GARKUWA PART 3

Bappa kuwa suna gama cin abinci yazo ya musu jagora cikin gida suka gaisa da Inna Amarya kana ya musu jagora har ƙofar gidan Arɗo Bani.
Nan suka zauna anata gaisawa.
Cikin kula Arɗo Bani yace.
“Mun gode sosai da ɗawainiya Sheykh Allah ya ƙara rufa asiri”.
Amin Amin yace.
Kana Alhaji Haro da Umaru suma sukayi godiyar, dan Bappa dasu ya raba yadukan Getzner da Shatu ta kawo mishi, al’kyabbar kuwa ya barwa kansa.
Nan sukayi ta hira har biyar da minti ashirin.
Kana Bappa yace.
“Muje gida ko wata ƙil sun dawo”.
To sukace kana suka miƙe sukabi bayanshi.
A gida kuwa, Ummi ce ta ɗan kalli Shatu tare da cewa.
“Shatu da kin kimtsa kayanki ai kinga magriba tana ƙara towa, kuma nasan bazamuyi salla a nanba”.
Cikin yanayin sanyi tace.
“Ɗazu da safe Ummey tamin wonkin kayana duk suna cikin jaka ma.”
Kai ta gyaɗa tare da cewa Inna Amarya.
“Anya kuwa ba kwana zasuyi a canba”.
Da sauri tace.
“A a wlh da wuya su kwana sai dai garin da nisane.”
Dai-dai lokacin Bappa ya shigo tare da cewa.
“Shatu fito ku tafi dare yanayi”.
Jiki a mace tace.
“Bappa bazamu jira Ummeyna ba”.
Kai ya jujjuya kana a hankali yace.
“A a kuje kawai ba komai Shatu nida kaina zan kawo miki mgnin naga kamar Sheykh ɗin hankalinsa yayi gida”.
Kai Ummi ta gyaɗa cikin takaicin rashin ganin Ummey tace.
“Eh dole hankalinshi zai koma can da yake shike limancin masallacin. Kuma ina sha Allah ni da kaina zanzo amsar mata mgnin”.
Da haka dai suka bawa Shatu ƙarfin guiwa suka taho.
Ita da Ummi a baya, Sheykh da Jamil a gaba Jalal a tsakiya.
Ana kiran sallan magriba suna isa bakin Part ɗin su.
Da sauri Sheykh ya fito ya buɗe gidan ya shiga, dan yin al’wala.
Kana suma suka shigo.
Jalal da Jamil kuwa sukayi side ɗin su.
Ummi na idar da salla ta miƙe da niyar shiga kitchen kenan Sara ta shigo da Foodflaks wanda Gimbiya Aminatu tasa aka shirya musu abinci.
Suna dawowa sallan isha’i sukaci kowa ya nufi makoncinsa.
Shi kuwa Sheykh yana shiga wonka yayi kana yayi shirin bacci.
Shiru-shiru baiga Shatu ta shigoba,
haka yasa ya miƙe ya fito falo, a hankali ya tsaya bayanta.
Ganin ta zaune da alamun waya takeyi da Ummeynta, cikin sanyi tace.
“Ayyah Ummey na, baki dawoba har muka tafi hankalina ya tashi gashi dare yayi kuma baku dawo ba.”
Murmushi mai kwantar da hankali Ummey tayi kana tace.
“Wlh kuwa Shatu na kuna fita, ina isowa, nama hango bayan motarku”.
Sosai shima yaji abinda Ummeynta ta faɗa sabida kanshi da ya sunkuyar ya manna da wuyanta.
Cikin sanyi tace.
“Ayyah UMMEY NA ina Junainah”.
“Gata nan tayi bacci, tun ɗazu wai yau gidan shiru ba daɗi tunda bakya nan”.
Ummey ta bata amsa.
Da sauri tace.
“Ayyah ƴar uwata. To Ummey ya batun mgnin nawa kuma?”.
“Bappanki yace zai kawo miki”.
Ta bata amsa tana konciya.
Daga nan dai sukayi saida safe.
Hannunshi yasa ya juyota ya ruggumeta tsam a jikinshi a hankali yace.
“I miss u so much my dear”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Miss u to”.
Wuyanta ya ɗan sunsuna tare da jawota sukayi cikin bedroom.
A hankali ya kwanta kana ya jawota jikinshi,
hannunshi yasa ya zuge igiyoyin dake ƙasar gaban rigarta murya can ƙasa yace.
“Wai maganin menene Ummey ta haɗa mana”.
Cikin fidda numfashi jin yadda ya kife tafin hannunshi kan Caɓɓulenta tace.
“Wai maganin zaƙine zan zubdashi”.
Da sauri ya zaro ido tare da cewa.
“Na shiga aljanna da izinin ubangiji.
maganin zubda zaƙi kuma Boɗɗona bama na ƙara mana zaƙiba”.
Cikin jujjuya ido tare da dariyar kalmar shi ta na Shiga aljanna da izinin ubangiji tace.
“A a zaƙifa na naƙuda, wai zai sauƙaƙawa mutun wahalar naƙuda”.
Ajiyan zuciya yayi tare da jawota jikinshi,
ya haɗe bakinsu wuri ɗaya, wani irin hott kiss mai cike da bege yake mata.
Daga nan suka narkewa juna.
Washe gari da safe Gimbiya Aminatu da kanta tazo har Side ɗinsu tai mata sannu da dawowa da tambayar mutanen gida.
Hakama Aunty Juwairiyya da Mom.
Yau kwananta uku da dawowa.
Junaidu da kanshi ya kawo maganin nata sai dai kai tsaye Valli Hospital ya kai mgnin ya bawa Sheykh.
Inda kuma nan ya bashi takardunshi ma na neman ci gaban karatun jami’a.
Sosai suke shan hira da Junaidun.
Shida kanshi ya ɗauke shi a motarsa zuwa tasha, inda zai shiga motar Shikan.
A cikin motar ne ya ɗan kalli Junaidun tare da cewa.
“Junaidu ai da kazo mana da Junainah”.
Murmushi Junaidun yayi tare da cewa.
“Malam ai bata sanma zan zoba, sabida in ta sani zatace muzo tare, kuma yanzu nafi son ta meda hankali kan karatunta, kaga dama ta rasa shekara ɗaya tafiyarsu Cameroon”.
Kai ya ɗan jinjina kana yace.
“Zan roƙi Bappa ya bamu ita ai, sai in sauya mata makaranta”.
Cikin kwaɓe fuska Junaidu yace.
“Uhumm Yah Sheykh ai kuwa ni ina tsoro”.
Da sauri yace.
“Tsoron me?”.
Kai ya ɗan kauda ganin sun iso tashan, a hankali yace.
“Kada ka dawo da ita birni tai nesa dani ta manceni wani ɗan sarakuna yayi wuf da ita”.
Murmushi mai yalwa Sheykh yayi kana a hankali yace.
“Astagafirullaha”.
Sai kuma yace.
“A a in sha Allah zan ajiye maka ita, kuma ai kaima yanzu zaka dawo nan cikin birnin”.
Murmushi yayi kana ya buɗe motar ya fita.
Kiranshi yayi ya zagayo ta inda yake, sannan ya bashi kuɗi.
Godiya yayi kana ya tafi, shima yaja mota ya tafi yana mai jin son Junaidun a ransa.
Dan shine ya sanar dashi komai kan Ba’ana da ɓatansu Yah Gaini. Da wulaƙancin da Ɓachamawa ke musu, sai dai iya abin ya sani kawai ya sanar masa.
Daga nan gidan Malam Abubakar ya wuce.
Bayan sun gaisa ne, yake ce mishi.
“Alhamdulillah Malam batun Sulaiman komai zaiyi sauƙi dan yanzu ina neman zama na musamman ne da shugaban SS da kuma shugabsn hukumar ƴan sanda na ƙasa.
In sha Allah gsky zatayi aikinta”.
Cikin jin daɗi, Malam Abubakar yace.
“Kai Alhamdulillah Sheykh Allah yayi maka al’barka ya rufa maka asiri duniya da ƙiyama”.
Amin Amin yace kana sukayi sallama da juna.
Shine bai shigo gidaba sai bayan sallan isha’i.
hannunshi riƙe da ledan magungunan da aka haɗawa Shatu wanda na zaƙine kuma yana sauƙaƙa naguɗa da izinin ubangiji.
(Ganyen bishiyar Ceɗiya, Dirim, Ganyen Barma Gada ban san sunanshi da Hausa ba, sai kuma zobo.
Sai cikinki ya kai wata bakwai zaki tafa sasu sai ki rinƙa shan ruwan, da zaran cikinki ya shiga wata takwas sai ki bari.
Sai randa duk kikaga alamun naƙuda sai kiyi maza ki tafa kiyi ta shansa da ɗuminsa, da izinin ubangiji wlh wani kafin ma mgnin ya tafasa da yardar ubangijin sammai da ƙassai zaki haihu lfy.
Yana sauƙaƙa nakuɗa sosai.
Ki haifo ɗanki lfy ƙato kuma jazir kamar ɗan larabawa da izinin ubangiji)
A hankali ya shigo cikin falon inda take zaune Ummi na gefenta.
Gefenta ya zauna tare da miƙa mata ledar.
Hannu tasa ta amsa tare da cewa.
“Ngd matuƙa Allah ya rufa asiri”.
Cikin jin daɗi yawan addu’ar da take masa in ya bata abu koda bata san komai bane yace.
“Amin Amin”.
“Na menene?.” Ta tambayeshi a taƙaice.
cikinta ya ɗan kalla tare da cewa.
“Magungunan da Ummey ta amso miki ne”.
Cikin sauri tace.
“Bappa yazo ne”.
Kai ya jujjuya mata alamar a a.
“To kaine kaje”.
Cikin wasa ya gyaɗa mata kai alamar eh.
Baki ta ɗan turo gaba tare da cewa.
“Shine ko kaje dani Hamma Jabeer”.
Murmushi yayi yana miƙewa tsaye yace.
“To banine najeba Junaidu ne ya kawo minshi har Valli”.
Cikin fidda numfashi Ummi tace.
“Niko da har ina cewa gobe Jamil zai kaini mu amso”.
Yana mai nufar ɗakinsa yace.
“Ato Junaidu ya hutasshe mu”.