NOVELSUncategorized

AHUMAGGAH 13

_*♡AHUMAGGAH????*_
   _A nigerian historical fiction_           
   *WATTPAD SURAYYAHMS*_        _Brilliant writers association_
 _Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence_




_Bismillahirrahmanirrahim_



_1⃣3⃣land of Aryans_


*KHALDUN SA’OOD!*


18h 40min flight Khaldun sa’ood ya dauka a duka duka cikin kasashen dake zageye da south eastern asia.

A hakan ma bai samu isa wajen kishiyar mahaifiyar san ba Sabida wani urgent secret mission daya taso masa wanda yake saka ran zai dauke sa kusan watanni shida batare da ya kira ko ankira shi.

A Chan gidan kuwa sun saka rai sosai akan zuwan nashi sai gashi sunji shi shiru kuma babu wani labari.

Sai ya zamto dole ma Gen alhj hamood yayi niyyar barin US zuwa iran,dan dama shikadai ke da masaniya akan haka

A yau tun Karfe 6 na safe ya dauko hanyar sa zuwa kasar iran domin fayyace ma kakkanin na sa halin da ake ciki
Dan yafi kowa sanin yadda iyayen nasa suka dauki son duniya suka daura akan khaldun

 Wanda shikansa ya san in awaya zai musu bayani bazasu fahimce shi ba ko kadan.

*Little lorestan 1316 bc:*

Little lorestan wata yanki ne dake cikin wata babban dawla a duniya mai taken the persian empire.

Kamar yadda a duniya akwai roman,greek da italian,haka ma Persian empire ya kasance babban jigon tarihi daya miko zaren sa daga yankin egypt har zuwa yankin greece.

Persian empire Yanki ne na al’ada da tarihi wanda ya hada manyan Kasashen musalmai kamar:
Asalin cikin kwaryan kasar iran
pakistan,afhganistan,india,da uzbeniskhan.

A tarihin daulan tun gabanin 7th century ad, mutanen su na da chan da suka rike al’adu da tarihin daular suna kirar daulan da suna” *land of Aryans’*:
(adopted in 1935)

Wanda a yanzu a duniya shine aka dunkula ake kira da suna kasar iran,wasu kuma suna ce dashi islamic republic of iran mai kimanin 82 billion inhabitant and the 17th lagerst country in the world curently.

Toh acikin yankin little lorestan anyi wani babban shaharraiyar masaurata mai suna the khorshidi dynasty.

Masarauta ne na sarki izz id deen muhammad izz deen,wanda Allah ya karbi ransa a shekarar 1316.

Da Ya mutu sai ya bar sarautan sa gaba daya a hannun matar sa mai suna dawlat khatun.

The same shekarar 1316 matar san da ake kira DAWLAT kHATUN ta amshi ragamar mulki and she become the 12th ruling queen of persia.

Sai dai kuma daga nan akayi rashin sa’a domin kuwa darajar daulan gaba dayan ta yafi karfin mulkin da mace zata rike bare ta gudanar.

Dan Da komai ya koma hannun ta tuni ya fara lalacewa musamman ma wajen tsarin mulkin daulan.

Hakan ya zame ma daulat khatun bata da wani mafita face ta yanke hukunci mai karfi wanda da zai ceto empiren ta darajar mulkin mijin ta baki daya. 

‘Hakan ya sa sarautar ta da mulkin ta baije ko ina ba sai ta sauke taken mulkin ta daura ma kanin mijin ta mai suna izz ideen al hassan izzideen,daga haka har darajan mulkin yayi ta ninkuwa yana karfi har aka zo zamanin ta da wani sarki mai suna sayful maluku..

“Daulat khatun kyakywiwar mace ce,tana da foster sister wanda take matukar kauna  mai suna badiatul jamal,

Wato yar gidan wanda ta shayar da ita ta kuma raine ta kenan 

a wani tarihin an ce daulat khatun  yar asalin zuriar da ya fito ne tun daga zamanin Annabi suleiman AS.!

“Dan haka Mace ce wacce ta gaji arziki mulki da sarauta,sai dai ita sam bata da sa’a akan soyayya.”..

Toh a Lokacin da zamani ya kawo ta mulkin sayful malik,daulat khatun ta kasance idon zakara a persian empire domin kuwa tayi karfin iko sosai wanda har kusan kowa ya fara juya ma akalar ta baya.

 domin kuwa da yawa anyi bakancen cewa gurbatacciyar soyayyar dake wakana tsakanin ta da sarki sayful maluku shi ya jawo ragwabewar mulki da sarauta a daulan daga zamani zuwa zamani.

Da shike ragamar gundarin mulkin na hannun daulat khatun ne sai ya kasance Sarki sayful malik ya maida kansa bawa ga mumummnan soyayyar ta.

Anan ya watsar da duk wani jarumtar sa da ikon sa ya kuma bada baya akan komai bashi da wani aiki sai bin maganan daulat khatun akan soyyaya, gata da kishi sosai dan bata taba bari wata mace mai kyau ko marar kyau ta hade ido da shi ba sai sister ta badia.

Itama badian sau daya ta kalle sa a bisa umarnin ta.

anan ma daulat ta riga ta bada sarki seif doka cewar kallon shi da yar uwanta badia shud be in just one glance kuma hakan ne ya faru.

daga baya tarihi ne Ya bayyana cewa har zamanin su ya gushe suka shude daulat khatun bata bar sarki seif ya sauya tsarin wannan mumumnan mulki ba.

hasali ma badia’tul jamal yar uwan ta ce kawai take goyon bayan Su baki daya a daulan

Rayuwar badia da yar uwan ta khatun akwai banbanci, amma har suka shude suka bar duniya badia bata taba ganin gazawar yar uwanta ba .cikin tsananin biyayya da kaunar junan su suka gudanar da rayuwar su ta duniya har bazaka taba cewa ba a ciki daya suka fito ba.

Toh Anan little lorestan har wa yau akwai jinin Zuriar daulat khatun da yar uwan ta badiatul jamal dake rike da ragamar khorshidy dynasty.

Ayayin da zamani Yake ta shudewa yana kuma sauya salo zuwa zamanin kimiyya da fasaha

 Zurian daulat khatun da yar uwan ta badia ne yayi linking har aka iso kan masauratan daya haifi dansu mai suna Gen Alhj hamood mufaddal clive Wato mahaifin khaldun sa’ood.

Gen alhj hamood dan gidan wata sarauniya ce da ake cewa malika reemah el sheik wacce itama kamar ya ce a zuriar badiatul jamal.

Kasancewar badiatul jamal foster sister daulat khatun ne,sai mulki da sarauta bai zamto daya daga cikin gadon ta ba.

Amma kuma awannan zuriar nata sai malika reemah elsheik ta auri dan sarkin afhganistan inda suka haifi mahaifin khaldun saood.

Gen hamood kuwa tun yana jinjiri plane crash yayi sanadiyar iyayen sa..

Inda rainon sa ya koma hannun dangin daulat khatun a hannun wata hamshakiyar basarakiya mai suna dilshad khatun

dilshad khatun ta kasance kamar daulat khatun  wajen mulki sarauta da iya rike yan uwan taka.

 Sunan dilshad din ma lakabi aka mata da sunan wata hamshakiya data rayu a tsakanin shekara 730-750

Duk dama zamanin tarihi yayi nisa amma dilshad sosai ta rike amanan dake tsakanin zuriar daulat khatun da yar uwan ta badiatul jamal, dan haka ita ta raine gen hamood mufaddal a masarautan ta kamar dan cikin ta data haife sa.

Sannan daya girma ya zamto senior naval admiral  a american navy sai ya kawo mace mai suna AARAH a matsayin macen da yake so kuma zai aura.

Sai dai ita dilshad khatun mace ce mai son juya akalar kowa ta yadda take so har ana cewa babu banbancin ta da sarauniya daulat khatun.

Toh da Gen ya zo da maganan auren sai Bata ki masa ba amma a bazata ta hada ta aura masa budurwan nasa Aarah da Babban yarta mai suna KHATUN.

Dan haka A rana daya aka daura auren gen hamood mufaddal da mata biyu

khatoon of the royal kingdom of dilshad daga zuriar daulat khatun.

Da kuma Aarah from a simple political family in Africa.

A masaurarn khorshidy Aka basu inkiyar jahan Aarah,da jahan khatoon.

Gen hamood da shike jinin zuraiat badiatul jamal ne ajikin sa,sai ya zamto mutum mai tsananin biyayya ga uwar rikon sa kuma surkuwan sa dilshad.

Bayan aure Anan persia ya aje mata matayen sa a karkashin
Kulawar masauratar dilshad sai ya tafi aikin sa a america.

Inda aikin sojan na sa ya sa baiya cika zama sosai Hakan ya sa jahan Aarah ta fuskance bakar azaba da fitinan su na tsananin kishi daga wajen jahan khatun da sarauniya dilshad mahaifiyar ta.

Jahan Aarah ta sha wuya sosai,gashi  Allah bai bata ciki akan lokaci ba most time sai dai taga jahan khatun Tayi ciki amma banda ita

To da shike Allah ba azzalumin bawar sa bane cikin ikon sa sai duk wani cikin da jahan khatun keyi da yayi kwari sai ya bare dakansa
Har aka shafe shekara biyar babu wanda ya rayu

Ahakan ma Sun sha daura ma jahan Aarah laifi da zargi da duk wani kazadi akai,amma haka dai ta cigaba da hakuri dasu Har Allah ya zo ya bata cikin khaldun sa’ood babu wanda ya lura.


A lokacin kuma har gen hamood  ya cika 4yrs couse ya rikide daga aikin sa na navy yaje dawo babban army officer still a kasar american.

Ranar daya zo hutu Sosai yayi murnan samun cikin jahan Aarah Murna marar misaltuwa,domin kuwa ta kasance matar so a duniyan sa!

Sabanin dilshad da yarta khatun da abun ya matikar bata musu ransu.

Dama asiri mai karfi sarauniya dilshad din ta saka jahan khatun tayi akan jahan Aarah tun farkon auren su akan bazata ta taba haihuwa ba

Ko da su ka zo suka ji zancen ciki sai abun ya matukar basu mamaki gashi matsafiyar su tace dasu akwai rabo a tsakanin su har da kari.

Jahan aarah kuwa Tana da hakuri sosai ga juriya da yawan biyayya ma mijin ta

ahaka cikin azaban fitinan su har ta raine cikin khaldun saood a masauratr dilshad batare da ta gaya ma mijin ta wani abu mummuna akan su ba.

Tun baya ganewa har ya zo ya fahimta Sosai

Toh bayan jahan Aarah  ta haifi khaldun sa’ood ko shekara biyu mai kyau baiyi ba sai ga cikin subaya ya shigo mata a bazata.

Nan ma jahan khatun ta tada borin kishi da masifa,har sai dilshad ta tursasa gen hamood ya karbe khaldun saood a hannun jahan Aarah akan su ne zasu rike shi kuma sune zasu raine shi

 Shikuwa baiyi musu ba ya dauko yaro ya bar musu shi.

Jahan Aarah tayi kuka sosai dan a duniya idan akwai abunda take so to danta sa’ood ne.

Wannan biyayyar da gen yayi shine abu na farko data kasa nuna hakurin ta akai

Toh sanadiyar nuna wannan fushin jahan Aarah ne ya jawo dilshad ta saka dokan cewa gen ya fitar mata da jahan Aarah a kingdom din ta kuma baza a bata khaldun din ba

Hakan ya jawo sanadiyar dawowar jahan Aarah kasar nigeria cikin garin kano,inda har ta haifi subaya ta raine ta.

‘Toh Tun wannan time din jahan Aarah bata sake komawa lorestan ba sai dai subaya da gen hamood suje,har shekaru suka shude su dilshad girma ya zo  suka saduda suka fara barin khaldun shima yana zuwa ma jahan hutu nigeria sama sama.

 Sun so ace khaldun ya tsani uwar sa ya fifita su amma Ikon ubangiji ya sa duk tsananin biyayyar gen hamood
Da kuma irin rainon da suka daura khaldun din akai bai hana dukan su jin kaunar jahan Aarah kamar yadda ya kama ta ba.
 

Toh A lokacin da gen ya tafi da Jahan Aarah nigeria kari na farko suka ci watanni biyu achan da mamakin sa ya dawo persia ya samu Jahan khatun itama tana dauke da cikin wata daya.

Ba’a wani jima da haifar subaya ba jahan khatun ta haifi yaron ta mai suna KAAMIL HAMOOD


Sai ya zamto  khaldun saood
Da kaninsa kaamil sun taso tare a acikin kingdom din dilshad khatun

Tun khaldun na shekara 12 aka tura sa fannin marine soja,shikuma kaamil na kaiwa 15 shikuma aka kaishi navy a cahn kasar america 

Anan har suka girma gen yayi retire ya samu duk wani matsayin daya ke dashi a yanzu suma yaran sa suka samu ingantaccen rayuwa.


Within the years Rayuwar su gaba daya ta sauya

yanzu dilshad ta dada tsufa sai tayi sanyi ta bar jahan khatun da hidima da ragamar rayuwar su,sun yi munafurcin har sun gaji jahan Aarah bata kula su ba,karshe ma da suka ga ta kyale musu gen da yayan nata gaba daya dan dole suka hakura suka dena shiga damuwar ta
ba kamar da chan ba.

Haka rayuwar su ta kasance

Sarauniya dilshad ta hakimce tana controling duk wani hidiman auren gen hamood da kuma rayuwan yayan sa Sa’ood,kaamil da subaya.

Gashi Acikin sun nan babu wanda bata iko da shi,dan direct zata kafa musu doka kuma ya zauna kenan har abada..

Shiyasa ma tun farko ta sa yarta  jahan khatun ta rike khaldun saood kamar dan cikin tan batare da wani ha inci ba

A yanzu Jahan khatuun tafi nuna soyayyar ta da duk wani daukawar ta akan khaldun saood fiye sa dan cikin ta kaamil kuma Duk wannan yana daga cikin umarnin sarauniya dilshad

Aganin su bakin cikin su shi zai kashe jahan sannan su zasu yi yadda suke so da rayuwar khaldun anan gaba.

Jahan khatun itace babban yar sarauniya dilshad sai wata da ake cewa jahan zainobia.

Jahan zainobia bata da irin muguyen halayen uwarta dilshad khatun bare kuma sistern ta jahan khatun

A africa jahan zainobia tayi aure ta haifi yarta mai suna JUNNUT,
WAnda aka dauko ta shekara guda kenan da  watanni 4 da suka wuce daga chan yankin  jinsin fulanin dake kusa da gulf of eden da bahar maliya.

Junnut itace asalin jini kuma jikar sarauniya dilshad ta karshe a masarautaran khoshirdy dynasty.
#FOLLOW SURAYYAHMS
COMENTS AND
Share share❤❤

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button