NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

     “Ba wai haka bane dole ta bar miki sarauyin ki amma ai shi bai fadawa duniya soyayya yake da ke ba,  abokiyar kasuwancin shi ya dauke ki. Kuma kowa yaji haka yasan ba soyayya.”
“Ammyn kin fison Rabi’ah dani ne?” Murmushi tayi sannan ta ce mata.
“Yadda na baki farin cikin ko Kannen ki ban basu haka ba, kece Æ™addara ta same ku, su ne suka amshi kaddaran hannu bibbiyu, daga Rahmah har Wasilah babu wacce take abin da kike aikatawa, Rabi’atu kuwa dole na kauna ce ya, sabida kaddaranki ya raba ni da ita, kin ga kenan idan da ita ce va zata yi abinda kike min ba, bawai nace ban amince da alakar ku ba, amma ki sani matukar Bilal ya amince dake babu damuwa.”

“Kawai ki gaya min kin tsane ni” tass Ammyn ta wanke ta da mari.
“Kinsan halin da na shiga kuwa? Kin san bakin cikin da naji kuwa? Akan ki aka kirani kasuwa duk  bai isa ya saki farin cikin ba? Meye nayi miki da na cancanci wulaqantar wa?  Toh wallahi idan kika kuma gaya min haka sai na zare ki a cikin Yarana ki tafi duniya ce ta fi gabaruwa jima” daga haka Ammyn ta bar mata dakin tayi ga abinda ta gadama, dake bata da hankali bata ko yi sallah ba, balle wanka da zata yi. Ta bar gidan ita tayi fushi.

Ammyn bata yi mamaki ba, dan ita Yanxun ta daina jin tashin hankali akan Jamilah sai dai ta bita da fatan shirya.

**
Tunda na dawo ban wani fita ko ina ba, haka muke zaman kurame a gidan sam bana son magana, idan ba ya zama dole ba.

Kwana na biyar da dawowa ne, da a yamma ina zaune, na saka yara a gaba suna min rawa sai dariya nake musu na tashi na ce musu.
“Kunsan rawan Afrika da waist a ke. Dan haka kamar yadda nake haka zaku min” na nutsu ina ta tikar rawa. Ko babu kome ya rage min damuwa.

“Maman Bosai yarinyar nan tana cikin damuwa sosai, duk ta rame” inji daya matar da take kula da kananun Yara,
“Eh Maman Fatrick, kamar damuwar bata da yawa, sai dai bana son alakarta da Hausawa ne, domin basu iya rike aure ba, sannan ba kuma ga tashin hankalin, tausayi take bani.”

Haka suka yi ta tattaunawa, dai suka yi shiru hango Faisal a bakin kofar shiga gidan.

“Kusan bata san yawan Alkhairin wannan yaron ba, tunda bar garin nan har yau bai daina mana alkhairi ba.” Inji Maman  bosai.

    Hango Faisal da yaran sukayi, yasa suka watse, tare da nufar shi inda yake rike da manyan ledoji, juyawa nayi ina kallon shi.

   Durkusa yayi a gaban su, ya rungume wannan ya sake wannan, karshe Abraham ya goya, suka tafi cikin gidan.
“Uncle Ina ka tafi?”
“Tafi na hau jirgin sama” yayi musu alama da hannun shi ya tashi sama.
“Laa uncle Kai ma kana hawa jirgin ne, Uncle jirgi Kato ne?”
“Katoto ma kuwa!” Ya shiga kokarin sauke Abraham a  gaban su maman bosai.

   “Ina wunin ku” ya gaishe su, sannan ya zauna aka fara hira, kamar bai ganni ba, shiru nayi ina kallon shi, sun jima suna hira, kafin ta rabawa yaran kowa abinda ya aike shi, sannan ya ciro chocolate ya tawo inda nake.
“Gashi na walnut ne, inji NaNa tace kina son shi” hadiye yawun nayi, tare da da cewa.
“Nagode ya Umma da su Seyo Na da NaNa, da Umma din Ha Na?”
“Ban sani ba, ko da zaki tafi kin gaya musu ne zaki tawo?”
“Hmm… Hmm dama… Dama”
“Look rayuwar ki ne, amma ki yi kokarin fahimtar mutanen da suke tare da kai ya zasu ji idan ka matsa a jikin su? Musamma’n wanda ya b’ata dogon lokaci yana jure rikicin ka”

“Kayi hakuri, gori suke min kuma idan nayi fada da su, laifina za a gani dan ni mareniya ce. “
“Waye ya ce Miki ke mareniya ce?”Shiru nayi domin ina da magana amma bana son yaga kamar na cika korafi ne.
“Zaki koma aiki daga gobe Insha Allah, ga kayan ki nan bari na shigo Miki da shi”

   Haka ya fita ya shigo min da kayan.
“Inji Wife ta ce kizo mata wuni, tana kewarki”
Share kwalla nayi, tare da kallon.har da wasu kayan da ban san su ba.
“Wancan inji Maman Ha Na,wai na kawo miki wancan kuma inji Umma”

“Nagode sosai”
“Ƙarki damu”
Da haka yayi min sallama, har ya fita ya dawo.
“Ya ce yana gaishe ki sosai” d’ago kai nayi tare da murmushi,  haka kawai nake jin kamar na samu kwarin gwiwa da zan iya komawa aikin.

Ganin Faisal da zuwan shi ya samun karsashi, ban san dalilin haka ba, washi gari na cab’a kwalliya da yar gown dina iya gwiwa ta, na saka wata takalmin moccasins flat shoe, sai yar Æ™aramar miniaudiere bag itama purse ce me shegen kyau, cream colour.

     Sai gashina da na gyara tare da tufke shi, a keyata na dauko janar da nake da yakinin turare ne, na bude Murmushi nayi dan na tuna lokacin da muka shiga mall din shi na ga jakar sit ne na turaruka, na kalli NaNa nace mata.
“Wannan kuma meye haka?” Dariya tayi sannan ta ce min.
“Turaruka ne na zamani haka yake zuwa mix maza da mata, amma ma’aurata sun fi saya.”

“Gaskiya yayi min kyau, kuma ina son shi”
“Toh ai baki da aure” tura baki nayi ina faÉ—in.
“Ai gaskiya nima aure zan yi”
“Toh duk saboda turare”
“Ina son kamshi” duk Umma tana jin mu, har muka koma gida maganar turaren nake.  Kwalla ne ya cika min Idanu sannan na fesa, kafin na mike ba gyara dakin. Na fito.

“Mama zan tafi aiki”
“Allah ya kare ki, ya baki sa’a”
“Ameen” na fada sannan na fito.
Toyota na gani, a kofar gidan mu. Dauke kai nayi zan wuce sai ga shi an bude motar.
“Ayola” na kira sunan shi.
“Rubih yar albarka, ai duk sanadin ne na samu motar wai inji wannan hausa Man din ina kai ki office din ku”
“Kai haba! Toh” bude motar nayi na shiga ina mamaki, gaba na shiga ban shiga baya ba, ya ja mu.

**
Faisal
A hankali yake sarrafata cikin tsannanin tausayinta, domin cikin ta ya girma, dan haka yake Bin ta a hankali, kamar kwai. Sai da ya kama aikin gaskiya ne ya kasa mata uzuri baki daya,.kamar ya cinye ta haka yake ji, dan dai sabida cikin jikin ta ne, yasa yake rage yawan abubuwan shi amma baki daya cikin ya kara mata wani al’amari na musamman, sai da ya gurzata son ran shi, sannan ya kyale ta. yana mai da numfashi. Itama tayi wani irin laushi. Janyo ta yai jikin shi.  Yana shafa bayan ta, sai ajiyar zuciya take, a hankali barci ya dauke ta, manna mata peck yayi a goshi sannan ya tashi ya shiga ban daki yayi wanka sannan ya fito ya shirya. Breakfast ya tab’a a gurguje ya fita.

      Bayan tafiyar shi kiran wayarta yasa ta farka dauka tayi.
“Hello Silah!”
“Kin samu labarin Jamilah bata gida? Tunda kuka dawo” tsaki tayi tare da cewa.
“Ta tayi duk inda ya mata ya Ammyh?”
“Tana nan dai but bata wani damu sosai ba.”
“Zata damu pretending take”
“Naga alama”
“Zan shigo an jima. A dubata” ta fada bayan ta kashe wayar. Tana tsaki ban daki ta nufa, sai da ta tara ruwan zafi sannan ta shiga cikin ta zauna dan har yau bata saba da fitinar Faisal ga…
3/9/22, 16:49 – Nuriyyat: 67

Mun isa Office baki daya ranar na fahimci Mutumin da ya zauna da kowa da zuciya Daya ba zai taba manta alkhairin ka ba, ina shiga office din aka fara ihu.
“Wow ta zama babba Yarinya ku kalli Rubi” kowa so yake ya Kalle ni.

“Ina Mr Jikamshi?”
“Sandar kiwon da kuka bani ya b’ata tare da shi.” Dariya suka saka sannan aka gaisa da juna, ina gamawa da su ba hango Yallabai Faisal. Wurin shi naje nace mishi.
“Good morning Sir”
“Morning Rubi, kin yi kyau sai kika kara fitowa sak mata ta” dariya nayi tare da bin shi muka nufi sabon labari office din da aka bani, nuna min kome yayi, sannan muka nufi babban department din su na Computer.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button