NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Gyada kai rabia tai tace “Eh Aunty amma in na mata wani style dinma baxa a ga wancan ba.”
Murmushi Aunty tai tace “yauwa yar gari maza yi mata kuma ki tabbatar yafi wanda kika mata wancan satin kyau.”
” Insha Allah Aunty wannan sai ya fi wancan kyau” inji rabia data fito da kwakkoran ta.
Tana cikin min na kafa sumy ta fito daga daki, zama tai gefena tace “masoyiya ynxu gobe iwar haka muna nn muna shirin kaiki gidan ki koh?”
Ko juyawa na kalle ta banba kawai na maida hankali na kan kunshin da aka zana min a hannu duk da bana cikin mood mekyau amma hakan bai hanani ganin kyaun da yai min ba.
Tana gamamin Aunty ta bata kudin ta tana mata godia.
Mikewa tai tana hamma cike da gajiya duk jikinta ciwo yake mata kamar wacce aka ma mugun duka.
A hankali ta ziro kafar ta kasa mikewa tai ta tsaya akan kafar ta cike da mamaki take bin jikinta da kallo ganin kayan da ke jikinta ba wanda ta sani bane.
Ita dai iya sanin ta da atampa ta kwanta amma sai ta ganta tsirara ba komai tana cikin tunanin nn taji an bude kofa.
Shigowa Alh mukhtar yai hannun sa dauke da tray da ya dauro cup cike da tea sai kuma plate da aka soya chips nd egg.
Da sauri ta janyo bargo ta rufe jikinta ganin ya shigo , shi kuwa ganin abinda tai yasa sa sakin wani makirin murmushi.
Ajiye tray din yai ya zauna a gefen gadon, hannu yasa ya shafo fuskar ta yace “good morning baby.”
Sunkuyar da kai tai gaban ta na faduwa ganin yadda ya rambada kwalli a idon sa.
Ganin taki magana yasa sa sakin wani murmushin ya mika mata tea din bakinta.
Bude wa yai ya bata sosai sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya kyaleta.
Hannun ta ya rike yace “babyna kira umma kiyi mata sallama ynxu zamu tafi ba lokaci ne amma naso na muje har gida muyi musu sallama.”
Kallon sa tai tace “ina zamuje?.”
“Dubai dama nace miki zan baki wedding gift koh to wannan ne nan da 1 hour jirgin mu zai tashi yi sauri ki kinsa zan jira ki a kasa” daga haka ya mike ya fita.
Bin kofar da ya rufe tai da kallo cike da murna ta mike ta fada wanka cikin kankanin lokaci ta shirya cikin wata jar doguwar riga data ga ya ajiye mata.
Sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta dauko wayar ta ta kira umma.
A gaggauce sukai sallama inda umma ta kasa zaune ta kasa tsaye yar ta zata tafi dubai.
Kasa ta sauka suka hau mota suka, suna daukar hanya ya hura mata iska a hanci data sata zubewa kan kujerar…..
Kallon sa khalifa yai yana fashe wa da dariya yace “amma maza dan iska ne kai wallahi haba ango ya zaka ce haka?..”
Kara hade rai yai yace “bana son iskanci fah toh karya nai uban me zan mata nifa na abinda ya hada ni da ita kawai daj albarkacin ummi zata ci da tace ma kula da ita kuma na rike amana amma ai an cuce ni kawai. “
Tsaki khalifa yai yace “lokacin daza kasa yar mutane a daki ka rufe kofa sani nai kai ne fah maza kana kallon mace kuma halaliyar ka ka kasa tabawa anyaaaa……”
Wani matsiya cin kallo yai ma Khalifa da yasa sa rufe bakinsa yana daga hannayen sa sama.
Kwafa yai yace “better sai kace wani dan iska don an ajiye ni gida daya da mace toh in ganta inji me banxa kawai ni ba macen zata sa naji ina sha’awar ta don banga abin sha’awar ba.”
Shidai khalifa bai sake magana ba sai kallon sa yake.
Ganin kallon da khalifa yake masa yasa shi mike wa cikin nutsuwar sa ya shige dakin sa..
Da sauri ya mike shima ya bisa don yasan kadan daga aikin sa ya kulle kofar sa ya hana shi shiga ….
Washe gari ta kama ranar asabar ranar da za’a dangana ni da gidana , tun da safe gaba na yake faduwa dauriya kawai nake ina yake.
Gurin azahar ni da sumy muka shiga gidan mu, tunda aka dauran aure ban sake fitowa ba sai yau.
Muna shiga umma tana fitowa daga dakin ta kallona tai tana min wani murmushi wanda ya tsaya min arai ganin abin in na kyale baxai wuce ba yasa na saki hannun sumy dake cikin nawa na matso daf da ita.
Kallon kallo muka tsaya yi ni da ita mun kai wajen minti uku ina kallon cikin kwayar idonta abinda ban taba ba knn.
Wani murmushi daya daki zuciyar ta da karfi har sai da ta dafe kirji nai mata sannan na dafa kafadar ta na rage murya sosai nace “ALLAH YANA NAN”
Wuce wa nai na shige dakin mu sumy ta biyo ni tana mamakin mai na cema Umma.
A zaune muka samu mamanmu ita da su hajjo suna cin dambu.
Zama mukai muna gaishe su cikin girmamawa.
Kallona mamanmu tai tace kin gama fushin ne kika shigo yau.
Nidai ko uhm ban ce mata ba na shiga dakin mu, kwanciya nai akan gado ina cire dan kwalin kaina sbd zafin da kitson da aka min yake.
Ina kwance aka kira sallar la’asar mikewa nai naje nayi alwala nazo nai Sallah na kara kwantawa har aka kira magriba ina kwance.
Ina sallah Gwaggwo hafsa tazo ta dagani ta shigar dani ban daki, ruwan da ta hada min na wanka wanda yasha turare tace nai wanka da shi kuma nai sauri.
Tunda na fito daga wankan nake ajiyar zuciya, shiryawa nai cikin atampa mai pattern grean nd white dinkin riga da zani dinkin ya min kyau sosai.
Zama nai gefen katifa ta ina kallon samy dake kuka a hankali ta zabga tagumi gefena kuma muhd ne shima kukan yake har da shassheka.
Ana sallar isha na tashi nai sallata amma sai na kasa tashi daga kan daddumar har sai da Aunty ta shigo ta mikar da ni.
Zaunar da ni tai ta shafa min powder da lip balm sannan ta janyo lifaya ja da fari ta nada min shi ta rufe min fuska, feshe ni tai da turare ta ajiye min farin flat shoe nasa ta rungumo ni muka fito palour.
Muna fitowa palourn ya kaceme da guda da addua.
Zaunar da ni tai a gaban mamanmu tace “to mamanmu sa ma ta albarka zamu mika ta dakin ta ynxu insha Allah.”
Shiru mamanmu tai sannan a hankali ta riko hannuna kawai ta fashe da kuka wanda yasani nima fashe wa da kuka na fada jikinta, rungume ni tai tana kuka ina kuka hakan yasa wadanda suke palourn masu raunin zuciya suma kuka.
Ganin muna bata lokaci ga kuma motar daukar amarya sunzo yasa Inna mikewa ta ce “hadiza ya za ki tsaya kuka kuma keda zaki ma yarinya nasiha sai ki sata a gaba kina kuka”
Ahankali mamanmu tace “ALLAH YAI MIKI ALBARKA MARYAM YA DAFA MIKI YA BAKI ZAMAN LAFIA DA KWANCIYAR HANKALI A GIDAN AUREN KI KIYI HAKURI INSHA ALLAH WATARAN SAI KINYI DARIYA”
Kara fashe wai da kuka ina rike mata hannu sosai da kyar Aunty ta jawoni ta rungume muka fito dama baba baya nn yace kawai in anzo a kaini.
Ita kuwa umma ba’a san dalilin da ya hanata zuwa ba tace baxata ba.
Zaunar dani Aunty tai a mota ta matsa Inna da hajjo suka shiga sai kuma Gwaggwo Zainab ta shiga gaba.
Motoci uku ne suka zo amma sai da suka cika daf har ma suka yi kadan don a haka wasu adaidaita suka hau dukda ba’a gayyace suba.
Tafiyar minti tamarin ta kawo mu kofar gidan, yana parking inna suka fito, hannuna ta rike tace fito da kafar dama kiyi bismillah haka nai suka sani a tsakiya itada hajjo har muka shiga gidan addua kawai nake ina fadin duk abinda inna tace na fada.
Cikin dakin direct inna ta wuce ni dani, zaunar da ni tai akan katifa ta da aka lailaye da bedsheet mai kyau ga bargo nan shima an ajije a gefe.
Zama sukai akai addua sai kara duba gidan suke sbd da wuta gashi ko ina haske.
Alhamdulillah kowa yake fadi sbd gida yayi kyau kuma su mamanmu sunyi matukar kokari suma.
Sai wajen 10 sannan suka fito gaba dayan su sbd khalifa da yake jiransu zasu maidasu gida.