NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

       “Yanzu kama nufin duk abinda yake faruwa a shirye yake kenan?” Inji Steven ya tambayi Irfan.
“Hatta dawowar ka akan case din Jamilah. Kayi kokarin durkusar da kamfanin JF Group, daga nan ne zaka fahimci an jima ana yaki a gidan ka da wajen gidan ka”

Murmushi Bilal yayi kafin ya ce.
“Kawai ban yarda ba akan abinda ke fada dan gane da Hajiya Shuwa,idan har mahaifin ka aka kashe ba zaka zauna kana kare ba haka ba”

“Kana da hujjar ka na zuba musu ido lokacin da kasan sune suke da hannu  kashe mahaifinka me yasa ka kyale su?” Shima Irfan ya tambaye Bilal.

“Sabida bani da hujja ne?” Ya fada yana kallon shi.
“Kana da hujja, kawai kyale su kayi ko? Ok while time kome zai bayyana” ya fada tare da mikewa zai fita.

“Bayan sun waye kake da yakinin yana cikin al’amarin?” Bilal ya tambayi Irfan.
“Adamu Abbas Jikamshi shine me ruwa da tsaki find out in your memory!”

    Fita yayi daga wurin cikin yana jin saukar abu a cikin ran shi domin baki daya nauyin da yake jin na tsawon shekaru ya sauka.
“Alhamdulillahi” ya fada bayan ya shiga cikin motar. Ya tadda ita,

..
“Mr Jikamshi, Family dinka bala’i ne, ban taba ganin masu matuÆ™ar tashin hankali Meye zaka yi yanzun nan?” Murmushi yayi tare da cewa.
“Toh meye zan musu? Naga dai ba wani abun tashin hankali bane”
“Kai!!! Babban tashin hankali ma ba zan iya jure hakan ba Wani irin taimakon xan maka?”

“Zaka min aikin amma ba yanzu ba, aikin da zaka min yana bukatar nazari sosai, sannan yana da kyau ka fara zuwa kaga mahaifiyarka…
3/13/22, 18:05 – My Mtn Number: 77

😭Ba zaka gane kai ba kowa bane sai ranar da Allah ya had’aka da rashin Darajar network ya nuna maka dan kana da data ba zai hana shi zabga maka rashin mutunci ba i feel bad 😭

Kuri yayi yana kallon Bilal, yana mamakin halin Bilal, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya gyara zama.
“Toh Mr Jikamshi, sai dai Matsalar bana son yadda.”
“Ba zata yi ba, domin tayi kewar ka, burin ta ta ganka burin ta tayi ido biyu da kai,bana jin zata iya juya bayanta dukda kayi mata laifi na tafiya kabarta har na shekaru.”

Shiru ne ya ratsa tsakanin su, kowa da abinda yake ji a ran shi, mikewa Steven yayi kafin ya ce mishi.
“Nagode sosai zan je na ganta, ka koya min wani abu da ban san ina da shi ba ko zan iya shi shine kawazuci, lokacin da Mama ta sayar da Rabi’ah nayi bakin cikin sosai, amma sai nake ganin idan na bar kasar ban nime ta ba, zata fahimci halin da nake ciki. Mr Jikamshi har inda nake tazo, amma baki kulata, domin tayi mugun kuskure wato ita ce uwa kuma ita ta haifi nata Yaran bai zama dole ta martaba na wani ba, Sai da nayi wata biyar ina jinyar zuciyata,.idan da ta ce bata son na tafi da Rabi’ah xan yarda har na hakura”

“Ba zaka yarda ba, ita kuma tana son ka, ba zata iya hakuri ta ga ka tafi da Yarinyar ba, bayan tasan idan ka tafi bai zama dole ko juyo akan lokaci ba. Wani lokaci iyayen mu suna da gajeran tunani, da a lokacin ka yi tunanin ai Mama shirya mu tafi Kema ba zata ji Haushin Rabi’ah ba,. Iyayen mu suna son mu nuna kulawar mu akan su, su kuma sai su koma kamar sune Yaran mu. Kamar yadda suka yi renan mu haka suke komawa muma sai muyi renan su.

       Duk girman mace, idan da zaka ajiye mata dan shekaru goma sha takwas wallahi shi ,zai gyara mata wani kuskureta, iyayen mu mata ka bar su a inda ja gan su, da yau zata ga wani da wani abu. Da zaka leka zuciyar ta zaka ga tana Addu’a Allah kasa wane shima ya isa kamar yadda wane ya isa, Iyayen mu suna mana wani irin soyayyar da basu iya wa kansu.  Matsalar da ake samu su din basu iya dauke kai daga wasu abubuwan da suke gani, kuma abinda tayi shine dai-dai jin ka da ka tafi da Rabi’ah a lokacin ba zaka kuma dawowa ta dadi ba, ita kuma tana ganin haka shine alkhairi gwara ta sayar da ita ta huta, wallahi ka godewa Allah da ba ba mutuwa tayi ba raba tsakanin ku kawai tayi, amma kayi fushi har haka, ina kuma ita tace zata yi fushi da kai kaga rigar jikin ka? Toh sai ya fi karfin ka, kai Malam iyaye ba abin yarwa bane karka yarda ka yi fushi da su domin kai lahiran ma.ba kyau zata maka ba balle kuma duniyar please ka koma gare ta, tana bukatar ka a halin yanzu domin Allah ka dai yasan adadin damuwar da ta shiga, Allah ka dai yasan yawan kukan da tayi, shin kai kana son Yaranka su maka haka?  Idan har kana son jin dadi toh yana da kyau ja kyautatta mu’amalar ka da Mahaifiyar ka kai ko tausayi bata baka, heartless man kawai”

  
    Kallon Bilal yayi kafin ya ce mishi.
“Kai wani irin mutum ne da kake da kirki haka?” Wani kallon banza Bilal yayi mishi a ran shi yake faÉ—in.
Banza dole kaga kirkina abinda kake hari nake son mallakewa

“Nagode sosai, amma haka ba zai saka na bar maka Rabi’ah ba dan hakan kowa ya nemi soyayyar ta amma ba zan bar maka ita ba” ya fada yana tattara wayar shi ya bar shagon.
Har zai tafi sai ya dawo. Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Baka ce kome ba”
“Me zance wa Mahaukaci irin ka bayan Mahaifiyarta ta bani ita, kuma itama tasan da haka!”

“Ikon Allah kace Hauka nake kawai, toh kayi kokarin cafke zuciyarta” ya fada bayan ya juya zai fita.
“Yaushe zamu kuma haduwa?”
“Eh toh zan tafi Korea gobe inshallah”
“Toh zan zo can. Idan na gama da kome na nan”

    “Allah ya nufa”
“Ameen” inji Steven,
Cikin d’aga murya Bilal ya ce mishi.
“Karka manta bible da Alqur’an sun yi magana akan hakkin Iyaye da kuma hakkin uwa da kan ta, karka manta ka roki yafiyarta”

“Nagode”

Murmushi Bilal yayi tare da saka yatsu biyu a goshinsa,  murmushi Steven yayi. Shima yayi mishi haka.

        Mikewa Bilal yayi sannan ya kira Thomas, suka yi magana kafin ya fita daga shagon. Hango Alhaji Abubakar yayi daga can nesa suna magana da wasu mutane,. Wucewa yayi wurin motar shi ya shiga, tare da kallon su ta Madubi kafin ya tadda motar shi.

         Bayan ya isa gida, wayar shi ya kalla rabon da yayi magana da Khalil, dan haka ya shiga cikin gidan, ya rufe kofar shi, dakin shi ya shiga tare da kunna wuta, Khalil ne zaune a saman kujera. Cire kaya Bilal yayi ya rage basu boxes din shi, sannan ya wuce ban daki yayi wanka ya fito ya shimfida abin sallah ya gabatar da sallah. Sai da yayi azkar sannan ya kura mishi ido.

    “Zan tafi Korea na Barka babu ruwa babu abinci kuma ban san ranar da zan dawo ba. Kenan anan zaka mutu” Bilal ya gaya mishi.

Girgiza kai yake da sauri da sauri, hawaye na zuba mishi ya fara kokarin magana. Bude mishi baki Bilal yayi, ya koma kan abin sallah ya dauki qur’ani yana karantawa, ya jima yana karatu, yana rufe shi ya kalli Khalil.
“Me ka ce?”
“Hajiya Shuwa ta sani aikin saka ido a kan ka. Ita ta sani mu had’a maka yadda za a rusa kamfanin ka, Bilal nasan na ci Amanar ka amma don Allah kayi min rai, karka kashe ni”

   “Akan me zan kashe ka, bayan hatsarin da muka yi da saka hannun ka ko ance maka ban san kai ne ka ture mu ba?” Cikin wani irin kuka ya juyar da kan shi ya ce mishi.
“Eh Bilal ni ne, sai dai bani da zabi ne, idan na Barka a raye zasu iya kashe shi Ni”
“Ni kuma an ce maka dan tsako ne da zaja kashe ni kamar yadda kayi fata, kasan yadda nake faffutukar rayuwa,. Kasan yadda nake niman hanyar da zan rufawa kaina asiri Khalil da kai ake kokarin kashe ni! Khalil abin haushi har da Mahaifiyar ta baka kyale ta ba, Khalil me yasa baka dauki fansa ka akai na ba? Amma ka tsaya sai da ka hada da wanda bai ji ba bai gani ba, haka yayi maka kyau dan haka zan kyale ka amma ka nime maboya domin suma ba zasu kyale ka ba, ni kuma ba zan kashe ka ba zan Barka ka rayu domin ka zama shaida na gaba da zai kare ahalina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button