NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri maman mu ta mike don jin muryar babanmu, fitowa nai da sauri na bude masa don nasan in har mamanmu ta bude masa to fa duk fadan dayai niyyar mun sai ya ninka sa kuma akan mamanmu zaiyi sa

More comments more typing

Comments nd share plz

Mrs A.M

????????????????????????
NOOR
????????????????????????

   Written by
       Mrs A.M 

Page 4

Dedicated to my one and only sis MRS OMAR????????

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ina bude kofar baba ya fado falon kamar ya kife bayansa kuma Umma ce tsaye ta rike kwankwaso daga ita sai daurin kirji, wannan dama ba sabon abu bane don ta mafi yawo da daurin kirji a gida akan sa kaya kannan nata kitson duk ya tsufa ya tuttuje jajir dashi kamar wacce take birgima akasa.

Kallona yake kamar zai shake ni yace don ubanki ban hanaki yima umma rashin kunya ba, ba babar ki bace ba don uwarki.

Da sauri na dago ina kallon sa tuni idona sun kada kunyi jajir, a duniya in da abinda na tsana tofa shine a zagar min mahaifiya

Don uwarki dukana zakiyi kika tsare ni da ido mara kunyar banza kawai, don kinga kaf cikin ku nafi dan sarara miki shine nima kike so ki fara raina ni

Sauke idona kasa nai kawai zuciya ta tana tafarfasa sbd hango fuskar umma danai tana zabga min murmushi.

Don girman Allah malam kayi hakuri wallahi baxa ta sake ba nima nayi mata fada wallahi inji mamanmu

Zaki rufe min baki ko kuwa sai na banke miki shi munafuka ai duk ke kike sasu a daki kina kitsa musu shiyasa dukkan su basu ganin girmana algunguma nidai wallahi bansan ma wani hau ne yahau kaina ba na yadda ba auro ki.

Da sauri na rintse idona jin abindq baba yake cewa mamanmu, kwalla ce ta tarar mun a ido nayi saurin komar da ita sbd abune mai wuya ke sani barin saukar kwalla a fuskata.

Mamanmu ma da sauri ta dauke kanta tana goge hawayen da ke zubo mata wadanda suka ki tsaya wa duk iya kokarinta na ganin ta tsai dasu.

Umma kam shewa ta saki kamar ba dare ba wanda yasa Muhammad da dama tunda baba ya fara buga kofa ya tashi amma ba wanda yasan ya tashi yana jin duk abinda baba yake cewa sai kuka yake ya kara tsorata ya fito da sauri ya makale a kofar dakin yana kallon su baba.

Cikin tsawa mamanmu tace min baxa ki basa hakuri ba uwarmu kin tsaya a kanmu kina kallon kowa.

Da sauri baba yace dakata hadiza basai kin zagar mun uwa ba tunda kinsan sunan uwar tawa taci
Kallo na yai yace in nakuma jin kin bata ma umma rai wallahi kinji na rantse sai na zane ki tsaf wallahi don uwarki kiji na fada miki ba tsoron ki nake ji ba in kinga bana miki fada sosai kina jin dadi to wallahi ynxu ubanki zaki dinga ci

A hankali na motsa bakina nace kayi hakuri baba

Kallona yai yace ita umman baxa ki bata hakuri ba ko kuwa.

Kallon umma nai dake ta yatsine yatsine ynxu nace mata kiyi hakuri.

Tsaki tai ta juya ta fita kawai, kallon mu baba yai yace wallahi dukkan ku ku kiyaye ni shima ya juya da sauri yabi bayan gimbiyar tasa????

Kallona mamanmu tai tana kokarin shanye hawayenta tace kinji dadi koh Maryo kinga abinda Malan yai mana hankalin ki ya kwanta ynxu????

Da sauri na matso gunta na durkusa nace mama don Allah kiyi hakuri wallahi mamanmu kin san baxan taba abinda zai sa ranki ya baci ba

Amma ban hanaki yima umma rashin kunya ba ynxu gashi kinga abinda ya faru…, kukan muhd ne ya katse mata abinda take shirin fada.

A tare muka juya muna kallon kofar dakin mu, a tsugunne yake yana kuka har da shassheka.

Nice nayi karfin mikewa da sauri na je gunsa na dago sa, ai kuwa ya fada jikina yana kara fashe wa da wani kukan.

Mikewa mamanmu tai itama tazo ta hada mu ta rungume mu duka tana shafa kan muhd
Dagowa yai ya kalli mamanmu yana rike mata hannu yace meyasa baba baya son mu kamar yadda yake son su Zainab.

Da sauri mamanmu ta rufe masa baki tace kul ban hanaka fadin cewa babanku baya son ku ba yana sonku sosai ya’yana ku cigaba da masa addua insha Allah wataran sai labari.

Ahaka ta samu duk muka dan saki ranmu amma duk da haka nidai zuciya ta har turiri take don takaici.

Mikewa nai bisa umarnin mama da tace mu je muyi alwala muyi sallah sbd lokacin har daya saura.

Alwala nai a bandakin mu dake falo, ina fitowa muhd ya shiga shima sbd mamanmu a tsaye take akan mu gun ibada shiyasa har shi shima yana sallah da daddare bisa koyarwar mamanmu.

Haka muka raya wannan dare cikin kai kukan mu gun mahalliccin mu sai gurin 3 na tashi daga kan sallaya na je na kwanta gefen mamanmu wacce ta rigani idar da tata shi dama muhd raka’a biyu yai ya kwanta.

A hankali na kwanta ina tunanin rayuwarmu duk yadda nake son yakice hakan a araina sbd muna da makaranta gobe da safe amma abin ya gagara….

ASALIN LABARIN✍️

Malam Yakubu da Inna Maryam yan asalin kauyen karaye ne dake garin kano sune suka haifi babanmu, auran saurayi da budurwa akai musu kuma yan uwan junane

Bayam auran su da shekara biyu Allah ya azurta maryam da samun ciki sunyi murna sosai inda suka dinga rainon cikin har Allah ya sauke ta lafia aka samu diya mace.
Ranar suna yarinya taci sunan babar maryam Zainab ake cemata Abu sbd alkunya.

Shekarar Abu biyu ciki ya kara bayyana a jikin Maryam, wannan cikin ma sunyi dauki kamar shine na farko
Shima Alhamdulillah ta sauka lafia inda aka samu Namiji, ranar suna aka rangadawa yaro suna Abubakar, Maryam tayi murna sosai sbd karar da mijinta yai mata yasa sunan babanta(baban maryam ya rasu kafin aurensu sakamakon sarar sa da miciji yai a gona, abinda yasa tace yai mata kara da bai sa sunan baban sa ba sbd shima babansa ya rasu tun yana yaro )

A haka suka cigaba da rainon yaransu cikin farin ciki lokacin da Abubakar yai shekara biyar lokacin Zainab ma tana da shekara bakwai.

A wannan lokacin Maryam ta kuma samun ciki.
Murna gun su Abubakar da Zainab ba’a magana don suna son yara sosai.

Haka Maryam ta haihu lafia aka samu mace akasa mata Amina.

Haka wannan family suke rayuwa cikin farin ciki da kaunar junansu
Iyayen su sunyi kokari matuka gun basu ilimi na islamiyya da boko daidai gwargwado.

Zainab nada shekara sha hudu akai mata aure da mijinta mai suna Hamza, (yana da rufin asiri daidai kwarkwado suna zaune a garin kano ynxu haka suna da ya’ya biyar uku maza biyu mata duk manya ne don sun girma.
Anma matan aure mazan ma biyu sunyi aure sai daya ne ya rage wanda shima an kai kudinsa)

Bayan auren zainab da ta koma kano iyayen ta da yan uwanta sunyi kewar ta matuka sbd Zainab ta kasance mai sanyin hali da nutsuwa sabanin yar uwarta Amina da ta kasance mai fitina tun tana yarinya.

A haka suka cigaba da zama inda ita ma Amina ta cika shekara goma sha biyar aka mata aure itama, tana zaune a kano ynxu itama tana auren mijinta wanda yake da arziki daidai gwargwado(ya’yanta uku ita kuma duk mata ne Khadija itace babba tayi aure sai mai bi mata fiddausi itama tayi aure sai kuma hafsa itace sa’ar walida ).

A lokacin da akaima Amina aure shekarar Abubakar is ishirin bayan auren Amina da shekara biyu Allah yai wa malam Yakubu rasuwa.

Iyalansa sunji mutuwar sa dama jama’ar garin kasance war sa mutum na gari mai daraja da kirki.

Inna(Maryam) taji mutuwar mijinta don har jinya tai ta tsawon wata daya kafin ta dan fara nutsuwa.

A hankali abubuwa suke tafiya inda Abubakar yake aikin noma a gonar su kuma suna samu har ya dan fara shiga garin kano yana kai kayan gonar sa ana siya
A irin haka ya hadu da umma wacce ake kiran ta Harira, ya hadu da harira a kasuwa tana saida abinci, tashin farko ya yaba da ita, kuma baiyi kasa a gwiwa ba ya bayyana mata sirrin zuciyar sa itama anan tayi na’am da shi kasancewar Abubakar badai kyauba tunda fulani ne????(yan uwan su Mufee????)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Leave a Reply

Back to top button