NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake dukar motar mu babban motar tai, tayi take motar mu tayi ta dunkure. Tun a dukar farko kan Ammyn ya bugu da glass din motar,  ta sake salati tare da riko hannuna. Gam bata sake ni ba, haka motar yayi ta dunkure damu, har muka fada babban ramin gutter. Baka jin kome sai ƙarar motar. A hankali na bude idanuna ina kallon mutanen da suke zagaye da motar, suna dariya. Kome kan shin motsi idan aka yi fadawa ramin zata yi, domin yana gab da fadawa ramin haka ya sani jin wani irin ciwo a rayuwata.  
“Ka fada musu harkalla ta fada, saura cash”

  Daga haka ban kuma fahimtar kome ba,

Bayan mintinan talatin, motar asibiti suka iso aka da ta yan fire Services,  aka zo aka janye motar su Bilal,. Cikin ikon Allah ana bude kofar motar Bilal ya farka, rike da kan shi. Kusan da shi aka ciro Faisal da yayi dogon suma, sai Ammyn da Rubih da aka ciro su, ita kan Ammyn babu abinda ya same ta kamar me barci ma aka suka fito da ita, Rubi ne jini ta hanci ta baki, da sauri a  ka sa kata a motar.

              “A’a karku kai mu TH ku kai mu Jikamshi Hospital.” Ya fada yana rike kan shi, haka aka yisa Asibitin cikin kankanin lokaci aka gama musu kome, Namir shi ya kira Alman ya gaya mishi, shi kuma ya gaya Ummin basu bari Rahmah ta sani ba, haka suka tawo asibitin aka kai su dakin da suke. Ajiyar zuciya Ummin tayi ganin su ukun gasu nan a raye. Ammyn ce dai babu.

   Ga Faisal baki daya aka rasa wanda zai iya gayawa su Jamilah. Dole Alman ne ya kira Yan sanda, su kuma suka kira Aaman, baya lagos amma bai yi kasa a gwiwa ba ya kira Mahaifin shi, Allah ya taimaka Alkasim yana gari shi ya tafi ya yiwa su Wasilah magana, babu shiri suka nufi asibitin dake ba a gaya musu rasuwar Ammyn ba, koda suka isa sun sami babu Ammyn. Wani irin zaman yan bori, Jamilah tayi tare da sake wani irin kuka, kamar ranta zai fita.

Kuka take tana ihu, sai da aka fitar da ita, har washe gari ana cikin tashin hankali, haka aka É—auki Ammyn zuwa Jama’are,bayan an yi mata suruta dake danginta sun bukaci haka, Rahmah kam, Haihuwa ce tazo gadan gadan, cikin saura kwanaki ta cika tara, babu shiri ta Haifin Yaronta tabarkallah, dole aka batar anan sabida yanayin halin da take ciki jinin ta yayi mugun hawa, wanda ya haifar mata da kumburi, ga rashin Uwa ga miji yana cikin coma.

    Har gwara Bilal shi, kan shine ta bugu,kuma an duba babu matsala sabanin Rabi’ah da buguwar nata yayi muni.

Hatsarin da kwana biyu, yaji sauki sai ciwon kai, dole aka shirya mishi tafiya  Korea sabida ganin likita. Haka ya saka aka shirya har da Faisal da Rabi’ah, suka tafi. Rahmah sun tafi Jama’are da Ummin sabida tashin hankali da suka shiga, sai da aka yi addu’ar Bakwai sannan suka dawo Alman ya shirya mata tafiya Korea. Domin yan uwan Ammyn sun so riketa a mata wankar jego amma ta kasa hakuri domin gani take kamar Faisal ya mutu boye mata ake, shi yasa suka dawo lagos,. Tare da kama hanyar Korea.

     *
Dariya suke tare da cewa.
“Bilal kadai ya rage, itama Yarinyar an ce ta mutu ko?  Shi daya zai kawo mana matsala, tunda an shigar bayanin ta mutu shi kenan” inji Hanan.
“Dama shirin da kike kenan? Ai da na sani da na kara miki da wani aikin.”  Juya Idanu tayi tare da cewa.
“Wani aiki Alhaji Adamu?”
Gyara zama yai tare da mika mata hoton Jamilah.
“A san yadda za ayi a shirya kome a kanta. Ta gane shigar ta JF Group masifa ce babba, a shayar da ita bala’in da  bazata tab’a mantawa ba, idan da hali akara mata fyaden da zai haukata tunanin ta”

  “Hmm! An gama magana” ta fada tare da kallon Alhaji Adamu.
“Duk wanda ya nime shiga rayuwata ina d’aga mishi kafa ban da wanda ya nime tab’a min dukiyata ba, a mata kome”

   **

Tunda suka isa Korea, sun samu Matsalar Bilal babu wani tashin hankali kamar matsalar Faisal da ya bugu a Kirjin shi, sai Rabi’a da jini ya kwanta mata a saman Æ™waÆ™walwar ta, toh suna da manyan likitoci. Da suka amsa sunan su, dan haka a satin su na biyu da zuwa aka musu aikin da a tarihin ba a tab’a makamancin haka ba, domin aiki ne na tsawon awa ashirin cif, sannan aka fito da su, tare da fatan nasara.

    Ita kan Rahmah ta lalace baki daya, dan ma Umma tana kokarin kula da ita, Ummin kuma da Yaron wanda aka saka mishi Ahmad sunan Baban Bilal, idan ka gan shi yana shan nono ya koshi uwar ce dai a dame.

    Haka suka yi kasance har tsawon kwana huÉ—u, kafin Rabi’ah ta fara farkawa. Alamar da Computer din yayi ne ya saka aka fara tururuwa shigowa. Suka shiga duba Vital, Pulse dinta, da Bp. Duk normal. Dan haka suka shiga kiran sunan ta.
“Mrs Gong Yoo! Kina ganin mu?” Kumshe Idanu tayi ta bude, suna nuna mata hannu, yatsu tabi da ido. Sai dai ba magana.

Haka suka gama abinda zasu yi suka mata allura, sannan suka fita suna gaya musu su kwantar da hankalin su shima Faisal zai farka, abin gwanin ban tausayi,haka ya kara gigita Rahmah dan tana ji tana gani mijin ta idan ya wuce kwanakin da ya dace za a iya cire life support din da aka saka mishi. Idan ta yi sallah ta fara karatun Alqur’ani, sai jaririn ya motsa take ajiyewa dukkan su Bilal ne akan su. Kasancewar ya samu lafiya sosai..

Duk wani dawainiyar mu shi ya sauka, tun kafin na farka yaƙe kokarin kwantar da hankalin Rahmah.  Har na farka, ina iya tashi na zauna.

     Sai dai bana hmm bana uhmm, haka ya kuma d’aga musu hankali, dan haka aka shiga bani magani tare da kokarin sake min wani aiki. Amma naki yarda, dan dole aka kyale ni. A wannan karon ba zance Bilal kome ba, domin lokaci guda yake warewa yake min hidima, abin burgewa.

“Ci abinci ko auta?” Ya fada min lokacin da ya sauko noodles yana bani da chopsticks, amsa nayi ina kallon shi.
“Nasan tunda aka kika ce kar a Miki aikin nasan lafiyar ki lau gaya min, meke damunki?”

Mutanen da suka kashe Ammyn nake son kama su kashe su, shine Hankalina zai kwanta na rubuta mishi a yar farin takardan da yake saman wurin ajiye magani na, kallona yayi tare da cewa.
“Bana son kina wanka da jinin Mutane, domin bana son haka ya tab’ a min rayuwar ki da na Yaran…”

Kallon shi nayi sannan na É—auki biron na rubuta kamar haka.
Zan kashe su koda hukuncin kisa ne a kaina

“TOH me yasa ba zaki min magana ba? Bana jin dadin haka?” Ya fada min,  

Hmm
Na rubuta mishi, sai dai bana jin dadin yadda nake mishi. Wa shi gari yana sallah aka Alman ya shigo da gudu, ya samu yana sallah.komawa yayi tare da gaya min Faisal ya farka. Murmushin farin ciki nayi, tare da sauna a gadon na nufi inda yake dakin shi yake da likitoci a cikin dakin suna ta mishi tambayoyin su nan me shegen hawa kai.

**
Jama’are.

   Motar Yan sanda uku ya shigo unguwar su Ammyn a kofar gidan su Ammyn ya tsaya, yan sanda mata suka shiga cikin gidan, da sallama.
“Ina Jamilah take?”
“Gani nan?”. Kwashe ta da mari yar sanda tayi, daidai fitowar Wasilah, da gudu ta fito ta kifawa Yar sandan Mari.
“Ke! Kika mari yar sanda!”
“Hafsat dauko min jakata,ki bani Ita. Na mare ta ta gaya min dokar kasar da ya bata damar Marin Farin hula? A wani kundin tsarin mulkin Æ™asar ne? Ita civilia ce, a ina aka baki damar haka? Daga IG ne? Ko daga mataimakin IC ne?” Mika mata jakar aka yi,ta ciro ID card dinta Barista Wasilah Ishaq DaÆ™ayyawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button