NOOR COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallon sumy yai yace sunana Mahmud fatan zaki taya ni kafa gwamnatina a zuciyar Gimbiya.
Kallon kasan ido nai masa na yan sakanni, baki ne ba can ba don na fisa haske dogo yana da jiki dan daidai gashi tubarkallah daga ganin sumar kansa bafilatanine.
Juya wa nai ina daukar ledojina na gyara jakata na kalli Sumy nace in kin gama ni na shiga gida.
Duk binta sukai da kallo kafin Mahmud ya jiyo yana kallon ta ya langwabe fuska yace kanwata anya zan samu karbuwa kuwa gun Gimbiyar yama sunan ta ya fada yana dan murmushi
Sunan ta Maryam kaikuwa yayana ya daga kallon nan da tai ma jikin ka yai sanyi ai sai kabani kunya.
Murmushi yai mata yace ynxu dai yaushe kike ga zanzo mu gana nida Gimbiya sbd Allah ya sani tunda na ganta kun fito daga shagon nn naji ta tafi da zuciyata.
Dariya sumy tai tace toh Alhamdulillah lallai kuwa in ka mallaki zuciyar ta ka chaba don kawata badai tsada ba
Shima yar dariyar yai yace ynxu dai ki ban numbern ta plz sai na kirata mu dinga gaisawa kafin ta tsayar mun da lokacin da zanzo.
Shiru sumy tai tana don tunani kafin tace gaskia bata da waya sai dai ta mamanmu amma bara in nashiga zan fadama mamanmu in ta amince toh shikenan kaga sai kuna waya ta wayar ta.
Kara langwabe fuska yai yace ynxu yaushe zan san maman tamu ta amince tunda bansan numbern kowa naku ba.
Cikin sauri sumy tace kazo ran Saturday in Allah ya kaimu kawai kaga duk ansar da mamanmu ta bayar sai kaji.
Shiru yai shidai Allah ya sani Saturday tai masa nisa kafin yaga Gimbiya amma bkm.
Ciro kudi yai a aljihun sa yabama muhd yace abokin gashi kasai sweets.
Kin karba muhd yai yana murmushi yace ngd Yayanmu.
Cikin jin dadin ya samu karbuwa gun kaninta yace a’a abokina karbi kasai sweets kaji.
Kara noke kai yai yace ngd Yaya Maryo tana bani kudin makaranta kuma in na karba saita zane ni ba ruwana.
Dariya yai yana kara jin son Maryo a ransa daga dukkan alamu tana da tarbiyya daidai gwargwado Alhamdulillah ya fada a fili.
Sallama sukai masa suka nufi soron, a tsaye suka ganta.
Ina hango su kuwa na balla musu harara na juya na shiga gidan, don dama naki shiga ne kar mamanmu ta ga ni na shiga sukuma basu shigo ba.
Tsakar gidan ba kowa wanda hakan ke nuna umma ta fita knn.
Tabe baki nai kawai muka shiga dakin mu da sallama.
Amsa mana mamanmu tai tana zaune a kan ledar falo don bamju da kujera ko daya amma falon yayi kyau a share yake tsaf kuma sai kamshin turaren wuta yake da mamanmu ta kunna.
Dukkan mu zama mukai muna gaishe ta, amsa mana tai tana kallonmu dukkan mu da alamar gajiya a tattare da mu.
Cikin farin ciki muka shiga bata labarin yadda nayi ciniki yau itama tuni ta hau murna tana kara sama sana’ar albarka.
Jakata na bude na dauko 500 din datai ragowa na mika mata nace gashi mamanmu ki rike ki sa mana albarka.
Kin karba tai da tana cemim bayan duk na kashe kudin a siyo madara da sugar kawai na rike sai da taga na yi raurau da ido sannan ta karba tana ta samin albarka.
Sumy ce tace mamanmu albishirin ki.
Da sauri na kalle ta ita kan taki kallo na ma don kar na kawo mata cikas tana kallon mamanmu da tace goro fari kar.
Yau masoyiya tayi kasuwa mai albarka don saurayin har nan ya biyo mu a mota yana da kirki wallahi ko muhd.
Da sauri muhd daya fito daga wanka kasancewar muna shigowa wanka ya fara don munyi salla a makaranta yace eh wallahi mamanmu yana da kirki yaban hannu muka gaisa kuma yaban kudi amma naki karba.
Tunda suka fara mamanmu bakin ta yaki rufuwa sai kallona take tana murmushi a ranta kuwa sai hamdala take tana fatan ya kasance mutum na gari.
Kallona tai tace wai haka maryo.
Turo baki nai kawai ina kauda kaina.
Hakan da nai yasa duk suka fashe min da dariya
Nan fa sumy ya zage tana ta fadawa mamanmu yadda sukai dashi.
Mamanmu tace kinyi hankali Sumayya Allah ya kaimu jibin in yazo ai sai a bashi numbern wayar ki tunda kinga ni bani da ita kafin Allah ya hore na siya.
Da sauri na dauko jaka ta ina budewa na galla ma sumy harara nace duk kin sa na manta abin alkairin da na siyo wallahi sai surutu kamar aku
Mikowa mamanmu ledar nai nace gashi mamanmu.
Kallona tai tana budewa ganin waya a leda da charger yasa tace ta wace wannan maryo a ina kika samo.
Murmushi nai nace biyawa mukai na siya miki dama na dau sim dinki da zan tafi makaranta na sa miki sim din hadda kati nasa miki a wayar.
Rike wayar take kwalla na taran mata a ido tana kara gode ma Allah daya bata ya’ya masu jin kanta shiyasa wani abin da malan yake mata nai ciki damun taba.
Kallo na tai tace ngd sosai Maryo Allah yai muku albarka gaba dayanku yabaku abokanan rayuwa na gari masu albarka ya kare mana ku aduk inda zaku shiga.
Dukkan mu muka amsa da Ameen.
Nan muka zauna saida muka gama cin abincin rana shinkafa da wake sannan sumy ta tafi gidansu.
Nan muka zana mama ta tayani nayi gullisuwar da alawar madara muna yi muna hira har na gama.
Haka washe gari muka tafi makaranta kafin mu dawo kam duk sun kare gullisuwar da alawar madarar cinikin dubu har da dari bakwai nai.
Ranan Asabar kuwa tun da na tashi nake jina wani sako sako don in na tuna wai yau wani zaizo zance gurina sai naji gaba na ya fadi
Sumy da mamanmu kuwa sai murna suke acikin kudina na bama muhd ya siyo pure water guda biyu da fanta daya.
Bayan magriba mamanmu tasa nai wanka na shirya cikin kayan Sallah ba na sallar da ta wuce baban su sumy ne ya min.
Riga da skirt e sun min kyau kuma sun kamani sosai hakan ne yasa bayan na shafa powder da kwalli na zura hijab dina iya gwiwa.
Na zauna zaman jira????
Sumy na gefena tana ta dariya itama tasha hijabinta duk da tace baxa taje su gaisa ba sai zai tafi.
Da gudu muhd ya fado falon yana cewa yaya yazo wallahi yace nakira ki…………
Comments nd share plz
More comments more typing
Mrs A.M????????
????????????????????????
NOOR
????????????????????????
Written by
Mrs A.M
Page 8
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Gaba na ne ya fadi jin abinda Muhd yace, dama kuma gashi tun safe nake jina wata sako sako sbd banta ba ni ko tsaya wa da saurayi ba sai gashi ynxu kuma zance zanyi ma.
Sumy ce ta tabo ni tana dariya tace “toh amaryar mu tashi ango yazo naga tun dazu dama sai dauki kike”.
Kallom ta kawai nai nace “hmm” don ni kadai nasan yadda nake ji.
Ganin banida niyyar tashi yasa mamanmu zuwa ta kamani ta daga ni, cikin taushin murya tace “Maryo ki kula da kanki yau zaki fara fita hira ki ji tsoron Allah ki tuna Allah na kallon ku ko mu bama kallon ku”.
“Tabbas bawai ban yarda da tarbiyyar da nai miki bane ko daya, kawai ina kara tuna miki ne, sai da mamanmu tamin nasiha sosai taga alama kuma sun samu zama a jiki na sannan tace jeki Allah ya zaba abinda yafi alkhairi”.
“Ameen” sumy da muhd suka ce.
Hannuna sumy ta kama muka fito a dakin sbd da tace baxa taje su gaisaba mamanmu tace gwanda ta rakani in ba haka ba sai na shiririta.
Cikin nutsuwa nake tafiya bayan sumy ta juya kaina yana kasa amma hakan bai yanani satar kallon sa ba yana zaune akan tabarmar da mamanmu ta bama muhd ya shinfida masa
Yasha shadda kalar kasa mai turuwa da hular sa data hau da kayan sai kamshi yake zubawa.
A hankali na zauna a karshen tabarmar ina sunkuyar da kaina, cikin nutsuwa na ce “masa ina wuni ya gida da su Mama” bayan nai masa sallama.