NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Dama Malam cewa yai iyayen sa suna son suzo a satin nn suka wo kudin sa zance in ta kama ma hadda sadaki.
Kabbara Baba yai cikin farin ciki yace kice musu suzo gobe ma zan zauna ina nn wannan yaro ai irinsu ba’a sake da su rike su ake gam gam, ice dai kina koya ma ita uwar tawa yadda ake kalamai na soyyaya koh?
Juyar da fuska mamanmu tai kawai kafin tace Malam ko za’a sai zuwa Alhamis tunda bamu tana di komai ba kuma kaga yana da kyau ace in zasu zo an musu dan abin tabawa koh?.
Eh kuma kinyi hankali Hadiza ashe dai har ynxu kina nn da hankalin ki???? toh ki fada masa su zo din ranar alhamis din, nima sai na fadawa malam Suleiman(baban su sumyy) da liman koh?.
Eh yayi Malam Allah ya tabbatar mama da alkhairin sa
Ke kiji ki sai ana zance lumi lumi ki dauko wata maganar kuma ai tunda kika ga an kai ga manya alkhairin knn haba ni bana son bakin ciki kuma
Allah ya baka hakuri malam, Ameen ya fada yana kokarin mikewa.
Wayar ta mika masa tace gashi Malam dazu da yazo ya bama Maryo
Karba baba yai yana jujjuya wayar, shikam badan yasan halin Maryo ba ba abinda zai sasa kin karbe wayar yaje ya siyar, amma ba hali don tsaf yasan halin kayarsa.
Mikama mamanmu wayar yai yace Allah ya sa albarka, Ameen malam sai da safe.
Ko amsa ta bai ba ya fice, bayan fitar sa daga dakin muka fito zama mukai muka ci kazar kadan, mamanmu muka ta nade sauran ta ajiye.
Wayar na dauka na shiga daki, sai da nai adduar bacci kafin na dauke ta na bude case din wayar dana gani red mai kyau nasa ma wayar, kafin na shiga ciki komai
Yasa min sim MTN da numbern sa yayi saving da habybyna, wayar mamanmu na dauka ina copying numbern yan uwana.
Bayan na gama nai masa dogon message ina mika masa godia ta, nuna min alamar sakon yaje ne yasani ajiye wayar a gefena na kwanta.
Asuba ta gari Amaryar Mahmud????♀️
ABUJA
Zaune suke a dinning suna cin abinci wannan dokar Abba ce dole ne tare zasu ci abinci breakfast da dinner.
Abba ne akan kujerar dake tsakiyar dinning din sai Mummy da Ammi a gefen sa, daga gefen Ammy salma ce zaune sai saudat a gafenta.
Gefen Mummy kuwa Munira ce zaune tasha kananun kaya matsatsu attachment din kanta ya zubo har tsakiyar bayanta, cin abincin ta take hankali kwance sabanin su salma da sai juya spoon din suke amma sun kasa ci.
Muryar Abba suka ji cike da gadara ya kalli Ammi yace gobe da asuba jirgin mu zai tashi ni da baby(????) zamu je Korea ina son na huta nagaji da zaman kasar.
Kallona Ammi tai idonta na cikowa da kwalla tace……….
Mrs A.M
????????????????????????
NOOR
????????????????????????
Written by
Mrs A.M
Page 11
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Kallonsa Ammi tai idonta na cikowa da kwalla tace "Allah ya kaiku lafia Alhaji".
Tabe baki Abba yai yace ai ba adduar ki muke bukata ko, itadai Ammi sunkuyar da kai kawai tai tana ci gaba da jujjuya spoon din hannun ta.
Mummy ce ta riko hannun Abba cike da kwarewa gun kissa ta matsa hannun ta dake cikin na Abba, kallon sa tai tana far-far da mitsi mitsin idanun ta tace darling ina ganin ko ni xan hakura da zuwa kaje da maman salma don naga kamar ranta ya baci.
Kyaleta babyna plz ta cika neman masifa ne in ba haka ba ai ke kanwar tace ko zuwa nace zanyi da ita ai ita mai bar miki tafiyar ce.
Wani murmushin mummy tai tana kallon Ammi, buga plate akai da karfi wanda ya sasu kallon mai buga plate, saudat ce a tsaye kusa da Ammi sai huci take.
Wani matsiya cin kallon tai ma Mummy sannan tace Allah ya isa tsakanin mu da ke wallahi shegia munafuka, wata zabura Abba yai ganin haka yasa ta kwasa a guje ta fita daga part din nasu gaba daya ta shiga part din kakarsu.
Salma ma mikewa tai ta bi bayan saudat don ita kanta bata jin zata iya zama duk hakurin ta kuwa.
Kayi hakuri Alhaji zan mata fada Insha Allahu,
Kar ma ki fara bakar munafuka ai da ace ta Allah ce ke da tun tana nn zaki tashi kiyi ball da ita.
Mikewa Ammi tai kawai ta shiga part dinta tana sharar hawaye.
Cike da bacin rai Saudat ta bude part din kakarsu zama tai akan kujera tana dafe kanta don ita wallahi badon Ammi ba ba abinda zai sata ta zauna agidan gwanda ta tafi gidan Auntyn ra kawai.
Fitowa daga kitchen wata tsohuwa tai hannun ta rike da kwanon silva mai dauke da fura lafiyyayya daga gani damun gida ne.
Fara ce tas don har jaja take duk da tsufan ta, bata da jiki sosai amma ba siririya bace kyakyawa ce tubarkallah daga gani zamanin kuruciya ansha layi a kofar gidan su(????)
Ganin saudat a kan kujerar ta tana kada kafa yasa ta kwafa cike da masifa tace toh uwar masifaffu mai kuma kike min a parti na(part) bana ce kar ki kara shigowa ba tunda ke in kika shigo ba’a yin abin arziki da ke.
Kallonta saudat tai tana turo baki tace toh don Allah ke dada wai meyasa kike haka ne da wanne zanji, acan cikin gida in ka shiga Abba da Mummy suyi ta zagin Ammi in munzo nan ma ki hau mu da masifa haba don Allah.
Zama dada tai ta zabga tagumi sai kuma ta fashe da kuka, cikin kuka tace ynxu yar’nan me kuma ya faru wannan mata wannan mata akwai tsinanniya tunda ta shigo gidan nn abubuwa suke ta faruwa abu dai gashi nan saka ka ba dadi, sai kuma ta kara fashe wa da kuka mai karfi kamar wadda aka aikoma da sakon mutuwa.
Salma ma ce ta shigo palourn, ganin dada na kuka yasa ta rugowa da gudu zuwa gunta rike hannun ta tai tace dada me ya faru.
Rike kai dada tai ta fada jikin salma tana kara rushewa da kuka, ganin yadda take kuka yasa saudat sakkowa daga kan kujerar tana fashe wa da dariya
Cike da keta ta ce dada don baki ji abinda ta ke ba, a taikaice dai dada gobe da asuba zasu tafi Korea ita da Abba.
Salati inna ta tafka tace shi madun………
Cike da nutsuwa ya ke daddann wayar sa iPhone 5s tunani yake ya kira ko kar ya kira har sai ya danna zai kira sai kuma yai matsa ya katse ahaka dai har bacci ya dauke sa.
Karfe 5 dai dai ya tashi, mikewa yai bakinsa dauke da adduar tashi daga bacci mikewa yai daga kan katifar sa ya dauki towel dinsa dake rataye ajikin wardrobe dinsa.
Bude kofar yai yana addua ya fito tsakar gidan inda sanyi ke buso shi lumshe idonsa yai cikin jin dadin yanayin.
A hankali ya ke tafiya har ya shiga dan baki, ya dau wajen minti 20 kafin ya fito a gurguje jin an kusa tayar da sallah dakinsa ya koma cikin sauri ya goge jikin sa ya shafa mai sannan ya zira gajeran wando bayan ya feshe sa da turare, jallabiya ya zura kalar ash sannan ya zura silifas dinsa ya fito ya nufi masallacin.
Sai da gari ya fara haske sosai sannan ya fito, cike da nutsuwa ya shiga gidan sa bayan ya sa mukulli ya bude yana shiga dakin sa ya nufa yasa kayan aikin sa sbd yau yana da aiki da yawa shiyasa zai nufi gun aikin da wuri don motocin da yake so ya gyara yau sun kai 6 kuma duk yai ma masu motocin alkawarin zai gyara musu shi kuma yana matukar kiyaye alkawari.
Yana fita ya hau mashin dinsa ya nufi gun aiki..
Washe gari dasu Umma suka ji labarin wayar da kuma zuwan da iyayen Mahmud zasuyi munga tashin hankali don Umma hauka ne kawai bata yi ba.
Bama lokacin da walida ta fada mata kudin wayar, ita kam walida tunda taga wayar take ma uwar kuka a daki hankalin umma in yayi dubu ya tashi gashi tai kissar don ta hana baba kin yarda da zuwan iyayen mahmud amma abun ya faskara don baba fa yaga gun cin kaza????
Mu kuwa ko a jikin mu don da safen ma lokacin muka bude sabon sha’anin mu, ragowar kazar mu ta jiya muka gyara sai kanshi take tuni kanshin ta ya budade gidan wanda hakan ya kara bata wa umma rai don har lekowa palourn mu tai tana zagin mu wai kwadayayyu wadanda basu san ciwon kansu, itadai mamanmu ko kallon ta batai ba sai nice na gwalla mata harara ina dago mata wayar tawa.