NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Inji wasilah, da take share kwalla.  Kallon Rahmah yayi tare da cewa.
“Rahmah!” A firgice ta kalle shi, da gani kasan tana cikin kunci.
“Ya dai?” Ya kuma tambayar ta,
Mikewa tayi ta dauko mishi hular Baba Haliru ta ajiye mishi. Amma bakinta ya gaza furta koda kalma daya ne, a kuntacce take kallon shi.

Mikewa yayi tare da kwantar da Rabi’ah sannan ya fita daga dakin.

Abinda ya faru kuwa,
Flashing back.

Yadda ake ruwan hankalin Rabi’atu yana waje, so take ta fita tayi wasa da ruwan, dan haka tayi ta matsowa daga dakin sai tayi kamar zata fito waje, Wasilah ya janyo ta dakin tana zungure mata goshi.

“Ke kam da maganar ruwa sai kace Yar ruwa, ki jira Yaya yanzu zata zo.” Bata rai tayi tare da tura baki tana kallon waje, har wani hadiye yawun ta take, domin tana son wasa da ruwa,  iska ne ya d’aga labulen taga wulgawan mutum dakin su, tunda ta shiga bata ga Fitowar Yaya Jamilah ba, ganin hankalin su Wasilah ya tafi ga hiran da suke, yasata fitowa daga cikin dakin, ta nufi kofar su.

Tana zuwa ta tura kofar taji a rufe, shine ta koma ta dauko turmi ta hau tare da leka window dakin, idanun ta ya sauka a lokacin da yake shiga jikin Jamilah, kura musu ido tayi tare da jin kamar an buga mata guduma a kanta, cikin kuka Jamilah tace mishi.
“Baba don Allah ka bari da ciwo fa, wayyo Allah na, Wayyo Amminahhhhh don Allah ki bari da zafi bana son haka, ka cire min a jikina.” Ta fada cikin shashekar kuka, tana ture shi, shake wuyarta yayi tare da matseta da karfin tsiya, tun tana shure shure, har ya ga ta daina.

    “Ahh!” Jan Zuciyar da Rabi’ah tayi kenan, tare da sauka a turmin ta koma gefe ta k’amk’ame jikinta. Zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri, kome ya tattaru ya kulle mata kai, idanunta ya gaza daina ganin wannan mummunar al’amarin, wayyo Allah. Tana zaune a wurin yazo zai fita ta ganta. Tsayawa yayi tare da kamo kunnenta, ya murde sannan ya kai kanta jikin shi daidai gaban shi, ya daura akan ta a wurin.
“Shegiya saura ke, ina jiran ki kosa. Na kare dake.”.yana gama fadar haka ya had’a mata kai da bango yayi tafiyar shi, zunzurutun tsoro yasa ko kuka bata yi ba, bata san ta inda ma ta fita ba, tasan dai taji diran shi.

Wannan ne abinda ya faru.

Washi gari

Liman ne ya fadawa mutane abinda ya faru, a take wasu a wurin suka kadda baki suka ce.
“Ai babu wanda ya aikata haka sama da Haliru, domin kowa yasan halin shi.”
“Baku da shaida, karku zarge shi mana haramun ne” inji Liman,
“Baba an samu hular shia cikin dakin su, kuma a yadda muka kwana jiya Rabi’atu tana ihu sunan shi take kira,  Baba idan baka yarda ba ga hular shi a dakin ya bari, kuma Rahmah ta bani. Idan baka manta ba farkon rasuwar marigayi abinda ya faru ba kowa bane shine, domin ina da kwararran hujjar da za a kama”

“Toh amma musulunci tana bukatar shedu hudu ne, wanda suka gan shi. Dan haka idan muka kama shi yana da hujjar…”

“Assalamu alaikum, jama’a kafin wannan abin wata hudu baya na tab’a  ceton ta a hannun shi ya jata zuwa lambu ta gudu, har na mishi kashedi, ko ku baku dauki mata ki ba, Mahaifina da ya turo ni na kula da su, zai iso nan da sati Daya dan baya gari ne, amma tabbas zan hukunta shi da laifin da ya aikata.” Shiru masallacin yayi, dole Liman ya tura sakon shi zuwa ga mai gari.

  “Bayan sun bar masallacin suka nufi asibitin baki daya dattawan jikin su a mace, sabida yadda suka ga Ammih ta karÉ“e su.
“Ya jikinta Maman Jamilah?”
“Malam Liman da sauki zamu ce kenan”
“Allah ya bata lafiya”
“Amin Ya Allah” daga haka bata kuma magana ba, har suka mata sallama zasu tafi anan ne suka ce mata.
“Inshallah zamu kama wanda yayi wannan aika aikan”

    “Hmm” ta ce tare da goge kwallar da ya xubo mata. Haka suka tafi suka barta. Cikin madaukakin zulumi da damuwa,  me yasa? Me yasa sai Jamilah? Anya an musu adalci kuwa? Wadannan sune abubuwan da suke zuwa ranta, kuma har ila yau bata daina jin zafin abun ba, iya kwalla kawai yake zuba amma zuciyarta kamar ta cire a kirjin ta.

**
Karfe tara Na safe Baba Haliru yaki zuwa ko ina, domin yaji labarin abinda ya faru a bakin Buhari, dazun nan da ya dawo masallaci yake fada.. shiga dakin Sabuwa tayi tana kallon shi.

“Wallahi kayi asara, duk mutumin da zai bi dan dan uwan shi ciki daya asararre ne,  anya kai mutum ne?  Lallai sai yanzu na  fahimtar cewa rijiya ta badda ruwa guga ya hana. Allah ya tozarta rayuwarka kamar yadda ka tozarta na wani, wanin ma É—an uwan ka, Allah sarki bad’i ba rai.  Sai ka gani a cikin rayuwar ka, domin nayi kuskure daya tak!”

   Daga haka  ta fita daga dakin tana kuka,  shigowar Buhari da gudu yana faɗin.
“Baban Mu wallahi ga yan sanda nan sun zo kama ka, tunda ka tab’a abinda zai dame ka.”. Bai gama  kai aya ba, Aaman ya shigo cikin gidan, da sallama.
“Kai ka kira min Tsohon banzan ka, muna jiran shi.” Fitowa yayi yana kallon Aaman.
“Akan wani dalili zaku shigo min gidana babu sallama?” Takowa gaban Baba Haliru yayi, ya zuba mishi ido. Kafin ya riko kwalar rigar shi ya watsa shi waje, su kuma yan sanda suna saka shi cikin motar yan sanda, suka tafi da shi.

Dake ba wani Babban gari bane a hankali maganar ya shiga yawo, gidajen mutane, har makaranta. Wasilah ce ta fara kokarin ganin ta fara zuwa makarantar, karshe zuwanta daya bata kuma zuwa ba domin nunawa ake kamar ita ce abin ya faru da ita,  ita kam Rahmah tana tare da Rabi’ah babu halin ta fita domin yarinyar ta shiga mugun tsoro da firgici, wanda ya haifar mata da rashin son magana ko a barta ita É—aya a wuri guda.

  ..
A asibitin kuwa sai da suka kwashe kwana huɗu cur, kafin Jamilah ta farka da wani irin mugun yanayi, domin bata kaunar wani yazo kusa da ita, sai Ammih kana fara kokarin haka toh abinda zai faru zata shiga ihu kafin wani lokaci ta suma,  idan kuma Ammih ne sai dai tayi ta gyara rigarta tana makurewa wuri guda, kamar mahaukaciya, kanta a sunkuye bata son a mata magana. Wannan abin yayiwa Aaman da Ammih ciwo domin tayi kuka da dukkan zuciyarta, tayi a hankali tayi da karfi, har sai da tace ina ma da mutuwa tayi da ganin wannan ranar.  Su kan su Doctors din asibitin kamar ba su aiki, domin baki daya kan su ya tsaya cak, dole suka kira Ammih da Aaman.

“Magana na gaskiyar da zamu gaya muku, shine tana fama da matsanancin tsoro da firgici, wanda ha haifar mata raunin tunanin ta, a koda yaushe zata na ganin kamar wani zai iya cutar da ita, ba iya haka ba kowa ma kallon wancan fuskar zata na mishi, tsoro da tashin hankali zai ta tana ganin kowa kamar dodo ne, domin yadda ka kusance ta yasa mata tashin hankali, dan haka zamu baku shawara ku nimo iyayenta a bata wani na kusa da ita wanda zai na kula da ita. Haka zai iya taimaka wurin dawowa hankalin ta. Da samun lafiyarta, mu namu bata magani ne da kula da ita, sauran kuma naku ne a samu me É—ebe mata kewa yadda zai cire mata tsoron kome a ranta.  Domin matsalar da aka samu kenan akan matan da aka musu fyade, toh kuma gashi kai ba fyade bane matar ka ce kaje mata da karfi.”

Wani irin rintsa idanun yayi tare da jin dole yau ya ci Uban Baba Haliru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button