GARKUWA PART 3

Daga nan ya tafi, ita kuwa Ummi amsar mgnanin tayi taje kitchin rabashi biyu tayi ta tafasa mata rabi ta tace mata shi, ta tasa mata a ɗan madaidaicin bokatin roba mai marfi ta rufe, ta kawo mata.
Kana ta ƙulle saura kuma.
Daga ranar ta fara sha.
Alhamdulillah komai na tafiya dai-dai yanzu cikin Shatu yayi watanni takwas cib, duk bayan sati biyu zai ɗauketa suje Valli Hospital ayimata awu su dawo gida.
A hankali komai ke tafiya yanzu cikin ya shiga wata na tara.
Yau asabar ne ba aiki shiyasa yake hutu in banda zuwa Masallaci ba abinda ke fiddashi.
A hankali ta shigo riƙe da tray’n abincinsa.
Da sauri ya tashi tsaye, maƙale da waya a kunnenshi bisa alamu da Umaymah yake mgn. Ajiye tray’n yayi tare da jawo hannunta bisa kujera 3 str suka zauna.
Matsawa can ƙarshen kujerar yayi, kana ya sunkuyo ƙasa hannunshi yasa ya ɗago sawunta da yanzu sun fara ɗan kumbura, kan cinyarsa ya ɗora sawun nata.
A hankali yasa kafaɗarshi ya maƙale wayar da yakeyi kana a hankali yasa yatsunshi ya ɗan fara mammatse mata sawun.
Cikin nitsuwa ya ɗan kalleta kana a hankali yace.
“Uhum gata nan ma. Umaymah gashi naga yanzu ƙafafun nata sun kumbura sosai mafa, bataji saitayi ta zama bisa kuje ƙafar a ƙasa.”
Cikin kula Umaymah tace.
“Amman dai ba wata matsalar ko?”.
Da sauri yace.
“A a ba komai tana lfy baby ma na lfy”.
hannunshi yasa ya gyara mata konciyarta, ganin ta mirgina ta konta.
“Yaushe ne EDD’nta?”.
Umaymah ta tsmbayeshi
Cikin nitsuwa yace.
“Saura mako uku”.
murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah kaga kuwa su Mamma da Aunty Rahma ma suna gab da zuwa dan jikin Jadda dake yawan tashin masa yace, yana buƙatar ganinmu baki ɗayanmu to zasu zo nanda sati ukun, amman banda yaransu”.
Cikin nitsuwa yace.
“Uhumm tsohonan da tsoroba so yake ya ruɗar mana daku yana komai kamar mai barin wasiyya, ni tun zuwanmu auren Haroon sai wani cewa yake ko bayan ransa kaza da kaza zaiyi kaza, to ni dai fatana Allah yasa Mamey na ta ƙara haɗa ido dashi kafin ya tafi”.
Ya ƙarashe mgnar cike da rauni da kuma ƴar raha.
Cikin rauni Umaymah tace.
“Kaci gidanku ai kaima Abbanka zai tafi”.
Numfashin ya ɗan sauƙe still ysnayiwa sawunta tausa.
Saida suka gama waya da Umaymah ya yunƙura zai ajiye wayar kenan.
Wani kiran ya shigo wayarshi yana ɗaga yaga DSS.
da sauri ya amsa tare da cewa.
“Hello sir barka da dare”.
Yaƙi in sallama sabida sanin kafurune bisa lfyn.
“Barka dai Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa.”
Murmushi yayi jin oganshi a fagen aiki ya kirasa da cikekken sunansa.
A hankali yace.
“Sir barka da dare”.
Cikin hausar arnataku yace.
“Kai Sheykh, kai da yan uwan Sulaiman kun hanamu bacci da yawan Addu’o’in kuna gigitamu da addu’a dole mu fito da shiko”.
Cikin dariya da kekyawar mu’amala yace.
“Sir ba dole muyi ta Addu’o’in ba, tunda bamu da kowa sai Allah da Manzonsa bamu da mai bi mana bayan gskyr masu gskyar da ake tozartawa.
Ya zamuyi sai mu haɗaka da Allah”.
Cikin dariya shugaban hukumar binciken ƙasa na sirri yace.
“Gsky to ku barni inyi bacci, kuzo ayi mgnar belinshi, nayi mgn da wanda case ɗin yake hannunsa.
Yace shima duk sanda zai bacci sai yaga Sulaiman da wasu yara sunata kuka, suna salla da addu’a kuma da zai sa a duba hakan za’a samesu.
Ni kuwa kwarjin Sulaiman na min yawa ko naje da niyar bincikarsa sai inji ban gamsu cewa shi mai sayan kayan sata bane”.
Wani irin sassanyan numfashi ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah to yanzu wacce rana zamuzo ayi mgnar belin”.
Cikin sauri yace.
“Next to weeks”.
Da sauri yace.
“Allah ya kaimu”.
Daga nan sukayi sallama.
Addu’a’u saifulmumini kenan
Gashi suda kansu sun nemesu.
Nan take ya kira malam Abubakar ya sanar mishi komai.
Bayan sati ɗaya, wanda ya kama saura kwanaki ne cikin Shatu ya cika wata tara.
Kuma Alhamdulillah komai na tafiya dai-dai.
A hankali suke tafiya lokacin da suka fito wurin awun.
A nitse suka miƙe ɗan corridor’n har cikin Office ɗin shi.
Bisa tattausar kujerar dake gefe ta zauna tare da sauƙe numfashi tace.
“Gsky Yah Sheykh yanzu kam fa na fara jin nauyin cikin nan, in zan ɗaga kafata sai inji ya tokareni”.
Goron ruwan faro mara sanyin daya ɗauko ya miƙa mata, tare da cewa.
“Eh dole kiji haka yanzu tunda cikin yayi ƙasa. Alamun haihuwa yau ko gobe ake cewa ko?”.
Rufe goran tayi bayan tasha mai yawa kana a hankali tace.
“Uhummm ni naƙuda kawai nake tsoro in badon shiba ni Ko yauma in haihu mana kawai in huta”.
Sunkuyowa ya ɗanyi yayi kissing goshinta a hankali yace.
“La, la, la kada ki damu ke kam Aish na ƙudarma ni zan miki kinji”
Yayi mgnar cikin wasa da kwantar mata da hankali.
Da sauri tace.
“Allah yasa haka”.
Amin Amin yace cikin murmushin.
Sai kuma ya fara tattare ƴan abubuwa shi dan zasu wuce gida.
Yana gamawa suka fita suka tafi.
Yau asabar Sheykh ne zaune gaban Malam Abubakar da Lamiɗo da Galadima dan Malam Abubakar ɗin ne yazo har gida a nitse Sheykh yace.
“Toh Alhamdulillah Malam in Allah ya kaimu gobe.
Ƙannen maman Sulaiman Ya Adam da Ashiru su shirya suje. Abuja su kai kuɗin beli kamar yadda suka faɗa. Naso inje to kuma abubuwa sun min yawa.”
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai kana a hankali yace.
“Sai dai kuɗin belin ne wuyar 3 million da sukace”.
Kai Sheykh ya ɗan ɗago tare da cewa.
“Eh ba damuwa na turawa Ashiru kuɗin a accutan ɗinsa in suje su cire suje musu da kash”.
Cikin jin daɗi Malam Abubakar yace.
“Kai Alhamdulillah Muhammad Allah yayi maka al’barka Ngd matuƙa”.
Amin Amin sukace kana sukaci gaba da wata hirarsun.
Alhamdulillah kuwa su Ashirun sunje lfya ranar Monday sun bada belin Sulaiman sun dawo lfy yan uwan shi mata kamar zasu mutu dan farin ciki.
Cikin Shatu kuwa gaba ɗaya ya sauƙo yayi ƙasa a hasashen likitoci sauran kwana takwas ta haihu.
Yau ta kasance ranar jumma’a ne.
Tunda safe Sheykh yayi shirin jumma’a’arsa.
Da sauri ya fito falonshi sai baza ƙamshi yakeyi.
Wani tattausan yadine a jikinsa lemon green mai masifar kyau yasha aiki da farin surfani.
Gariyar tayi cas da jikinsa.
farin hula mai ratsin lemon green ya kafa bisa tattausan gashin kansa.
sai takalminsa sau ciki shima lemon green.
Da sauri ya ɗan ja da baya ganin ya kusa yayi karo da Aish ɗinsa da cikinta da ya fito sosai yayi kuma ƙasa sosai in ka ganta har kamar ta ɗan rame.
Cikin kula tace.
“Hamma Jabeer fita zakayi ne?”.
Motsota yayi a hankali ya ɗan ruggumota kana yasa hannunshi ya ɗan shafi cikin a hankali yace.
“Eh fita zanyi Aish ina son inje gidan Malam Abubakar dan mu gana da Sulaiman tunda ya dawo shekaran jiya ban samu mun naje na masa jajeba”.
Cikin fidda sassanyan numfashi tace.
“To zaka dawone kafin azahar”.
Kai ya jujjuya alamar a a.
Manna kanta tayi da ƙirjinsa kana a hankali tace.
“Toh kuma zanje makaranta fa, zan shiga aji daga ƙarfe sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya zamu gama takardun da suka rage mana”.
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da cewa.
“Wannan makaranta ni dai tana cimin rai”.
Cikin sanyi tace.
“Toh ai ma mun kusa samun hutu yau last page ɗin ezam ɗin zamuyi”.
Kai ya ɗan sunkuyar ya manna hancinsa a wuyanta a hankali yace.
“Toh yanzu muje in kaiki da kaina in na sauƙeki sai in wuce gidan malam kuna tashi inzo in ɗaukiki in dawo dake, nasan kafin nan kuma lokacin salla yayi.”
To tace kana taje ta shirya.
Ta zurma ƙaton hijabi.
Haka kuwa akayi yana sauƙeta saida ya tabbatar ta shiga aji lfy kana, ya juya ya nufi gidan.
Malam Abubakar.