NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   Karan abu naji sai lokacin na fahimci, ashe a cikin jirgin kasa muke, ko da aka bude mu, fita kowa yayi Nima na taso, wuyata sanye da wata irin sarka, kayan nan dai sune a jikina. Ina fitowa naga wata mata ta nufo ni sanye yaƙe da riga da wani wando legishole, sai karamin shima a cikin Black Jacket din jikinta.
“Rebecca!” Gyada mata kai nayi sannan ta ce min.
“Siren James, Mss Jessica Simpson ta kawo min kome naki, amma taya aka yi kika rayu bayan naji an ce tayi gobara ta kone?” Kallonta nayi da fuskana da ta bushe da jini nace mata.

“Na tuna an buge ni da wani abu a kaina bayan nan kuma ban kuma sanin abinda ya faru ba.” Shiru tayi kanta a sunkuye, kafin ta ce min.
“Ok zo mu tafi babu lokacin ya fara kurewa.”

    “Amma ina zamu?” Na tambaye ta, ina kallon wurin da yake cike da yan mata da maza.
“Zamu je taron mu na kasa da kasa ne, a Mexico” maganar Maama ne ya fado min.
Zasu tafi dake ki nutsu domin ba tafiyar da zaki yi bane domin jin dadin ki, duk wani abu da ya faru a can ne aka shirya Nicole Brohna

“Maama ta baki wani abu ki ajiye min?” Na tambaye ta da sauri,
“Eh ta bani su!” Ta kamo hannuna har wurin wani akwati, kallon shi nayi sannan na kalle ta nace mata.
“Taya aka yi na zo nan?” Shiru tayi tana kallona.
“Taya aka yi nazo Ban?” Na kuma daka mata tsawa,
“Kiyi nazari mana”

Shiru nayi domin kome ya tsaya min cak, gashi tafiyar mu yana gab ta fara tafiya. Ganin ina niman daukar wani abu yasa ta fara magana.
“Kiran Yan kwana kwana da akayi ne, lokacin da gobaran ta tashi shine muka samu dauko ki”. Wani irin sarawa kaina yayi na rike shi, tare da durkusawa kasa, ina Æ™oÆ™arin tuna abinda ya faru. Tabbas an jani a kasa tare da saka ni a bayan mota amma ban san Meye ya faru ba, juyawa nayi ina kallon ta.

“Kin san me ya faru, wacece Kelly Clarkson?” A hankali ta zauna tare da É—aukar karar sigari ta kunna, sannan ta ce min.
“Muje zan gaya miki wacece Jessica Simpson da Kelly Clarkson.”

   Daukar Kayana yi, sannan na bita kuka shiga jirgin kasa, da zata fitar damu zuwa bakin koge, daga nan kuma mu shiga jirgin ruwa. Tunda Muka shiga sai na kasa kuka, na kasa kome amma ina ji a raina labarin da ta bani na a kawo ni, kamar ba haka bane kwanciya nayi a kujeran jirgin, sabida ciwon kan da ya kamani, har muka iso bakin Kogin, ananne muka sauka tare da saka kayan mu a cikin jirgin ruwan.

      Tunda muka shiga cikin jirgin ruwan ta kalle kafin ta fara magana da cewa.
“Suna na Annabella, an fi kirana da Anna, ni da Jessica Simpson da Kelly Clarkson kawaye ne, kasancewar mu yan kasar Mexico,  mahaifin Jessica Simpson wato Me Simpson yana daga cikin manyan Attajirai kuma masu kuÉ—in Mexico, uwa Uba yana cikin masu safarrar miyagun kwayoyi, wannan yasa suka dinke da Mahaifin Kelly Clarkson, Mr Clarkson.  Amintaka ce da babu son kai ko son zuciya.

    Mr Nicole Brohna shine abokin sune, abubuwan na cigaba duk yana kawo musu, sai dai shi ba ta cigabar su yake ba, ta yadda zai kwace dukiyar su yake, ana haka kuwa aka rasa taya aka yi hukumar ƙasar Amurika suka fara niman Mahaifin Jessica da Kelly. Tunda suka fahimci haka sai suka takaita tafiyar su, dole suka bar shi a cikin kasar, ana haka dai aka wayi gari Mahaifin Kelly da kan shi ya tafi har gida ya kashe mahaifin Jessica, sannan ya kunawa gidan wuta, bayan ya tabbatar babu wanda ya fita, a lokacin Jessica tana Miami wurin kanwar mahaifinta.

   Mahaifiyata kenan, sai jin labarin mutuwar iyayenta tayi, tana kokarin zuwa aka turo daga hukumar tsaron Amurka, aka tafi da ita rabona da ita kenan sai bayan shekara goma sannan muka hadu, anan take gaya min ai suna tare da Kelly, amma babu abinda yake shiga tsakaninsu sai fada domin inda suke horo ake basu.

     Rebecca Jessica tasha wahala domin sai da ta kai duk abinda tayi Kelly ce take kwacewa,  daga karshe Ta bar U.S ta dawo nan bayan an fitar da sanarwar labarin ta mutu,  har tsawon shekaru ashirin da biyar, Jessica ta horar da yara irinki, wasu sun tafi wasu sun mutu, sakamakon aikin kisar da suke, kuma nasan Kema ta baki wannan horon, abu daya zaki mata ki shiga Mexico ki biya alkhairin da ta miki, ga yadda ta tsaya kome.

   **
Lagos
Jikamshi Mansion.

Abin karyawa suke ci, wayar shi tayi kara. Mikewa yayi tare da cewa.
“Na koshi” ya saka kai zai fita, Alhaji Adamu Abbas Jikamshi ya ce mishi.
“Kusan shekara hudu kenan ina binka akan Yarinyar da zamu had’e ku baka ce min kome ba?”
“Abba ai na gaya maka ina da wacce nake so, sannan bayan haka bana jin zan iya sauraron kowa akan abinda nake so”

Murmushi Alhaji Adamu yayi bai ce mishi kome ba, har ya fita.
“Hello Baby, yaushe kenan? Ok gani nan zuwa” ya faÉ—a mata, bayan minti arba’in ya isa kofar gidan su, Tsaye ta ganta da Aaman.

“Jamilah kuskure kike aikatawa, ina gaya miki ki rabu da Namir” ya gaya mata yana kokarin ta fahimce shi.
“Ya Aaman ka bani wuri na wuce domin wallahi zan iya zaginka, Meye kake takama da shi, wanda nima ba zan iya takama da shi ba? Idan baka ni hanya ba zan zageka” ta fada tana kokarin wuce shi, yayi maza ya  riko hannun ta.
“Ina sonki!”

A matukar firgice ta kalle shi, domin tasan yana sonta, amma matsalar bai tab’a nuna mata alamar haka ba, sai yau. Kallon shi tayi sama da Æ™asa.
“Kar dai jin labarin dukiyar nan ne yasa har ka fara tunanin zaka aure ni domin samun kason ka? Idan kuwa haka ne bana son ka, ban tab’a son ka ba, kuma bana fatan haka please sake ni, Jamilah Ishaq ce gabanka ba wancan Jamilar da aka ketawa Alfarmar bace, matukar kace zaka kawo min abinda bai min ba zan zage ka zan ci mutuncin ka.” Tana kai aya ta kwace hannunta, sannan ta nufi wurin Dr Namir.

Shiga motar tayi tana kallon shi,
“Sorry”
“Ƙarki damu, ina tare da ke, yaushe zaki fara final exam dinku?”
“Ina tunanin saura sati Uku” daga nan suka bar kofar gidan, motar.

**
Abuja.
Gwagwalada.

Tunda ta fara karatu bata tab’a fita yawo ba, asalima bata tab’a dogon yawo ba, sabida gargadin Ammyn ta ma mace.
Wayarta da yake kan tabirin Litattafan dakin ne yayi kara. Dauka tayi domin har yanzu ba wani dogon shakuwa suka yi da shi ba, amma kuma tana jin kamar a tare akan yi su.
“Hm”
“Ina jiran ki a waje”
A rikice ta ce mishi.
“Ah.. ah .. ko zaka kira min Ammyn ka gaya mata zamu fita” ta fada Idanunta yana cika da kwalla,
“Bude min kofa”  ai kamar wacce aka sanya mata lantarki jikinta ta ya shiga rawa, bude mishi kofar tayi, yana tsaye hannun shi a harde kirjin shi. Wani irin kallo yake Binta da shi daga sama har kasa, a sanyayye ya shiga dakin, ta matsa mishi. Ya shiga yana bin dakin da ido, a hankali idanun shi ya sauka akan bra dinta, wanda ta kwaso shi a wurin shanya. A hankali ya isa bakin gadon, ya zauna yana kallon ta yadda take tsaye kanta a sunkuye. Baki daya duk lokacin da ta gan shi abu daya yake zuwa ranta yadda suka tab’a karo wurin fitsari.

“Baki iya karban bako bane?” Ya tambaye ta, a sanyayye. A rude ta bude karamin firij din dakin ta dauko mishi ruwa zata mika mishi, tsautsayi yasa ta taka pencil din da tayi amfani dashi, baki daya ta zame tare da faduwa a jikin shi.
“Ya Allah” ya furta lokacin da ta sauka, a kan shi cikin tsananin tsoro ta rintsa idanun ta. Bakinta yana rawa, sun kwashe kusan minti biyar, a cikin wannan yanayin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button