NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Maryo nice mahaifiyar ki ni na haife ki duk abinda yake damunki ki fada min in bani ba wa zaki fadawa maryo.”
Hawayene kawai naji suna zubo min sai na fada jikin mamanmu na fashe mata da kuka, bata rarrasheni ba kuma bata hanani ba sai da nayi mai isa ta sannan ta dago ni ta goge min hawayena tace “ina jinki mene damuwar ki”
Cike da shassheka nace “mamanmu Mahmud ne gaba daya ya chanja min tunda ya dawo daga tafiyar da yai ya rage kulani ko na kirasa sai ya nemo dalilin da zai sa muyi sallama kuma mamanmu tun shekaran jiya bai kira ni ba na kira sa amma yaki dagawa na masa message yaki reply mamanmu kawai na kara fashe wa da kuka.”
Kiyi hakuri maryo ni kaina na fuskanci canji wajen sa sosai amma kiyi hakuri komai mai wucewa ne kiyi ta addua duk da nasan bakya wasa da ibada amma mu dage da sallar dare muna kaima Allah kukan mu insha Allah komai zai daidaita.
Sai da mamanmu ta min nasiha sosai masu ratsa jiki sannnan ta fita.
Cikin wannan hali aka kawo lefen Walida akwati 8 zo kuga hauka gun walida da Umma, ranar munsha gori ni da Mamanmu su Gwaggwo Amina kuwa ranar sai da na fada mata bakar magana sbd zagin mamanmu da tai.
Haka aka gama suka tafi, tuni gidan mu ya fara cika da yan biki.
Inna Maryam ma tazo ta sauka a dakin mu don basa shiri da Umma ko kadan.
Hajjo ma tazo itama duk sun tare a dakin mu hakan yasa ni komawa gidan su Sumy nida Muhd don dakin mu ya cika da yan uwan mamanmu dana baba.
Har ana sauran kwana biyu biki Mahmud baya daukar waya ta kuma baizo gidan mu ba, a yanxu kuwa su hajjo sun san da matsala tsakanin mu sbd ba kayan lefe kuma bai zo ya nuna gidan da zan zauna ba.
Umma sai sakin gori take wai haka za’a kaini gidan mijin ba gida ba lefe, mudai bata gabanmu ni burina kawai Mahmud ya kirani sbd ynxu kona kira sa ma wayar a kashe take gashi ban san da numbern yan gidansu.
Ranar Alhamis aka samu a lalle nida walida a tsakar gidan mu, bayan an gama na koma gidan su Sumy aka zanan lalle na za da baki yayi kyau har ya gaji da kyau. Kaina anmin kananan kitso don duk yadda bana son kitso ranar haka Aunty ta tsaya a kaina aka min.
Washe gari ya kama juma’a ana gobe daurin aure aka yi yini.
Nasha less dina mai kyau kalar ja da fari ya haska ni sosai, sumy tai min light makeup na bata waya ta tai min hotuna sosai.
Duk da yadda gabana yake faduwa amma haka nai ta sakin jiki a cikin yan uwa na ina murmushi sai bayan magriba aka gama yinin wanda dama ba wani dj ake ba yini ne dai irin namu na talaka wa.
Wajajen karfe goma babansu sumy ya kira babanmu a waya.
Yana dagawa yace lafia kuwa kira da daddaren nn yahuza.
Ka fito kawai Abubakar kanin baban Mahmud ne yazoo……..
Mrs A.M????
????????????????????????
NOOR
????????????????????????
Written by
Mrs A.M
Page 15
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gaban sane ya fadi cike da damuwa ya mike ya zira takalminsa ya fita.
A kofar gida ya same su suna tsaye kallo daya yai ma baban su sumy ya ji gaban sa ya fadi sbd kana ganin sa kasan yana cikin tashin hankalin sosai.
Karasa wa yai gunsu yana mika ma kawun Mahmud hannu, musabaha sukai sannan kawun Mahmud ya ce “kuyi hakuri don girman Allah akan abinda zan fada muku wallahi mu kanmu kunya ta hana mu tunkarar ku sai danaga in muka tsaya bata lokaci ba tare da mun fada muku ba zakuji kunya muma kuma zamu zama kananun mutane.”
Tunda ya fara magana baba da baban su sumy suka tsaya suna kallon sa cike da fargaba da tashin hankali don daga gani duk abinda yazo ya fada musu ba alkhairi bane.
Cigaba yai da magana cike da damuwa yace “Mahmud tun watan da ya wuce muka kasa gane masa gaba daya, kullum bashi da aiki sai zuwa gun manyan sa yana kuka yana cewa baya son auren nn tun muna daukan abin wasa sai gashi har da kwanciya a asibiti yai, da muka ki amince wa ma cewa yai zai gudu y bar gidan baxai sake waiwayen muba. “
“Don Allah kuyi hakuri wallahi ynxu maganar da nake muku waccen satin aka daura masa aure da yar uwar sa, kuma tunda akai auren aka kai masa amaryar sa bai sake zuwa gidan su ba.”
“Gajiya mukai da abinda ke faruwa kawai muka ga gwanda azo a sanar muku abinda ke faruwa kuyi hakuri don Allah in Allah ya kawo mata wani mijin kawai tayi auren ta insha Allah baza ta wulakanta ba.”
Wani gumi ne ya yankowa baba, zai iya cewa tunda yake ba abinda ya taba sashi cikin tashin hankali irin wannan al’amarin ba.
Cike da tashin hankali baban su sumy yace “ynxu ba yadda za’ai a daura musu auren ba komai mu ko a ta biyun ce zata shiga tunda yarinyar nn tana son yaron nn kuma shima alamomi sun nuna yana kaunar ta.”
Cikin damuwa kawun Mahmhd yace “wallahi har hakan munyi tunani malam amma yaron nn yace ko an aura masa yarinyar nn sai ya sake ta a take a gun da aka aura masa ita shiyasa muka ga da azo ana dana sani tun wuri gwanda muzo mu fada muku.”
Baban sumy ya bude baki zai kara magana kenn baba ya riko masa hannu cikin fushi da bacin rai ya kalli kawun Mahmud yace “mun gode ita kuma yarinyar kamar yadda nai niyya Insha Allahu gobe da auren wani zata kwana.”
Jan hannun baban su sumy kawu yai har kofar gidan sa sannan ya dafa sa yace “Malam Yahuza kar kai maganar nn da mai dakin ka don Allah kasan halin mata kawai ka kyaleta,” yana gama fadin haka ya juya ya shige gida.
Yana shiga dakin sa yaga Umma a tsaye tana daure da daurin kirji.
Ganin yana yinsa yasa ta kallon sa da kwallin da bokan ta ya bata.
Dafa sa tai tace “malam lafia kuwa naga ka fita a wannan lokacin kuma ka dawo cike da tashin hankali me ke faruwa ne?”
“HMMM wato harira kamar ni wannan yaron mahmud zai wulakanta don wulakanci wai ya fasa auren Uwata kiji wulakanci fah.”
Umma jitai kamar ta taka rawa a gurin amma sai ta kanne tace “garin ya shi ba shine yace yana sonta ba naga yaron nn ko ni daba shiri muke itan hadizan ba nasan ya na son maryo amma mai yasa zai wulakanta mu haka ana gobe daurin aure.”
Cike da takaici yace “ba wannan bama wai yaron nn sbd iskanci da iyayen suka ki amince wa da fasa auren har kwanciya yai a asibiti kuma yace musu zai gudu ya bar gidan, ynxu maganar da nake miki satin da ya wuce aka daura masa aure da yar uwarsa nikuma wallahi yadda nai niyya dole gobe insha Allah na daura mata aure da wani sai dai bansan ko waye zai aure ta ba.”
Dafa sa umma ta karayi tace “malam kawai kaja bakin ka kai shiru kar ka fadawa kowa in yaso goben a masallacin ka yi shellar ga yar ka nn zaka bada sadaka.”
Da sauri ya juyo yana kallon umma sai dai kallon ta da yai yaji kawai ya amince.
Cikin murna ya riko hannun ta yace “kin kawo shawara harira amma kina ganin zasu yadda hadizan ga kuma inna itama.”
Cikin kissa umma ta tsara sa da yadda komai zai faru hakan yasa ya rungume ta yana mata godia ace warsa ta fitar da shi kunya.
Fita umma tai ta wuce dakinta nan fa ta bude sabon shagali amma taki yadda ta fadawa kowa sbd in har wani yaji dole kafin daurin auren zancen ya fasu, abinda ita kuma baza ta bari ya faru ba don in had zancen ya fasu inna sai tayi yadda tai fasa aka fasa auren.
Washe gari
Tunda gari ya waye nake jin wani irin faduwae gaba dana rasa daga ina take zuwa, jina nake kamar wata mara lafia.
Da kyar na mike nayi alwala nayi sallah.
Sumy na gefena itama duk jikinta yayi sanyi sbd rabuwar da zamu yi yau.
Karfe goma dai-dai yan daurin aure suka nufi masallacin juma’a dake gwammaja.