NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Saura kadan dariya ta kubcewa Noor amma ya danne ta yana kare mata kallo, a ransa yace amma gaskia khalifa ka cuceni da kai tunanin zan iya kiran yarinyar nn shimfida ta wannan ai haihuwar kaji na haife ta na????
Wuce wa yai kawai ya raba ta gefen ta ya sa mukulli ya bude dakinsa ya shige ya rife, ya rufewq murmushi ya subuce masa yana shafa gashin bakin sa wai bature…….
Ni kam mutuwar tsaye nai ina binsa da kallo wai ynxu wannan baturen knn baba ya aura min in banda abinsa lallai ina zan kai wannan gansamemen, don duk tsayi na kaina a tsakiyar kirjin sa ya tsaya tabbb.
Dan dukan kaina nai tunowa danai meye hadina dashi ma.
Daki na shiga nai sallah na dade zaune ina azkar sai da naga rana ta fara fitowa sannan na mike na shiga gyara dakin.
Ina cikin gyarawa naji fitarsa daga gidan hakan yasa ni saurin fitowa na dau tsintsiya da moper na shiga gyaran gidan.
Sai da na gyara ko ina banda dakinsa na wanke ban daki na gyara kitchen sosai na jera komai yadda nake so sannan na fito.
Fellen zanin wanka na dauka da hijab na fito na shiga bandaki a raina ina mitar rashin toilet a dakina(su maryo masu daki????)
Ina fitowa na shigo dakina na zauna na shafa mai shiryawa nai cikin riga da zani na atampa kalar peach na shafa powder da kwalli.
Hijab na dauko da wayata na fito palour zama nai ina kallon ko ina don palourn ya min kyau sosai.
Jinai ana buga kofa hakan yasa na mike na zura hijab dina na fita, silifas dina nasa na nufi kofar.
Shiru nai ban magana ba, kara buga gidan akai hakan yasa ni fadin “waye.”
Muryar tsohuwa naji tana cewa “nice nn Indo tare muke da jikata Bintu amarya makotan kune ko shi mai babban sunan bai fada miki kina da makociya indo bane.”
Nidai ba wani gane zancen ta nake ba kawai na bude mata kofa ina matsawa don bata hanya ta shigo.
Tsohuwa ce zatai sa’a da inna ko ta girmi inna ma bayan ta kuma budurwa ce wacce zata girme min da shekara biyu mai dan jiki don ta fini kauri.
Shigowa sukai ni kuma nai musu jagora zuwa palourn.
Zama tai kan kujerar dake kallon kofa ta na shafa ta tace “Masha Allah gida yayi kyau kuwa sosai sai dai fatan Allah ya bada zaman lafia ya kawo zuriya dayyiba.
Nidai ban magana ba sai tsugunnawa danai a gabanta nace “Ina kwana baba.”
“Lafiya qalau yar nn taso ki zauna mana.”
Mikewa nai na zauna a gefen ta sannan na kalli budurwar da aka kira da bintu nace “sannun ki.”
Ciki ciki ta amsa da “lafia” nidai ko kara kallonta ban ba don naga sai wani ciccin magani take.
Juyawa nai gun tsohuwar data fara gabatar mun da kanta tace “sannu yarnan ni sunana Aisha indo amma kowa inna yake cemin, jikokina ne biyu tare muke zama da su da Salimu sai Bintu marayu ne iyayen duk sun rasu shine nake rike su.”
A hankali nace “Allah ya jikansu ya gafar musu”
“Ameen” inna tace sannan ta cigaba da fadin “tsawon shekara 3 muke tare da mai babban suna ai nice komai nasa kin ganni nn kamar kaka ya dauke ni nima kamar kaka na dauke sa fatan kema zaki dauke ni haka koh.”
Sunkuyar da kai nai ina murmushi nace “Insha Allah inna”
Kallona tai tace “ya sunan ki ne yar nn.”
“Maryam” na bata amsa ina mikewa don kawo musu ruwa.
Bina tai da kallo ganin na fita sannan ta juya gun bintu tace “kinganta kamar ba yar kasar nan ba kinga idanun ta kuwa saidai yarinya ce daka gani.:
Tsaki bintu tai tace “ke wai toh inna ina ruwan ki”
Kauda kai inna tai kawai tana kallon tv da ba’a kunna ba.
Ni kuwa kitchen na nufa ina shiga na dauko tray na bude fridge sbd dazu dana zo gyara naga lemo da pure water leda biyu a ciki, dauko pure water nai guda uku nasa akan tray din na dauko lemon fru fru guda biyu na dora shima sannan na dauko cups na cikin jug dina na dora akai.
Da sallama na shigo dakin, ajiye tray din nai a kasa nace “gashi inna.”
Mika mata pure water nai ta karba ta shanye sannan ta kara miko mata lemon na bude mata shima tunda ta kafa kai saida ta shanye.
Hira tai ta min tun bana sakin jiki da ita har na fara mayar mata don inna badai abin dariya ba.
Can tace “bara mu tafi dai maryama kafin mai gidan naki ya dawo zan aiko bintu ta kawo miki abinci kinji koh.”
“Toh inna na gode sosai Allah ya kara lafia da nisan kwana mai albarka”
:Ameen yar nn diyar albarka.”
Muna fitowa tsakar gidan aka bude kofar gidan aka shigo, shigowa yai yana sanye da kananan kaya wadanda suka amshe shi sosai bayansa almajirai ne wajen su uku suka shiga shigo da kayan abinci.
Tsaya wa yai ganin inna yace “ina wuni inna kun dawo lafia.”
Washe baki inna tai tace “lafia qalau mai babban suna ai jiya muka shigo da daddare shiyasa baka ganmu ba ynxu nace amma bara na shigo mu gaisa da amaryar ashe baka nn ma.”
Dan satar kallon ta yai yaga sai dibi dibi take a cikin hijab, juyar da kansa yai ya na amsa gaisuwar Bintu da take masa cike da iyayi.
Kallon ta nai naga sai washe baki take tana wani gyara mayafin ta, tabe baki nai don sai ynxu na gane abinda take nufi wato son baturen take knn.
Inna ce ta kalle sa tace “fatan dai ka gasa ta sosai koh mai babban suna don daga ganin alamunta bata da kwarin jiki sosai.”
Da sauri na zaro idanuna waje na sa hannu na rufe bakina ina kallon ta.
Noor ma dan kara ware idanun sa yai yana kallon inna jin babban maganar data ke.
Ganin duk mu biyun bamu yi magana ba yasa inna dafa ni tace “ko kina jin ciwo ne haka sai na aiki binta taje ta siyo miki maganin rage radadi kinsan halin mazan zamanin basu cika hakuri ba wallahi.”
Sunkuyar da kaina nai kawai ina jin kunyar duniya ta hadu ta tarar min ji nake kamar na shige kasa, ganin bani da zabi yasa na juya cikin tafiya ta a hankalin na nufi palour na.
Cikin tausayawa inna ta kalli Noor tace “don Allah mai babban suna ka sassauta mata kaji kadan daga mata kafa kayi hakuri la daure ka cije nasan da wuya amma ka daure dai daga gani taji jiki duk ta chanja wallahi(kin taba ganin tane????)”
Shidai bai magana ba sai kallon ta da yakeyi kawai yana godewa Allah da khalifa baya nan da yasan ba karamin tsokanar sa zai dinga yi ba.
Kofar gidan inna ta nufa tana “fadin kar kuyi girki yau gaba daya zan aiko muku dashi, yo taya ma zan bari tayi girki bayan ka gama yiwa yarinya raga raga kamar wani mara imani.”
Shidai bai ce komai ba sai kallonta da yake yi yana mamakin halinta ko wa yace mata wani abun ya shiga tsakanin su oho.
Yaron da suka shigo masa da kayan abincin ya ba su kudi sannan ya tsayar da karamin cikin su yace yana zuwa.
Palourn ya nufa yana shiga ya ganta zaune tana dan na waya.
Dagowar da zanyi mukai ido hudu dashi hakan yasani mike wa da sauri ina gyara hijabi na…………
Mrs A.M????
????????????????????????
NOOR
????????????????????????
Written by
Mrs A.M
Page 21
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Dauke idanun sa yai daga kaina ya na dan kare ma palourn kallo, tabe baki yai ya kalle ni cikin nutsuwa yace "biyoni."
Yana fadin haka ya juya ya fita, binsa nai da kallo ina juya maganar sa wai biyoni to nabisa muje ina.
Ganin zan bata lokaci yasa gyara hijab dina na fito daga dakin.
A kitchen na gansa tsaye yana gyara kayan abinci ya aka shigo dasu, kofar kitchen din na tsaya ina sunkuyar da kaina.
Juyo wa yai yadan saci kallona sannan cike da nutsuwa yace “ga kayan abinci nn duk abinda babu ko kuma zaki bukata ki rubuta in nadawo anjima ki ban.”
Gyada kai nai inajin yadda gabana yake faduwa da karfi, kare hade rai yai yace “ba da bakine?”
Da dan sauri nace “toh zan duba insha Allah.”
Dan tabe karamin bakinsa yai yace “ga yaro can a waje shine yake min sharan tsakar gida da kuma aike,” daga haka ya juya ya fita daga gidan.