NOVELS

GARKUWA PART 3

Cikin da mamaki take kallonshi.
Shi kuwa Sheykh ido ya lumshe tare da sauƙe sassayan numfashi, sabida tayi masifar mishi kyau Especially kitson kumbo bobini da akayi mata asalin kitsonmu na Fulani kenen.
Murmushi tayi ganin wani irin mayataccen kallo mai cike da bege, shauƙi, kewa, so, kauna, tare da zallan fileeng mai kashe sasasan jiki.
Ita kuwa kai ta ɗan ɗago ta kalli bayanshi hango Jalal da Jamil ne yasata.
Faɗaɗa murmushin ta tare da cewa.
“Lale marhaɓin da Hassan da Hussaini.”
Bappa kuwa bai kula da ita bama sai yanzu da tayi mgn,
Dan sauri ya nufi ƙogar ɗakinshi yana ce musu.
“Kai kunsha hanya kam, masha ALLAH ku iso ku iso.”
Haka yasa suke biye dashi a baya.
Ita kuwa Shatu da sauri ta nufo bakin ƙofar zauren nasu sabida hango Ummi da tayi cikin tsanani jin daɗi tace.
“Lah oyoyo Ummina,”
Ta ƙarashe mgnar cikin jin daɗi da isowa gaban Ummi ta ruggume ta.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da kwaɓe fuskarsa ya tura baki ya mata alamun.
“Wato ni baki ganni bako”.
Harshenta ta ɗan zaro mishi ta gefe.

Kanshi ya juyo da sauri ya kalli gabanshi jin ya ɗan bugi kanshi jikin rumfar Bappa.
Cikin kula Bappa ya shimfiɗa musu babbar taburma, kana ya ware wani ɗan carpet a kam taburmar cike da kulawa yace.
“Bismillah ku zauna”.
To sukace kana duk suka zauna.

Ita kuwa Ummi cikin jin daɗi tace.
“Oyoyo Shatu na, munyi kewarki”.
Cikin dariya ta ɗan janye jikinta, kana tace.
“Ummi mu isa ciki”.
Sai kuma ta juyo da sauri tana cewa.
“Inna Amarya! Inna Amarya gasu Ummi na sun zo”.
Da sauri Inna Amarya dake Kitchen tana gasa musu yan shilan tattabarun. Ta fito tare da cewa.
“A maraba lale marhabin”.
Sai kuma tayi maza ta nufi ɗakin Ummi inda suma Shatu nan suka nufa.

Cikin sakin fuska tace
“Ummi shigo ɗakin Ummeyna”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Toh Shatun Ummey da Ummi”.
Dariya Inna Amarya tayi tare da cewa.
“A lallai kam Shatun Ummey da Ummi fa”.

“Sannu da zuwa Ummi”. Inna Amarya ta faɗa tare da juyawa har taje bakin ƙofar kuma sai ta juyo tace.
“Shatu taho ki kai musu ruwa”.
Da sauri itama Shatu ta miƙa tabi bayanta.

Shiru Ummi tayi bayan sun fita, tana mai bin ɗakin da kallo komai a kimtse yake ras.
Babu hargitsi ko ƙura duk da jeren kayan dake da yawa.
Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi tare da cewa.
“Toh ina Ummeynta ɗin, naji wannan dai Inna Amarya ta kirata”.

Su kuwa Shatu kai tsaye kitchin ɗin suka koma,
Da sauri Inna Amarya ta jawo kwaryan kindar tare dasa maburgi a ciki, ta fara burgashi tana cewa.
“Yauwa Shatu miƙo min ƙwaryar zumar nan”.
Da sauri tace to, kana ta miƙa mata.
Tsulala zumar tayi a ciki, ta burgeshi da kyau.
Kana ta rabashi biyu, sannan ta jawo akoshin data saka furar data gama kirɓawa yanzu.
Ta ɗauki ludayin damu ta fara damawa da sauri.
Sai kuma ta kalli Shatu data jera ƴan ƙananan ƙore guda huɗu bisa tray’n fefeyin saƙa,
damun ta fara zubawa cikin ƙoren kana tace.
“Yauwa Shatu dauki akoshin nan ki haɗa musu da gashin tattabarun naki.
To tace kana ta jawo ƙaramin akoshin tasa na Ummi kana nasun kuma ta barshi a ciki, ta rufe da fefeyin sai tururin da ƙamshin gashin tukunyar ƙasa yake da ƙamshin man shanu.
Bayan sun gama kimtsa komai ne.
Inna Amarya ta ɗauki na Ummi ƙaramar kwarya da damun kidar dai mai binshi zallan nonon da zuma, kana sai akoshin mai ɗauke da gasassun tattabarun.

Ita kuwa Shatu akan fefeyin ta jera ƙoro Ukun ta rufe da fefeyin ɗaya babba kama ta jera kananan ƙoren uku masu zallar nono da zuma suma ta rufesu da fefeyi ɗaya,
Kana ta ɗauka akoshin gashin a sama ta rufe sannan ta jera ludayeyin suma masu kyau da kwalli a saman fefeyin.
Ta ɗauka ta nufi bakin ƙofar ɗakin Bappa inda suke gaisawa.

A hankali tace.
“Assalamu alaikum”.
Da sauri Sheykh ya juyo ya kalleta, ido ya zuba mata cike da bege.
Bappa da Jamil ne suka amsa mata.
A hankali ta zare takalmanta kana ta hau bisa taburmar, gefenshi ta ɗan tsuguna ta ajiye tray’n.
Tare da kallon Jalal daketa kallon tsakiyar gidan yana murmushi da yanayin tsarin gidajen gargajin suna burgeshi.
Jamil ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Ina wuni Adda Shatu”.
Cikin kula tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Jamil ya gida ya Gimbiya Aminatu da Abba da Lamiɗo da Galadima da Aunty Juwairiyya suna lfy ko”.
Jalal ne ya ɗan juyi cikin ɗan sakin fuska yace.
“Alhamdulillah suna lfy, Lamiɗo yace mu gaidaka”.
Ya ƙarashe mgnar yana kallon Bappa.
“Ina amsawa kuwa ngd matuƙa”.
Bappa ya bashi amsa.
Ita kuwa juyawa tayi ta ɗan kalli Yah Sheykh a hankali tace.
“Barka da yamma”.
Cikin sassauƙar murya yace.
“Barka dai ya gida, ina Junainah?”.
Cikin jin daɗin kular da yake kan Junainah tace.
“Yanzu nan ba jimawa suka fita unguwa ita da Ummey na”.
Fuska ya ɗan tsuke tare da cewa.
“To amma meyasa baki cewa Junainah ina zuwaba nasan da zata bar zuwa unguwar”.
Cikin tura baki tace.
“Toh ai ni banyi zaton zakuzo ɗinba”.
Bappa ne ya amshi zancen da cewa.
“Ai kuwa itama Ummmeynkun da ta sani bazata fitaba”.
A hankali Shatu tace.
“Ai magani taje amso min a Rugar Gebi, shine ita kuma Junainah tace sai ta bita.
Amman bazasu daɗe ba”.
Jamil ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Toh ai sai mu ɗan jirasu ko?”.
Da sauri Shatu tace.
“Yauwa ku jirasun”.
Ta ƙare zancen tana turo tray’n tsakiyarsu kana ta kalli Jalal tare da cewa.
“Ga Kidar da gashi mai ɗumi”.
Kai Jalal ya jinjina dan ya gamsu da tsabtan mutanen gidan”.
Ganin hakane yasa Bappa ya miƙa ya basu wuri, yana mai cewa.
“Sheykh kusha tsala”.
Kai Sheykh ya jinjina bayan Bappa ya fita ya ɗan kalli Jalal da Jamil da tuni suka jawo ƙoren bayan sun sauƙe akoshen gashin.
Ido ya zuwa Jamil ganin yadda ya lumshe idonshi lokacin da ya kai damun nan bakinshi, sai kuma ya kalli Jalal da ya matso gaban akoshin tare dasa hannunshi ya jawo ƴar ƙaramar butar Bappa dake wurin ya wonke hannunshi kana ya yago naman mai haɗe da robon man shanu, yasa a baki ido ya lumshe tare da taunawa kana ya haɗiye.
Cikin sauƙe dogon numfashi yace.
“Yah Sheykh kaci wlh yayi daɗi sosai.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
“Aish dubo waiji kisa musu kada su faɗi”.
Dariya mai ɗan sauti tayi kana tace.
“Kaima in kaci sai kayi santi”.
Idonshi ya ɗan zuba mata kana a hankali yace.
“A a aini abinci ɗaya nakeci inyi santi, kuma ba banishi zakiyi ba dan rowa”.
Ya ƙarashe mgnar yana mata nuni da idonshi cewa.
“Kece”.
Da sauri ta kauda kanta tare da cewa.
“To kaci dai”.
Ƙoryar zallan nonon da zumar ya jawo kana yace.
“Toh kije ki shirya kafin mu gama sha ko”.
Da sauri tace.
“Wai tare zamu tafine?”.
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.
“Ai babu wai, in sha Allah yau a masarautar Joɗa zaki kwana”.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah dan Al…”.
Da sauri yace.
“Please dan Allah kada ki haɗani da Allah ki cuceni ki sani yin abinda bana so, Please je kiyi shiri kinji ko Aish dan Allah”.
Cikin sanyi tace.
“Toh zamu jira Ummey ta dawo ko”.
Kanshi ya ɗan sunkuyar tare da cewa.
“Zuwa ƙarfe biyar da rabi zamu jira”.
Cikin sanyi tace.
“In sha Allah ma kafin nan ma, zata dawo”.
Kai ya gyaɗa mata kawai ta juya ta tafi.

Inna Amarya ta samu zaune da Ummi suna ɗan taɓa hira Ummi na shan nono.
Gefensu ta zauna, kana ta kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi kunzo Ummey na bata nan”.
Cikin kula tace.
“Eh yanzu Inna Amarya ke gaya min, ai zamu ɗan jirata”.
Da sauri tace yauwa.

Nan sukaci gaba da hira.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button