NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kamar Ya? Akwai wani abu da kuka yi ne ban sani ba?” Ganin bai dauki haske ba, kawai ya gyara zancen da cewa.
“Dama wai ko ta maka wani abu ne?”
“Ok dama mun hadu ranar a bikin da aka yi ne kuma ina bukatar ta zan biya iya adadin abinda take so please just one night zan yi”

      Sunkuyar da kai tayi, tana me kuka a hankali,tace.
“Na saka ta a jirgin ruwa ta kaita Nigeria” kura mata ido yayi abubuwa da yawa yana zuwa kan shi, mikewa yayi tare da cewa.
“Ok baki da hoton ta ne?” Dafe goshinta tayi, kafin ta shiga duba wayar ta, babu hoton Rebecca.
“Babu”  ta lumshe idanun ta hawaye na zuba mata, domin taga samu da rashi lokaci guda.

     Gyada mata kai yayi, duk da ba haka ya so ba, mikewa yayi tare da ajiye mata number shi ya ce mata.
“Koda zaki samu labarin ta, gashi nan ki kirani zan nime ta.”

   “Ok” haka ya tafi abin shi yana jin damuwa,shi wutar jarabar da yake cin shi ne, babban damuwa ba wai dan yana son wani abu bane. Ya rike kan shi na lokaci me tsawo amma yanzun baki É—aya ita yake bukata, ita yaÆ™e son ya huta da ita, shi idan da hali ma ko aurenta yayi a boye , idan ta gama samun gamsuwar da yake bukata,sai ya sake ta.

Da wannan tunanin ya koma hotel, Washi gari da safe ya bar faransa.
**
Bai shigo lagos ba, sai dare ya shigo lagos jikin shi a mace,  a wannan lokacin aka fara bikin Faisal da Rahmah, wacce suka dawo Lagos da Ammyn,  gashi Mahaifiyar Aaman tasa an mata gyaran amare, ita da su Jadwah da Jawahir. Bikin ya kafa tarihi domin baki dayan su amare a arewa aka daura auren su, anan kuma Lagos walima da wasu kananan event akayi a nan, ana gama daurin auren aka dawo nan lagos, ina aka koma bikin bude Kamfanin Bilal.

Tun daga bakin get zaka fahimci kamfanin duniya ce, duk inda aka bude dai kayi santi, haka akayi walimar baki daya. A daren kuma akayi Dinner me mugun daukar hankali, ita kanta Amaryan me kwalliya na musamman aka dauka mata anan lagos ita da su Jamilah. Idan ka gan su da Faisal sai sun burge ka.

    Tunda Jamilah ta daura Idanunta akan Bilal Ahmad Jikamshi, baki daya ta dauke wuta, a ranta kuwa cewa take ashe a tv karya suke mana, domin bata yi tsammanin yakai haka haduwa. Faisal ne ya gabatar da ita wurin Bilal tare da gaya mishi ita ce Alhaji Adamu Abbas Jikamshi ya wulakantata a ranar saka ranar auren su da Namir.

   Aikuwa ya kalli Faisal ya ce mishi.
“Allah sarki bata da wani matsala gata tafi kanwar kyau”

“Matsalar ka ce, idan kana so ka shiga a yi da kai” murmushi yayi sannan ya ce masa.
“Eh toh tana da sura me daukar hankali, daga sama zuwa kasa” ganin haka kuwa ya karasa inda take, da Wasilah suna ta farin ciki, yanayin ta kawai zai nuna maka cewa karfin hali ne Sabida yadda  yake. Zama yayi kusa da ita ya ce mata.
“Hi beauty”

   Wani irin taurari ne suke yawo akanta..
“Dani kake?”
“Wacece kyakkyawa kamar ki anan? Duba da kyau su da kwalliya suka yi kyau ke kuma babu kwalliyar”  wani irin abu taji a ranta.
   Tana lura da yadda sauran yan uwan shi, suke kallon ta.
“Kamar ban da ce da wannan yabon ba, Nagode sosai” mikewa tayi zata tashi saka mata kafa, ta koma ta zauna.
“Bani hannunki” mika mishi hannun tayi,haka suka mike a tare yana bin manyan mutane yana gabatar musu da ita, a matsayin new Bussiness partners din shi. Duk inda suka gifta sai kaji ana cewa nice couples, har table din su Umma ya isa tare da gabatar da ita.

   Komawa gefe yana kallon yan uwan Baban shi, dan haka ya shiga gaya mata magana tana Murmushi,  kallon shi Hajiya Humaidah tayi cikin bakin ciki. Kallon Mimih tayi tare da mata alama da ido ta tafi can. Daukar glass cup tayi da ruwan juice. Lokacin yana tambayar ta akan karatun ta, aikuwa a take da yaji inda yayi karatun ya shiga bata labarin yadda zata girma da ilimin ta ta gina karatun ta da kasuwancin.

   Taji dadi sosai kuwa tare da mishi godiya, ta ce mishi.
“Amma ina son na zama Bussiness partner É—inka tukun kafin na zama na gina nawa na kaina. Kome ka gani?”
“Kin kawo shawara me kyau” suna  cikin hiran ya hango Mimih da ganin yadda  take tawowa yasa shi fahimtar da wani kudirin a ranta, dan haka ya janyo Jamilah daya barin, kamar yadda yayi tunani kuwa tana zuwa ya watsa mishi a jikin shi. Kura mata ido yayi.
“Oh…oh…oh… Oppa kayi hakuri wallahi ban san kai na samu ba”
“Mr Jikamshi! Sannun muje restroom ka gyara jikinka.” Haka ya bi jamilah har ban dakin maza, ya gyara jikin shi tana tsaye. har aka tashi wurin bikin suna manne da juna, koda zasu rabu karban number ta yayi, ya kaita har gida. Sannan suka yi sallama.

   Faisal kuwa tsakanin shi da Allah ya dauke matar shi zuwa gidan shi ɗan yasan Ummin ba zata bashi Rahmah cikin sauki ba, dan haka yana kaita bai tsaya wata wata ba, ya kira Bilal da Aaman ya ce musu.
“Karku ce zaku nime, ni dai na dauki mata na, na kawo kaina tunda akan kawo min mata na, uwar me zan jira?” Dake conference call ne sai cewa suka yi.
“Kar ka manta da kazar amarci da kuma sallah nafillah da ake kar a je mata kai tsaye” inji Aaman.
“Na yarda na amince na wuce layin gwauraye da tuzurai”

Ya fada yana musu dariya shu’uman ci.

   Haka suka shiga da ita cikin gidan, ya kai ta wani daki na musamman,da ya tanada. Sun kasance cikin farin ciki, sannan ya fita ya shigo mata da manyan laida ya shigo da shi.  Nan ya saka ta a gaba sai da ta ci ta koshi. Suka ga brush sannan ya umarce ta tayi alola suka gabatar da sallah nafillah, kafin ya kama kanta tare da mata addu’a.

     A hankali ya janyo ta a jikin shi, tare da bata labari tun tana nokewa har ta hakura, domin baki daya a tsorace take, ganin haka ya share tare da danne kwadayin shi, suka kwanta tana jikin shi.

  **
Baki daya Hankalin Jamilah ya tafi akan Bilal, iskancin da take yanxun ta rage, sai ma kokarin ganin ta shiga harkan kasuwanci.

     Da wannan burin ta kwanta tare da jin kamar ta samu Jikamshi baki daya.
….

Washi gari haka suka yi ta kiran Faisal dakyar ya tawo suka tafi gaisuwar iyaye, tare da jin dadi kamar me, amma shi kan gogan sai wani kallon agogo yake, da gayya da suka zo gidan Ammyn Aaman ya ki su tafi. Yau ne Ammyn ta ga Bilal shima kuma ya ga Ammyn,a wurin yaji wani irin giramta da kunyarta sun cika mishi zuciya da idanun shi.har suka bar gidan ya kalli Faisal.
“Mamar su tana da wani irin nutsuwa kamar ba ita ta haife su ba”
“Ni zan baka labarin nan tunda da kyar ta bani auren Rahmah”suka kwashe da dariya.
“Muryan ta yayi min kama da na wata na. Ashe Jamilah ce”

A haka suka ajiye zancen.
Malam Ango yana isa gida tun a falo ta fara watsi da kayan shi domin yana jin Ummin tana balbale shi da masifa ya rike Rahmah.

Yana shiga dakin ya samu tana sallah isha,ban daki ya shiga yayi wanka ya fito daura da towel, dake yayi Sallah a can gida bai bi ta kanta ba, ya cire kayan shi, tana addu’a ta ga zai sake towel din…..
 

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button