NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Tunda ya zauna kome ya kunce mishi, kwantar da kai yayi yana kara nazari. Yarinyar tayi kankanta da karuwanci! Ya fada a ranshi dafe goshinsa yayi tare da jin kamar ya kurma ihu.  Sakamakon kalaman ta da yake dawo mishi.
“Don Allah kar ka min haka! Don Allah kar ka min haka,  don Allah kar ka min haka”  duk da duhun dakin da kuma mask din da yake Fuskar ta, ya kara tabbatar mishi da cewa yarinya ce qarama.

  Tashi yayi ya nufi window falon, yana kallon waje. Kusan ranar yana tsaye a wurin, har aka yi kira sallah sannan ya nufi masallaci estate din, yana idarwa ya cigaba da zama a cikin masallacin a nan ya zauna har Isha. Sannan ya fito a wajen Masallacin ya hadu da Irfan. Dauke kai yayi tare da cewa.
“Gong Yoo! Babu yaki Meye ya kawo gaba?” D’ago kai yayi tare da murmushi.
“Ya kake Irfan Kabir Wazir!” Sauka yayi daga bayan motar, ya ce mishi.
“Na ji kana gab da bude kamfanin ka. Yaushe ne?”  Wani tab’e baki yayi tare da d’aga kafadar shi ya ce mishi.
“Ban sani ba” sannan yayi gaba abin shi.
“Ok naga kamar sakataren ka yana da kokarin bin baya ko koyarwar ne?” Dunkule hannun shi yayi tare da juyawa ya kalli Irfan sannan ya sake murmushin gefen baki ya wuce abin shi.

  Koda wasa bai bukata bawa Irfan amsa ko wani damar da zai nuna ya gaza, shi yasa yayi tafiyar shi tunda bai isa ya tare shi da duka ba, magana ce, zai bashi amsa a hankali.

**
Bude Idanu nayi, naji ji ni a cikin wani irin wuri kamar duhu kamar dai cikin abu nake, shi ba rami ba shi ba kuma tab’acin gini ne, shiru wurin can, aka bude saman kamar wanda yake cikin rijiya haka wurin yake, tsani aka saka, a hankali aka sako wata irin fitila me shegen haske.

    Kashe min Idanu yayi sai da na kare idanuna, a hankali na lura ashe bani daya bane a dakin, ga wasu a kwance can gefen mu wani ne a kwance kamar Ya mutu kamar ya.
“Oga wannan wannan mutuwa zai yi fa?”
“A jefa shi a ruwa” wani irin tashin hankalin ne ya kuma kama ni, wani jarka aka ajiye mana, da sauri kowa yake kokarin dauka ya sha ruwan, sai mutumin yasaka kafa ya ture, haka muke bin ruwan domin musha, amma mutumin nan yana turewa.

            Komawa gefe nayi na zauna domin dakin ba iya maza bane hatta mata akwai su, suma kokuwar dauka suke har suna yaga tufafin su.

“Ku dauka kusha mana” komawa gefen da nayi na hakura domin abinda suke kamar dabbobi haka mutanen dakin suke.

“Zamu baku kusha amma sai kun kwanta da junan ku” ja da baya nayi sosai tare da k’amk’ame jikina, abinda ya faru ranar yana dawowa a kaina, wani irin tsoro ne ya kama ni, sai gashi mutane domin su ci abinci sun kama zina.

      Su kuwa sai dariya suke suna faɗin.
“Wancan ya fi wancan kuzari, a’a wancan gaskiya yafi” ina manne a wurin har aka gama, sannan suka watsa musu bread da wani irin abu kamar madara kamar nono, juyawa Babban su yayi ya haska min torch lighter a fuskana, na Æ™are da hannuna.

     ” Ke Yar uban waye da ba zaki shiga ayi dake ba?” Kallon shi nayi tare da cewa.
“Ni ba Yar uban kowa bane, kawai ba zan shiga kazamtar ku bane, domin ni kamar sarauniya ce.”

“Ku dauko min shegiya” haka suka dauke ni, har wajen suka fitar dani. Wani irin isa me dadi na shaka, ware Idanu na nayi, tare da kallon inda Ƙaddara ta kawo ni, watsar dani suka  yi. Sannan suka shiga bina da duka sai da nayi laushi har bana numfashi me kyau. Sannan suka ja ni har zuwa wani daki aka watsar dani.

    Shigowa ogan yayi ya zuba min ido,kafin ya shiga yaga rigar jikina ya É“alle haf vest din jikina, hàdiye yawu yayi. Ya saka hannun shi baki daya ya caccumo nonuwata, rintsa Idanu nayi. Tashi yayi tare da had’a ruwan zafi, haka ya jani har ban dakin ya tsoma ni, ganin bani da kuzari ya saka shi kai hannun shi kasata. Da sauri na rike hannun shi, tare da janyo shi sai da ya fada cikin ruwan matse kan shi nayi sai da naga baya motsi, wato yasha ruwa ya koshi. Har ya suma sannan na tashi kayan shi na saka, tare da leka,  na farko idan nace zan gudu ban san ina ne zasu kai mu ba, dan haka na koma dakin na zauna domin ban hango iyakar tekun ba.

Haka na koma dakin na zauna ina kallon shi, har ya farka. Yana tashi ya koma gefe yayi tare da kallona, shi kansa ya razana dani,

“Ƙarki min kome!” Nima ja da baya nayi, ina kallon shi.
“Ina zaka kai ni? Taya na shigo jirgin nan?”
Ta shi yayi tare da dauko wani key, ina kallon shi ya kai ni har wani daki, kaya ne a rufe a wurin.
“Ga kayan ki, madam Tola ta haÉ—a mu”
Kaya ne me mugun yawa, kallon shi nayi tare da cewa.
“Nawa ta bika?”
“Kiyi hakuri”  ban ce mishi kome ba, na wuce dakin shi na kwanta, haka na gyara gadon shi na kwanta.

    **
Jama’are.

Kallon Rahmah Ammyh tayi, kafin ta ce mata.
“Ina son na kai ku DaÆ™ayyawa ina ga kamar ayi bikin a can zai fi nan!” Shiru yayi bata ce kome ba.

“Rahmah kina jin labarin  Jamilah?” Murmushi Rahmah tayi kafin ta mai da kwallar da yake cika mata Idanu.
“Tana lafiya “

“Wasilah tana lafiya?”
“Suna lafiya” haka ta ture abincin gabanta, karar wayarta yasa ta dauka.  Tare da kallon Ammyn ta ce.
“Ina wuni?”
“Lafiya Yan mata ya kike?”
“Lafiya lau” ta bashi amsa,
“Meye zaki yi ki turo min, next week zasu kawo kayan auren”
“Babu kome, Allah ya kai mu” ta faÉ—a, tunda aka fara maganar auren su ya lura bata sakewa da shi kuma dama can haka ne, bata yarda ta sake da shi, dan haka ya ce mata.
“Zan zo Jama’are”
“A’a don Allah kar ka zo” ta fada tare da jin kwalla na cika mata idanu.
“Meye nufin ki?”
“Babu” ta fada kamar zata yi kuka,
“Ko wani abu na miki?”
“A’a wallahi baka min kome ba” shiru yayi kafin ya ce mata.
“Ok zamu zo da Bilal”
“Allah ya kawo ku lafiya”
“Ki gaida Ammyn, yar kauye kawai ko soyayya baki iya ba, kina nan kullum kamar yadda na san ki. Ki shirya domin wallahi Ni ba sakarai bane idan na saka ki gaba da soyayya sai kin gudu”

    Shiru tayi bata ce kome ba, kawai murmushi kawai tayi. INSHA ALLAH zata shirya zama da shi koma ya yake zata zauna da shi.

Bayan sun gama magana ne ya kashe wayar, tayi tana Murmushi tare da sosa kai.
“Kina son shi ko?”
Sake sunkuyar da kai tayi tana jin wani irin kunya, ta gyada mata kai.
“Allah yayiwa Rayuwar auren ku albarka”
Shiru tayi tana kallon ta, kafin ta ce mata.
“Gashi Jamilah ta ki zuwa, kuyi hakuri da yan uwanki”
Gyada kai tayi tare da sunkuyar da kai tayi tana kallon kasa.
“Ina son ku baki daya ina son ku sosai, ban tab’ a jin kome akan ku ba, ban tab’a banbanta ku ba, amma Jamilah ta min kallon ina son kai.”

Shiru tayi bata cigaba ba, ba kome bane yake kara mata ciwo kamar yadda Jamilah ta kwashe takardun su, a ina take ma yanxun? Me take da takardun.

“Allah ya shirya zuri’a” ta fada tana kallon kofar dakin ta.
“Idan aka gama bikin ku zan koma DaÆ™ayyawa”
“Hmm! Ammyn mu, ba zaki koma DaÆ™ayyawa ba, lagos zaki zauna. Baki nan sai Abinda  Jamilah ta gadama take, gwara kina nan ace kin barta a can babu wanda zai mata fada, ke Uwa ce bai dace kina karkata akan gefe guda ba….
Kuyi hakuri bamu da wuta ne wallahi

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button