NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ka bar gaya min maganar banza ce maka akayi wani abu ne? Ko ka manta dauko ta nayi babu sanin inda take, nama fasa barin ku tafi kawai zata zauna na mai da ita da kaina”
“Oppa!!”
“Mimih” ta kira sunan shi, shigowa muke ina cewa Alman.
“Wallahi  sai na gani, kut ka sumbace Ni? Sai na rama wallahi” muka shiga zagaye dakin.
“Wannan wani irin iskanci ne!???” Ya buga mana tsawa, sai da kaina ya sara.
   Kallon shi nayi tare da cewa.
“Toh kuma Meye  nayi kai kace kar na kuma zuwa,.yanzu ka kira kana masifa, zo mu tafi Alman” na riko hannun shi. Ganin shi aka yi ya diro daga gadon, cikin fushi ya cire robobin jikin shi.
Ya fisgo ni, muna fuskarta juna.

“Kar na kuma ganin ki da kowa har Faisal idan na ganki da shi sai na miki abinda zaki ji tsoron kowa a rayuwar ki kin ji ko baki ji ba” ya fada idanun shi cikin nawa. Bakina yana rawa Idanu na cikin nashi na gyada mishi kai ina jikin jikina ko ina yana rawa.
“Fita min da gani” ya ture ni, na fadi a kasa.
“Bana son ganin kowa a nan kowa ya fita” ban iya tashi ba sai da Rahmah da NaNa suka taimaka min, sai lokacin na samu damar kuka.
“Toh ni bazan yi farin cikin ba kenan? Kai kullum kayi ta takura min sai kace ni daya ce.” Na fada cikin matsanancin kuka,

“Ka gaya min Meye na maka da ka tsane ni?” Na fada da Æ™arfi. Juyawa yayi ya ce.
“Ku rufe min kofar”
Takowa yayi gaba na, ya rasa ma me zai ce min kawai ya koma bakin gadon shi ya kwanta, tare da tab’a wani abu dai ga nurse haka ta zo ta gyara mishi kome na shi. Ni kuwa ina tsaye ina kuka.

   —
“Oppa ya fada dayawa” Seyo ta fada
“Inji waye? Kawai yana bata kariya ne dan ya dauke ta a inda ya dace ta zauna ne.”
“Allah da gaske kishi yaÆ™e” shiru Faisal yayi yaki magana, dan yasan tabbas za a rina, amma kuma haka na da matukar hatsari ga ita rubin.

  … Zama nayi na ci kuka na koshi karshe na kare da barci a sofar dakin,  dauke kai yayi tare da harara na.

…. Haka na zauna a wurin shi har dare, da umma ta dawo ta dauke ni. Muka dawo gida, a hanya nake mata kuka da rokon ta, akan ta saka baki na koma gida, shafa kaina tayi tare da cewa.
“Zai bari koma kin ji” gyada mata kai nayi,
… Ina shiga dakin da nake naga Mimih da Jamilah.
“Karuwa ce shi yasa ai take makale da shi. Yarinya da ta gama zagaye duniya da bin maza so baki san me yake mata ba, mu kan ai muna ganin karuwanci.”  Ita Mimih bata bani haushi ba, amma ita Jamilah ta bani haushi ban kula su ba sai nuna musu kofar da nayi, haka suka fita suna zagina ban kula suba.

    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya ina fuskarta kalubale daga Jamilah da Mimih, shi kuma idan ban je asibiti ba kamar zai dawo gida ya dauke ni. Dan haka na dauki kudin shi a dakin shi na hada kayana nayi tafiya ta, ba yau na fara tafiya ba. Dan haka dakyar na samo passport dina dakin shi, wanda yayi min a London domin lokacin da ban da lafiya bai samu yi min ba . Sai da na warke yayi min ta london.

    Dan hakan na tattara kome nawa na dawo lagos aiki ne da kamfanin shi na hakura.
Lagos.

Lokacin da na iso gidan mu dare yayi dakyar na samu aka bude min kofa, ina ganin Mama ce na fada a jikinta ina kuka.
“Kina kukan rabuwa da shine ko kina kukan kewar mu?” Kura min ido tai ganin yadda nake share kwalla, wani na zuba, kama hannuna tayi ta kai ni daki.

    Kwanciya nayi domin ba zan iya magana ba, shafa kaina take a hankali har barci yayi gaba dani.  Tashi tayi ta shigo da da kayana, sannan ta fita zuwa dakin ta.

   **
Shiru Umma tayi tana kallon Jamilah.
“Ke kin kyauta da kike…

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/9/22, 16:49 – Nuriyyat: 66
“Kike ci mata fuska? Ko gidan ku babu mafadi ne? Ba nan aka lalata auren ki ba sabida abinda ya faru dake? Ina ruwanki da Rebecca akan ku take? Idan zaku koma Faisal ka tafi da Nadiah, zaman ya isa haka gidana ba matattarar yaki bane, ina ce kun kore ta ne dan Gong yoo ya damu da ita? Toh ta bar muku shi sama ko baku kore ta ba, zata tafi sakarkarun banza”

Tayi musu tass, sannan ta hana a gayawa Bilal ta tafi domin ta san shi zai iya hauka ce musu. Haka suka yi shiru. Babu shiri Faisal ya fara shirin dawowa gida.

   —
“Ina tambayar ku ina yarinyar take babu me bani amsa meye nufin ku ina Yarinyar take” Umma da shigowar ta kenan ta ce mishi.
“Ta koma gida”
Sake baki yayi yana kallon ta kafin ta ce mata.
“Akan me?”
“Sabida naga haka ta dace da ita” shiru yayi tare da cewa.
“Faisal kira min nurse a sallame ni” sake baki suka yi har Umma ta ce mishi.
“Babu inda zaka sai ka warke domin bani ciki da shahshanci”

  Ta fada fuskar a hade dan dole ya hakura.
     Kuma ya rasa wanda zai gaya mishi abinda ya faru, dan haka dole, ya hakura ya zuba musu ido. Ranar wata Laraba Faisal suka zo mishi sallama. ta shi yayi yana kallon su.
“Ban san me zance ba, amma inshallah idan naji sauki zan zo kaji, sannan ka kula min da kowa da kowa, kace ina kewar su.” Kallon shi tayi tare da rike hannun Faisal.
“Kana kewan ta ne?”
“A’a” ya fada, a hankali kafin ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

  “Ok, Allah ya baka lafiya sai mun ganka” inji Faisal,gyada kai yayi. Abinda Rubih tayi yayi masa zafi domin da yau wata babba ce sai ya bata mamaki, har Faisal ya kai bakin kofa ya ce mishi.
“Karka manta ka duba mana wanda zai kula da department din mu na sadarwa.”

“Ba mun magana magana ba, waye kake tunanin zai iya kula da wurin bayan ita?” Shiru yayi bai ce kome ba,  musamman yadda Faisal ya tsare shi da Idanu.
“Allah ya kyauta ok zan nimo” ya saka kai ya fita, bai kuma juyawa ba dan yasan Bilal din matukar zai tsaya sai sun raba hali.

     Kallon ciwon jikin shi yayi dan yasan shi ya hana shi rawan gaban hatsin, yayi bakin cikin ciwon yaso da lafiyar shi lau, ya yafi yaci Kaniyarta. Amma tayi na kudin ta zai kama ta.

  A daren ranar su Faisal suka bar korea, har da Mimih abin yayi mata zafi, ita kuma Umma tai haka ne domin ta ce matuƙar ba Rebecca ba, babu yar banzan da zata zauna mata a gida. Haka ya sa duk aka tattara su, sai Yaran ta. Itama Mama Ha Na taji Haushin tafiyar Rebecca. Shi yasa ga bawa Faisal aikan Rubin ita kuma Umma suka hada mata kayan ta da ta bari.

Faisal
Sai da suka biya ta Dubai suka huta kafin suka samu jirgin lagos, suka dawo, motar da yazo daga gidan Hajiya Humaidah ya dauki Mimih sai Jamilah su, suka mai da ta gidan, kallon Rahmah tai lokacin da suka shiga gaida Ammyn take cewa.

“Mrs Faisal Shema, ki rubuta ki ajiye kamar yadda kika gayawa Mahaifiyar Bilal haka zaki koma ki gyara abinda kika b’ata. Ammyn mun dawo yana gaishe ki” ta fada tare da nufar cikin dakin su.
“Meye ya faru Rahmah?”taji muryan Ammyn.

“Babu kome.” Ta fada tare da mata sallama, bayan tafiya ta, Ammyn ta shiga har dakin Jamilah, ta shiga tambayar ta me ya faru.

“Babu kome, kawai wata karamar karuwa ce zata shiga tsakani na da Bilal har da goyan bayan Rahmah da mijinta bayan kowa yasan cewa akwai alaka a tsakanin mu da Bilal, Ammyn ai kin san akwai Alaka a tsakanin mu da shi. Yanzu Misali idan Rabi’ah ta dawo ta ce tana son Bilal me zan iya yi akan haka?” Kura mata ido tayi gaban ta yana faduwa.
“Allah kar ya nuna min ranar da zaku tsaya kuyi fada akan namiji daya, ki hakura fa Bilal ga Aaman yana sonki” sake baki tayi tana kallon Ammyn kafin ta ce mata.
“Kenan idan har ace Rabi’ah zata so Bilal haka zan hakura na bar mata shi? Ammyn wannan soyayya ce ko son kai?  Tsakaninki da Allah ba zaki tsaya a tsagina ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button