GARKUWA PART 3

Cikin gamsuwa da jin sanyi tace.
“In sha Allah kuwa.”
Nan sukayi ta hira maƙota nata zuwa Binto budurwar Ya Gaini tazo haka Hari.
Sune basu shiga sai kusan ƙarfe sha biyu na dare.
Yau ko Junainah batayi bacci ba.
Suna shiga suka kwanta, Ummey na kan ɗaya gadon ita kuwa Shatu ita da Junainah suna kan ɗaya gadon.
Cikin sanyi Ummey tace.
“Uhumm Shatu ya mai gidan naki da mutanen gidan naku?”.
Dogon numfashi ta sauƙe tare da cewa.
“Uhumm Alhamdulillah Ummey yana lfy yace in gaidaki shima zaizo da tarema zamuzo to sai aka kai wasu asibitinsa sunyi hatsiri”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Allah ya basu lfy”.
Amin tace kana a hankali ta gyara kwanciyarta tare da jawo hand bang ɗin ta hannun tasa ta fito da cakuleti masu daɗi ta miƙa Junainah da sauri ta amsa ta ɓare tasa a baki.
Ita kuwa Ummey ta kalla tare da cewa.
“Uhmmm mutanen gidansu kuwa masu cike da sarƙaƙiya da mugunta suna can sunata fama da muguntarsu.
Kai Ummey gidajen sarauta akwai wuyan zama”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Ke dai ki dage da addu’a in sha Allah babu abinda zai sameki”.
Cikin gamsuwa tace.
“In sha Allah kuwa, shima Yah Sheykh yana yawan mana addu’o’in”.
Kai Ummey ta jinjina cikin gamsuwa.
Dai-dai lokacin kuma.
Sheykh ne tsaye tsakiyar falonshi gaba ɗaya ya rasa me ke mishi daɗi.
Tsaki ya ɗan ja, tare da cewa.
“Gidan ba daɗi”.
Sai kuma ya zauna bisa kujera, a karo na biyar ya kuma kiranta stiil bata ɗagaba.
Sabida wayar na sailent kuma tana cikin hand bang ɗin ta.
Allah ya sani ta mance da batun wani suyi waya dashi.
Dogon tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
“Yayi kyau Aish wato kin samu su Ummeynki ni kin mance da nima”.
Haka dai ya kwanta yanata jan tsaki a haka yayi bacci.
Ita kuwa da Ummey kusan kwanan zaune sukayi ranar.
Koda asuba sukayi salla wani hirar suka kuma buɗe wa.
Harda Bappa daya shigo.
Nan ta jawo jakar da Sheykh yace tsarabar Junainah ne.
Tana buɗe wa daga sama ta samu wata leda cike da kayayyakin kwalam na makwaɗaita irin Junainah.
Sai kuma wasu irin tsala-tsalan turame atamfa da Shadda da lashi da hijabai guda biyar-biyar iri ɗaya alamun na Ummey da Inna Amarya.
Sai kuma wasu dogayen riguna masu kyau guda biyar irin na larabawa da alamun na Junainah ne sai dai zasu ɗan mata tsawo kaɗan.
kana sai takalma na manya da kamar na Junainah.
Sai kuma wasu irin yadin Getzner masu kyau kala biyar sai manyan al’kyabba guda biyu da alamun na Bappa ne.
Sai kuma kuɗi a cikin ko wanne kaso alamun kuɗin ɗinkin ne, sai can ƙasar jakar kuma turaruka ne masu tsadar gaske da sabulai da mayukan shafawa.
Ido kawai suke zuba mata.
Ita kuwa cikin jin daɗi tace.
“Gashi inji Yah Sheykh”.
Cikin jin daɗi Junainah ta fara tsalle da ribibi kan kayan zaƙin sam batama kula kayan suturun ba.
Bappa da Ummey da Inna Amarya data shigo musu da karin kumallo kuwa cikin fulaku da kawaicin fulanin kwarai sukace.
“Kai Shatu ya zakiyi ki barshi yayi mana irin wannan hidimar haka”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah Ummey kawai kusa mana al’baka”.
Cikin sanyi suka haɗa bakin cewa.
“Allah ya muku al’baka ya sauƙeki lfy”.
Amin Amin tace tana jawon akoshin ɗumamen gashesshen naman.
Nan Bappa ya fita su kuma suka zauna suka fara cin abinci.
Ranar ma dai haka suka wuni hira, sam ko ta kan wayarta bata biba.
Yauma kamar daren jiya haka sunata hira.
A ɗaki duk da kusan sha ɗaya ne.
Sheykh kuwa a hankali ya fito falo inda Ummi da Juwairiyya suke zaune dan Juwairiyya ta shigo dubata Ummi da jiki a haka nan a hankali yace.
“Ummi gidan shiru ba daɗi”.
Da sauri Juwairiyya ta kalleshi tare da son gimtse dariyarta.
Kana a hankali tace.
“Ai fa kam gidan ba daɗi fa Sheykh”.
Kanshi ya ɗan jinjina kana yace.
“Ummi ki shirya gobe zamuje Rugar Bani”.
Cikin jin daɗi Ummi tace.
“To Allah ya kaimu”.
Amin Amin yace yana mai juyawa ya koma falonshi yana maici gaba da kiran Shatu.
Dai-dai lokacin kuwa Shatu kwance take gefen Ummey cikin kula Ummey ta kalli cikin nata tare da cewa.
“Ya kai wata nawa Shatu?”.
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
“Bakwai”.
Kai ta gyaɗa cikin gamsuwa tare da cewa.
“Masha Allah, zan haɗa miki mgnin zaƙi ki fara sha yana sauƙaƙa naƙuda”.
Cikin gamsuwa tace.
“Toh Ummey na”.
Sai kuma tasa hannunta ta jawo hand bang ɗin ta ganin haske da sauri ta fito da wayarta.
Cikin juya ƙwayar idanunta ta amsa kiran tare da karawa a kunne a hankali tace.
“Assalamu alaikum”.
Wani irin sassanyan numfashi ya fesar tare da cewa.
“Wa alaikassalam yah Aishhhhhhhh”.
A hankali ta ɗan juya ta kalli Ummey tare da yin ƙasa da murya tace.
“Ina wuni”.
Cikin narke fuska yace.
“Aish nayi fushi dake”.
Da sauri tace.
“Na tuba”.
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
“Wato kin samu su Junainah kin mance dani ko? Kin barni da kewa gaba ɗaya gidan ba daɗi”.
“Murmushi tayi tare da cewa.
“Junainah ce take shagaltar dani”.
Da sauri yace.
“Okay to ki shirya gobe da wuri zamu zo ɗaukari”.
A hankali tace.
“A a dai kam Hamma”.
Kauda zancen yayi da cewa.
“Ya Baby na tana Lfy ko”.
“Alhamdulillah tana lfy”.
“Masha Allah”.
Yace kana sukaci gaba da hira
Daga bisani sukayi sallama.
Ita harda Allah gani take zai barta tayi koda mako ɗaya ne.
Koda ta juyo taga tuni Ummey da Junainah sunyi bacci.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya miƙe ya nufi Bedroom yana mmkin tsawon lokacin da sukayi suna hira.
Allah ya sani bai taɓa zato da tunanin shaƙuwarsu ta kai hakaba saida bata kusa dashi.
Washe gari bayan anyi sallan la’asar.
Suna fitowa suka nufi Part ɗin Sheykhhhh.
Suna shiga abincin rana sukaci kana suka fito cikin shiri suka shiga mota.
Jalal ke tuƙi Sheykh na gefensa.
Jamil kuwa na baya kusa dasu.
Ummey kuwa tana can baya sit ɗin ƙarshe.
Waya takeyi da Umaymah tana sanarmata cewa gasu nan kan hanya.
Ƙarfe huɗu da kwata dai-dai suna bakin ƙofar gidan Bappa.
A hankali sukayi parking cikin nitsuwa Sheykh ya buɗe marfin gefensa kana ya zira ƙafarsa ta dama ya fito.
Da sauri Bappa ya miƙe tsaye ganin Sheykh.
Hakama Junaidu.
Shima Sheykh da sauri ya nufi Bappa Jamil da Jalal na biye dashi a baya.
Ummi kuwa yanzu ta buɗe marfin motar ta fito.
Ciken girmamawa Sheykh ya miƙawa Bappa hannu tare da ɗan rusunawa.
Cike da mutumtaka Bappa ya bashi hannun fuska cike da fara yace.
“A a a a masha ALLAH maraba lale marhabin da baƙin kirki kai sannunku da zuwa”.
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gasheshi yayinda Junaidu kuwa ya rusuna yana gaida Sheykh.
Cikin tsananin karramawa Bappa ya juya yace.
“Maraba lale kushi go ku shigo daga ciki.”
Cikin sanyi Sheykh yace.
“Bappa nanma yayi ai”.
Da sauri ya jujjuya kai tare da cewa.
“A a Muhammadu kada muyi haka da kai maza ku shigo ciki, ai nanma gidane”.
Yana faɗin haka ya juya yayi cikin gida.
Dole tasa Sheykh ya bisa a baya.
Kana Jalal da Jamil na biye dashi.
Ummi kuwa na biye da bayansu.
Haka nan sukeji suna mararin shiga cikin gida.
Yayinda gaba ɗaya zuciyarsu ke bugawa da sauri-sauri.
A hankali Sheykh ya sako ƙafarsa ta dama cikin gidan dai-dai lokacin kuma ya yayi ido biyu da….!
By
*GARKUWAR FULANI*
4/6/21, 4:15 PM – &: Ya hango Shatu tsaye a gaban randunansu.
Tana cikin shigar asalin fulani, riga da zanin, rigar guntuwa sai dai tasa wata a cikin red color mai dogon hannun yayinda yadin rigar da zanin kuma fari ne an ƙawatasu da kolliyar zanen ɗawosu, da zaren ulu red, blue and yellow, sosai cikinta ya baiyana.
Ya fito ras