NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya fada da wani irin gwarin gwiwa, dariya Yaran suka saka musamman Hannatu.
“Baban Mu kuda baka haram, shi yasa nake niman ruwan zafi, domin tsarkake kanka ba, Allah ya kyauta bamu san wacce irin Æ™addara ce ta saka Innar mu auren ka ba, mutum sai kace tauren” ta fada kasa kasa tana me barin dakin, cike da jin kamar ta shake shi, ba mamaki wata ya samu ua lalata mata rayuwa.

      Haka suka watse a dakin cikin jin haushin shi sa.

A asibiti kuwa daga Aaman har Ammih kamar ka tsaga kirjin su, kaga irin tashin hankalin da suke ciki. suba zaune har kusan karfe goma na dare, dan ma asibitin kudi ne, babu laifi likitan daga Yan lema yake zuwa, suna zaune ya fito tare da nurse biyu,  ana turo Jamilah akan gadon.marasa lafiya, tayi wani irin rama kamar wacce ta jima tana jinya.

“Dr ya ake ciki?”
“Alhamdulillahi, kai ne mijinta?” Kallon Ammih yayi tare da kallon Jamilah da za a wuce da ita.
“Eh nine mijinta!”
“Ok Babu damuwa, wannan Mamarta ce?” Kallon Ammih da take kallon Aaman cikin mamaki yayi.
“A’a Mamata ce,”
“Gaskiya karka kuma kusantar da karfi, domin zai iya tab’a maranta, ka gane tayi kankanta da bukatar ka, please ka dan d’aga mata kafa, domin idan a asibitin gwamnati ne zai iya zama case din fyade ne.”

Cikin rawan jiki ya amsa,  tafiya office din Likitan suka nufa. Ammih tana bin su da ido, har suka shige sannan ta bi dakin da aka kwantar da Jamilah. Tsayawa tayi a  kofar dakin tana jin kuka yana zuwa mata, waye yayi musu wannan zalincin? Meye tayi da zafi da za a sauke shi a akan Jamilah, yarinyar da ko hararanta kayi a take zata rude, zubewa tayi a kasa tana kuka kamar wacce aka aiko mata da sakon mutuwarta.  A sanyayye ta shigo dakin ya same ta tana kuka, kasa tsayuwa yayi ya fita daga cikin dakin, ya fita waje dafe goshin sa yayi yana jin kamar zuciyar shi zata fita.

    Shafa Aljuhun wandon shi yayi yaji babu wayar shi, dole ya Koma dakin ya samu har lokacin kuka take, bai san yadda zai dakatar da ita ba, dan haka ya juya abin shi bai kuma waiwayawa ba, domin baya son taga hawayen da yake zuba mishi. Bai san lokacin da ya fada ba, sai dai zai iya cewa halayyar yarinyar, dabi’unta, nutsuwarta da kamalarta ya fisgo shi gareta, baya jin akwai wata magana sa ta tab’a had’a shi da ita,  sau daya tayi magana da ita, wanda zai iya cewa tambayar ta yayi a lokacin. Daga wannan lokacin bai kuma  mata magana ba, dan ya fahimci tsoron shi take.

A kwai lokacin da suka makara, aka fara zane kannenta, tsabar tsoro sai Rahmah ne ta amshi dukarta, domin Masifar tsoron duka ne da ita, tun daga ranar yayi magana a cikin ajin su, inda ya ce musu.
“Duk wacce tasan tana jin tsoron duka kuma tana lati toh ta daina idan ba haka ba, da kaina zan zane mutum.”

Ai kuwa tun daga ranar bata kuma yarda sun makara ba, bakwai da Arba’in a cikin makarantar yake, zama yayi tare da kifa kan shi a saman sitiyerin motar, yana jin babu dad’i. Dakyar ya ja motar,.ya nufi gida.

      ..
Asibitin kuwa kamar yadda Ammih ta ga rana haka ta ga dare, domin kasa barci tayi, a hankali ta shiga ban daki tayi alola, ta fito ta shimfida dan kwalinta. Ta fara sallah tana kuka tana sallah, Sabida ciwon abinda aka mata. Haka ta idar sannan ta koma gaban Jamilah ta zauna tana kallon yadda Allah yake ikon shi, bata san wacce irin rayuwa yarinyar zata yi ba nan gaba, Allah yasa kar abun da ya faru ya shafi rayuwar ta, tsoro take ji kar wani abu ya taba rayuwar ta.

A can gidan kuwa sai da Ya fara zuwa gidan su yayi Sallah sannan ya dauki bargo da babban flask wanda Sadam ta cika da ruwan zafi, ya nufi gidan su Jamilah, sai da ya fara zuwa gidan ya ga halin da suke ciki, sannan ya ce musu.
“Ku kula da kanku, Insha Allah zata ji sauki”

“Malam Aaman ashe abinda ya faru kenan?” Inji Ammar da ya fito daga dakin su.
“Eh wallahi, abu babu dad’i zan kai musu abubuwan bukata ne, kafin Zuwa gobe muga yadda jikin yaÆ™e?”

Ya fada yana mikawa Ammar hannu.
“Toh Allah ya bata lafiya, amma ya kamata a kama wanda yayi wannan abun”
“Eh toh sai  yadda ta yiwu kawai, Rahmah ki kula da kannen ki”
“Inshallah” ta fada muryanta yana rawa.
“Ya Aaman Rabi’atu bata magana da, sai razana take”
Kallon su yayi sannan ya ce musu.
“Yanzun abinda za ayi ki kula da su, zuwa gobe kin ji, kita mata addu’oi, kin ji bari na kai musu kayan.” Haka ya musu sai da safe ya bar gidan, ya nufi asibitin. Yana zuwa ya ajiye mata kayan har lokacin bata daina kuka ba, irin me ban tausayi nan, wanda kana gani zaka fahimci na zunzurutun bakin ciki ne da damuwa, da yayi mata yawa, kuma gwara ta fesar da kukan domin idan ya bar shi zai hanata barci, kuma an yi ba a yi ba kenan.

     Ajiye mata kayan yayi tare da shimfida abin sallah, ya ce mata.
“Ammih ki daina kuka! Ga shi ko zaki sha ruwan zafi ne?” Girgiza kai tayi tana kallon shi.
“Me yasa akayi karya? Bayan tsakanin mu da kai babu kome sai alkhairi?”
“Rayuwarta za a yiwa tabo, idan ban amsa a matsayin mijin ta ba, a hankali haka zai hanata farin ciki, nayi ne dan na boye ciwon, babu dad’i kalmar”

Ayi hakuri dama labarin akan girman Ƙaddara na gina shi, domin ban kawo haka domin ya raunana wasu ba sai dai ya nuna maka giraman kaddaran da yake gaban ka Waama kadrallahu hakk’akadrihi don Allah ku sha ruwan sanyi muna son zama matar NOVEL bamu son kaddaran matar novel Nagode sosai

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny

Na
Mai_Dambu

Fatan Alkhairi gare ku Team din Yaya Haliru😂🤣My Boss ba
Ina mata yan kwalisa ina macen da ta yarda da kan su shin ko kunsan
MAMAN LABIB COLLECTION TAZO MUKU DA TURAREN WUTA MASU KAMSHI DA KAMA WAJE.

kAMAR SU KAJIJI, SANDAL FLAKES, SANDAL BANGE, SUGER CUBE, WHITE SANDAL, HALUT, DORUT, DUKKAN, AKAN FASHI ME SAUKI

Maza garzayo karki bari a baki labari… kayan mu akwai kyau da nagarta ga masu bukata zasu iya tuntubar wannan number sai kun zo👇🏾💃🏼Http://wa.me/+2348144687796

Juyin juya halin <8>

Share kwalla da yake zubo mata tayi, bata kuma Ce mishi kome ba, har ya mike tare da kallon Jamilah, sannan ya fita daga cikin dakin, baki daya ya rasa meke mishi dadi a rayuwar shi, ya yake kamar zuciyar shi zata fita dan haka yana fita daga nan gidan Baba Haliru ya nufa, bubbuga kofar gidan yaso yi amma ya fasa, sannan ga juya tare da barin unguwar.

A gidan kuwa, tunda Malam Aaman ya tafi, suka shiga dakin Ammih suka, kwanta, can sun fara barci Rabi’atu ta danna ihu, tare da kiran sunan Baba Haliru.
“Wayyo Allah na, Wayyo Yaya Jamilah, Baba Haliru karka kashe ta, don Allah kar ka kashe ta, wayyo Allah Wayyo Ammin mu, wayyo Abba mu kazo Baba Haliru zai kashe Yaya Jamilah.” Tana ihu tana fisge fisge, Ammar da matar shi ne suka fito tare da buga kofar dakin, Rahmah kan rike ta ke, amma kukan da take ya ci karfin ta, ihun ne ya tashi Ammar da matar shi suka zo, suka buga kofar dakin.
“Wasilah bude mana kofar?” Ya fada yana bubbuga kofar, da sauri ta bude kofar, ya shigo ya same su a dame, yayi ta tofa mata addu’a, can ta sake wani irin kara me had’e da kuka, kafin ta koma jikin shi tayi luff, tana sauke ajiyar zuciya.
“Meye ya faru?”
“Sunan Baba Haliru take kira tun dazun, tana cewa kar ya kashe Yaya Jamilah.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button