin ciki yace.
“Nafi jin daɗi da al’faharin in ganni tsakiyar yaranmu suna rigima ina sasantasu.
Da yanke hukunci nan nake jina a cikekken sarki mai iko da dama da matsayi.
Fiye da in ganni a fada in mulkar masararutar Joɗa dattawa na zama a ƙasa na.”
Cikin jin daɗi tace.
“Na lura ai kana jin daɗin hakan”.
Yatsarshi yasa ya ɗan lakace hancinta tare da cewa.
“Eh mana, sabida su ƴaƴa farin cikinsu nada yawa a rayuwar iyaye.
Duk yawansu bazaka banbance sonsu ba.
Kamar dai tsakanin mata in kana dasu sama da ɗaya.”
Shiru tayi tana kallonshi sabida taji ya saki layin zancen kuma, ta dade da fahimtar akwai abinda yake jimamin sanar mata.
Shi kuwa ganin yadda ta tsareshi da idone ya sashi.
Sauƙe numfashin sa tare da gyara zamanta a jikinshi.
Murya cike da nagarta, kamala, nitsuwa, da tausasawa, yace.
“Kin san meyasa nace miki haka”.
Kai ta jujjuya mishi alamun a’a sabida wani irin tsinkewa da zuciyarta ya fara.
Shi kuwa a hankali yace.
“Bari in miki kekkyawan misali.
Kinga dai Afreen ita muka fara gani muka fara haifa ko.
Ita Allah ya fara nuna mana matsayin ƴarmu ta cikinmu ko?”.
A hankali tace.
“Eh”.
Cikin nitsuwa yace.
“Gud to kinga dole ita muka fara so da sabo da ita da jin farin ciki da ita da buri da fata, da komai a kanta kawai mukayishi tsawon watannin da mukayi kafin ki haifo mana Jabeer ko?”.
Stiil kai ta gyaɗa mishi zuciya na tsinkewa.
Shi kuwa hannunshi yasa cikin rigarta tare da cewa.
“To kuma Alhamdulillah da muka samu Jabeer.
Sai shima muka fara sonshi da begenshi da al’faharin samunshi.
Ba tare da kuma mun dena don ita Afreen ɗin ba ko?”.
A hankali tace.
“Eh.”
Kiss ya ɗan manna mata a saman breast ɗinta kana yaci gaba da cewa.
“Kuma son da mukewa Afreen na forko bamu rageshi ba, saima ƙaruwar da yakeyi sabida tana girma muna ƙara shaƙuwa da ita, son kuma da muke mata bai hana muso shi Jabeer da yazo daga baya ba, har kuma muke jinshi matsayinsu dai-dai da nata.
Sai dai mun san ta fishi girma dole mu nuna mishi ya bata girmanta”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Eh”.
A hankali yace.
“Kuma gashi bayan Afreen da Jabeer ɗin yara huɗu Allah ya sake bamu, kuma duk muna sonsu, son sabbin bai ƙori na tsoffinba ma’ana sonsu Khausar bai kori na Afreen ba.
Ita kuma Afreen sonta bai hana sonsu Khausar ba.
Duk muna sonsu muna ji dasu, sai dai dole babba babbene kuma dole mu sosu tunda Allah ya bamu su.”
A tare suka sauƙe ajiyan zuciya.
Harshensa ya ɗan zaro yana lasar saman breast ɗinta.
Saida yaga ta ɗan nitsu kana a hankali yace.
“Toh wannan itace cikekkiyar misali tsakanin miji da matasan son uwar gidan bazai taɓa hana na amrya ba.
Haka kuma son amrya da take sabuwa bazai taɓa hana son uwar gidan da take sun dade tareba.
Asalima tanada.
Tata kimar da darajar a matsayinta na babba, wannan shine misalin daya kamata duk matan duniya ku gamsu dashi.
Ki dena zaton wai in an auro amarya za’a dena sonki.
Wlh sam ba haka bane uwar gidana.
Ke kuma amarya ki daina gigi da zaton wai ba’a son uwar gidane ko an gaji da ita ko yayinta ya wucene aka auroki.
Wlh sam ba haka bane.”
(Wannan itace falsafa mai kyau, in dai ke ba jaka bace ya za’ayi kiyi zaton dan ya auroki zai daina son uwar gidansa.
Ke kuma uwar gida in banda kishi me zaisa kiyi zaton ke kece sama dake aka fara to ai uwarsa ma na nan kuma bare ke daya sameki rana tsaka da haƙora talatin cas a baki nai.
Dan zai auro wata sai kiyi zaton ai dai nice uwar yayanshi.
To babu ruwan soyayya da uwar yaya.
Ke dai dage ki iya allonki ki wonke.
Da kekkyawan mu’alama amrayar kanta zatafi girmamaki da ganin darajarki.)
Cikin wani irin masifeffen maƙoƙon kishi kumallon mata da kuma tsantsar karantar miji da fahimtarsa murya na rawa hawaye na zuba cike da rauni Shatu tace.
“Allah ya bamu zaman lfy Yah Sheykh, ƙarin aure ba laifi bane.
Allah fa da kanshi ya baku wannan damar”.
Cikin rawan jiki da tausayin rauninta wanda yasan dole taji kishi.
Cikin sanyi yasa harshensa bisa haɓarta a hankali ya fara lasar hawayenta cikin tsananin son da ganin darajarta da yabawa da kulawarta da fahimtar abinda yake son sanar mata.
Shiru tayi tana jin ɗumin harshensa shi kuwa cikin sake mata kiss tako ina yace.
“In bakya so ki gaya min Aish sai in fasa auren.”