NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

     Sannan yar kungiyar kare hakkin dan Adam,na kasa baki daya.
“Idan muka ce zamu yi fada muna da karfi ne bari na tuntube Mataimakin IG muji?” Kiran Aaman tai, ta gaya mishi,shi kuma ya kira Kwamishinan yan sandan Jahar Bauchi,daga can aka kira na station din da aka turo su, kafin awa uku. Mataimakin IG ya iso Jama’are, a ranar suka bar Jama’are,domin case din daga Lagos ne.

    Lokacin da suka iso,abin mamaki har an shigar da karan Jamilah a bisa tuhumar ta da laifin kisan kai,. Kuma wallahi sun mata mugun da baibaiyi.  Akan lokaci ya kira Bilal ya gaya mishi, shi kuma yayi amfani da irin nashi kwarewar ya kira manyan yan majalisun da ya basu gudummawar shi  lokacin Zabe, tare da mai girma gwamna da wasu Manyan jam’iyyun siyasar kasar nan da suke tare da shi idan zasu yi wani sabgar suke shiga jikin shi, tuni ya aika musu da maganar Jamilah.

Sanin cewa idan har suka rasa tallafin shi akwai abu a kasa, suka sami shugaban kasa da maganar, take aka mai da case din wani iri, tare da fitar da abinda Hanan take aikatawa, dama akwai case din a gaban Yan majalisu,. Shima Shugaban kasa yasan da zancen,. Kawai sai aka kuma juya case din wata fuska na daban,  inda kowa ya fara zare hannun shi, sabida akwai manyan mutane a cikin hidimar Hanan.

   Bilal bai yi kasa a gwiwa ba, ya nufi Russia inda suka yi meeting da manyan su na Korea da nan Russia, suka janye duk wani abun da suke da Nigeria, itama kuma Rasha ta basu goyan bayan haka. Musamman ta aikin tsaron sirri, shugaban kasar Korea ne da kan shi ya kira shugaban kasa ya gaya mishi sun cire hannun su akan kome da suke haddaka. Kuma aka kawo lauyoyin daga Korea su tsare case, ɗin.

  Sai dai me? Lokaci guda aka nemi kashe Lauyoyin, abinda ya fusata Bilal ya saka aka dawo da lauyoyin. Ya dawo gida tare da Rubi cikin dare.

“Kin ce kin san muryan Gayen da ya kai aikin?” Ya tambaye ni.
“Eh na san shi.”

       “Ok” daga haka muka wuce Wurin da Alman yake kai mu hira, muna shiga cikin Club ne na casu, tun daga nesa na hango shi, yana gani na ya fara gudu, saukar kwalbar wine nayi na jefe shi da shi ya bugi keyar shi, faduwa yayi, na bi dan iska na turmushe shi, sannan na ci kwalar shi muka fita, wuka na sauka na shiga yankar fuskar shi ina jin wutar da take ci a zuciyata ba ta gama kasuwa ba.
“Waye ya saka aikin?”
“Mr Khalil da Hanan sai Adamu Abbas Jikamshi sune”
“Ku nawa ne?”
“Mu uku ne?”…….
*Anya jamilah zata tsira?”
3/12/22, 12:24 – My Mtn Number: 75

Jan shi muka yi har cikin motar da muka zo da shi aka saka shi a boot,
“Daga kan shi ba zaki kuma shiga wabi bincike ba”
Ya fada yana zama a cikin motar.
“Akan me? Mahaifiyata suka kashe min,hmm na kyale”

“Eh haka nace”
” Zan kyale su ba”
“Zaki kyale su dan dolen ki”  ya fada tare da mai da hankalin shi kan tukin da yake yi, har muka isa gidan da yake aikin shi. Tunda muka isa ya shiga cikin gidan,  bayan ya dauki Yaron.

Yana ajiye shi ya fito muka tafi, shiru na mishi,tare da dauke kaina.

**
Washi gari.

Da kan shi ya kai ni idan Ya Jamilah take,tayi bakikirin, tsabar wahala. Tunda ta gan mu take kuka, shiru muka yi haka tayi kukan har ya ishe ta, sannan ta bude baki zata yi magana ya ce mata.
“Na rike miki kan maciji domin kuyi  wasa da bindin shi, na baki damar da zaki yi fada domin kanki amma kika watsar da damar ni bance ina son ki ba.

   Ban kuma ce zan aure ki ba, kawai dan fitina kika saka yar uwarki a gaba, kin zata idanun duniya baya kan ki ne? Ai already sun san da abinda kike aikatawa. Tun ba a je ko ina ba, kin dukka kasa ina kuka, wani irin zuciya gare ki? Mahaifiyar ki ma bata huta daga Jidalinki ba? Jamilah ki kwantar da hankalin ki ynzun tunda bukatar ki ya biya Ammyn ta rasu”

“Ya isa haka, bai dace ba ka sakata a gaba kana mata irin wannan maganar ba, bayan kasan halin da take ciki. Babu dan da zai yi farin cikin ganin ganin gawan Iyayen shi ko min munin su kuwa, kawai dai Æ™addara wacce ta riga fata amma babu yadda Ya Jamilah zata so a kashe Ammyn da kuma kai da Faisal. Nasan cewa na hanata abinda take so, amma bana jin zata iya kashe Uwar da ta haife ta. Kafin yau da wa take mu’amala kafin faruwar hatsarin shine tambayar da zaka mata” na saka hannu a cikin wandon jikina, na fita daga cikin office din Yan sandan.

    Kallon ta yayi tare da cewa.
“Kina da goyon bayan ta sosai, waye yake tare da ke kafin faruwar hatsarin?” Kallon shi tayi na wani lokaci kafin ta ce mishi.
“Ina tare da Irfan Kabir Wazir.” Gyada kai yayi tare da kallon ta.
“Kinyi wani abu ne a gaban shi?”  Shiru tayi kanta a kasa kafin ta ce mishi.
“A’a amma yazo maganar kamfanin JF Group ne da aka samu matsalar na’urorin tsaro. Shine Rahmah ta kira ni gasu Ammyn nan zuwa.”

    “Kenan yasan mun fito zamu dawo da Ammyn?”  Ya tambaye ta.
“Eh” ta fada tana jin wani irin kuka na zuwa mata, Sakamakon shigowar wani dan sanda, rike hannun Bilal tayi.
“Don Allah kayi wani abu tun da aka kawo ni yake son yayi min Fyade don Allah ka taimake ni” ta fada cikin shashekar kuka. Kallon dan sanda yayi sannan ya janye hannun shi yana fada mata cewa.
“You deserve a miki fyaden ko zaki kuma hankali,  ke baki da hankali baki daga son kanmu yayi yawa” daga haka ya fita, tare da da kallon Rubi.

Wayar hannun shi ya kira wani dan Jarida, ya mishi bayani abinda yake faruwa. Sannan ya tafi wurin motar shi suka bar office din Yan sanda.

Bayan kamar minti goma, sai ga wasu matasa biyu, sun shigo office din yan sanda, daya yana cewa.
“Ba zan yarda ba wallahi sai ka biya ni kayana babu giyar da ka sha ko kamfanin giyar kasha sai ka biya ni”

“Kai-kai! Lafiya” mutumin yana tangadi, ya ce.
“Wato da na sha kwalba bakwai, na afa kwaya tara.”
“Kai ku kai shi washi cell” haka suka kama shi zuwa Cell lokacin Officer yana kokarin ganin ya keta alfarmarta. Aka wuce da shi, yana jin kukan Jamilah.

    *
Aaman
“Aaman ka bude tv kuma kasa IG ya bude tv” inji Bilal.

“Ok” yana kunnawa kai tsaye aka nuna yadda dan sandan nan yake kokarin yaga rigar Jamilah kuma Live ake dauka, kafin kace me Hukumar Human right sun fara magana, abinda ta cika gidajen tv da radio da kuma kafar sadarwa internet. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba, aka rufe Case dinta bayan an dakatar da dan sanda a aiki baki daya ita kuma aka mai da ita gida sakamakon case din ba za a rufe kai tsaye ba.

**
Kallon Juna suka yi Bilal da Namir.
“Kasan mahaifin ka yana laifi kuma hatta wannan case din da hannun shi a cikin case É—in”
“Eh na sani amma matsalar kana ganin zaka iya rufe shi da hujjar hannun ka? Bayan wanda na baka akwai wani ne?”

    “Eh toh sai dai bani da tabbacin haka zai yiwu, ina son na maida Jamilah da Wasilah korea ne, idan suna nan zasu zama abin hari,dan haka kai ma ka yi nesa sa shi dan ba zan yafewa kaina ba, idan wani abu ta faru da kai”  inji Bilal.

   “Toh Nagode, amma don Allah kar hukuncin yayi tsauri ina son mahaifina” inji Namir,
“Haka ma ba zai faru ba” ya fada bayan ya juya mishi baya.

   ….
A cikin sati biyu kacal suka tattara duk wani shaidu da zai wanke Jamilah, kafin nan basu yarda an yi Shari’a a gaban kotu ba, an yi shine a siritacce, sannan aka wanke Jamilah. Nan da nan aka wanke ta, sannan aka fitar da sanarwar kama Hanan. Yar Duwala, Adizah, Na maroko. A cikin awa ashirin da hudu za’a gabatar dasu a gaban Babban kotun Nijeriya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button