NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

        Har sun wuce, ya ce Faisal.
“Yarinyar nan tana mana shigar rashin mutunci ka mata magana.”
“Ina ruwanka? Kayi sha’anin gaban ka” kwafa yayi yana hararan Faisal.

  Wajen karfe biyu ina cikin aiki a babban office din department din mu, hankalina ya kai kan shi na Kira Bola ina mishi bayani,  kamar zai shige jikina. Sai jin shi muka yi ya cewa bola.
“Ka Bola same ni a office dina, ke kuma kar na kuma ganin ki anan maza fita” tashi nayi na kashe laptop din.

   Koda suka koma office din shi da Bola.
“Meye yasa haka? Kake shige mata kamar zaka shiga jikinta?”
“Wato yallabai yarinya nan tana zafi ne, kuma a yadda take min magana tafasasshen mutun irina ba zai iya jurewa ba”

   Kallon shi yayi kafin ya mike yana faɗin.
“Haka takewa karanunkan unguwar su, da jakunar unguwar su, infact kowa ma haka take mu’amalar shi, domin baki daya bata dauke su a mutane ba, kar na kuma ganin ka a inda take.”

“Ok Sir” ya fada, tare da sunkuyar sannan ya bar office din. A hankali Bilal ya hana maza kusantar inda Rubi take, sannan ya kasa ya tsare ya hana ta sakat, ga dan banza masifa ita kuwa tayi ta kananun magana. Rumors ne ya shiga cikin mutanen, inda maza ma’aikatan kamfanin suke fadar ai Mr Jikamshi yana son Rubi domin ya hana kowa shige mata, haka maganar tazoe har kunne na. Ranar juma’a, ya shigo kamfanin na tsare shi ina cewa.
“Mr Jikamshi!” Yadda na kira sunan shi ya sa shi tsayawa yana kallona.
“Wasu magana suna yawo a cikin kamfanin nan wai ni da kai mun yi dating juna haka ne? Akwai wata alaÆ™a tsakanina da kai ne?”

Kura mata ido yayi, a karo na farko da ta burge shi.
“Kai ka fito daga most Nobel Family ka gaya musu babu abinda yake faruwa a tsakanin mu” a hankali ya tako gabana.
Kasa yayi da muryan shi sannan ya ce min.
“I like your confidence, Dan haka cigaba ni ban da lokacin ki” ya fada min sannan ya wuce abin shi. Takaici ne ya kama ni, ina ji ina gani ya tafi ya bar ni da kayan haushi. Wucewa wurin Baba Tunde nayi, baki daya suka watse, haka nayi ta bin su suna guduwa.

..
“Khalil kira min yarinyar can” ya fada mishi,
“Ok” fita Yayi.

Ina cikin mita yazo.
“Kizo inji Yallabai”
Zan bashi amsa na hango Alman, kallon Camaren da yake wurin nayi sannan na d’agawa Alman hannun. Isowa yayi wurina.
“Baby zo muje casu” aikuwa na kalli Cameran na mika mishi hannu, muka tafi da sauri.

   … Dafe Kirjin shi yayi yana wani irin hakki. Tun da muka fita ban dawo office din ba. Karfe biyar Alman ya sauke ni a gida, a hankali na juya ina takawa.
“Baby kina da zafi mu hadu wata sati” d’aga mishi hannu nayi,  na bude get  hango shi nayi yana wasa da yara. Sake ware idanuna nayi, sannan na kuma rufe shi.

Saboda yau nayi abinda ya sani jin kuka ya ka mani, hawaye ne ya zubo min, takalmina a hannu, haka na wuce dakina, ina shiga na zube a bakin gadon, ina wani irin kuka,
“I drunk again” na fada cikin shashekar kuka, shigowa yayi tare da kallon yadda nake kuka.
“Ka fita bana son ganin kowa”
Na fada cikin kuka, kallona yayi lokacin da na mike, kallon rigar jikina yayi yadda aninin gaban rigar suka balle.  Har yana hango farin vest din jikina wanda yake hade da pink bra,
Wani irin fisgo ni yayi cikin fusata ya ce min.
“Meye ya faru fitar da Alman?”
Jiri da barci nake ji, a hankali na zube a Kirjin shi ina cewa.
“Ban sani ba” sake d’ago ni yayi cikin fushi ya wanka min mari, sai da na wartsake.
“Me Alman yayi miki?”
“Me yasa kake jin haushi? He touch me” wani irin mari yayi min da ya sani fashewa da kuka, aikuwa take ba fara amai, kuma a jikin shi. Boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, tare da faÉ—in wata kalma.
“Alhamdulillahi, me Alman yayi miki gaya min”
“Barci nake ji” na fada cikin matsanancin kuka,
“Ok”
Kwantar dani yayi tare da kallona. Wayar shi ce tayi kara ya duba hoton videon Alman da Rubi, kallon ta yayi musamman yadda ta fita hayacinta, suna wani shegen romance da kiss kamar zasu cinye kan su, yana ganin lokacin da Alman yake balle botirin rigarta, tare da kai hannun shi tudun kirjinta ya wani damke su. Kashe wayar yayi. Sanan ya fita.
“Thomas ka bibiye layina an turo min wani sako, ka binciko min layin.”
Sai da ya koma cikin gidan yayi musu sallama, sannan ya tsaya a kofar gidan, bayan minti goma sai ga sako. Murmushi yayi tare da tadda motar shi ya nufi unguwar su Ammyn.

    Kiran layin Jamilah yayi, sannan ya jirata da murna ta fito, ya dauke ta suka fita. Sai da suka bar cikin garin lagos ya tsaya.
“Jamilah ni dake nace ina sonki?”
“Me ya kawo wannan maganar?”
“Tambayar ki nake! Na tab’a cewa ina sonki?”
“A’a” ta fada kamar zata yi kuka,
“Meye haka?”
Ya tura mata wayar kan cinyarta,
“Ban gane ba?”
“Zaki gane idan na miki bayani dala-dala ko?”
“Mr Jikamshi!”
“Look ni na taimaka miki ne domin daukar Revenge ban tsaya miki domin na so ki ba, dake me hankali ne da kin manta da waye Alhaji Adamu Abbas Jikamshi! Amma duk damar da na baki bai saka kin san me ke damun ki ba. Aaman Muhammad Lawal Dambatta yana sonki da gaske. Ni ba soyayya nake dake ba, asalima taimakon ki nayi domin ki cimma nasarar abinda aka Miki.  Sannan ai abin kunya ne ace yadda kika yi ruined life É—inki da selfish ni na aure ki? Ke baki san abin kunya bane? Ita wacce yarinyar da kike kokarin cutar da ita din ta bani abubuwa dayawa, dan haka kar na kuma ganin wani abu daga gare ki, kina tafiya da rayuwar ki like Innocent lady, bayan ina sane dake, ko yayya mutum ya rab’e ni ina sane da shi dai dai naki kuka shi dan bana son na katse mishi hanzarin shi. Nasan abinda kema baki sani ba, sannan na san kudin da kike amfani da shi na yan uwanki ne, ba akan ki aka fara samun matsalar rape victims ba, kuma ba za a kare akan ki ba, ita wancan yarinyar da da kike Æ™oÆ™arin karta kusance ni kin san wacece ita?

    Bari na na tuna Miki ranar da da na sa a kamata kina bayana da kanki kika ce. RABI’AH! LITTLE SISTER KO?  Kika sake wani haukarki yasa ta fahimci kina saka mahaifiyarku kuka,  a fusace ta girma. Kuma kome kashin abu daukar shi take babba. Na reneta kamar mayunwaciyar zakanya ce. Idan ba ni ba, kaf duniya ba namijin da ya isa ya tsaya a gaban ta. Ni daya nake da iko da ita idan kuwa nace mata ga abinda kike…. You fi…Ni…sh..ya faÉ—i maganar ararrabe

Flash Back
3/10/22, 08:10 – My Mtn Number: 69

Flash Back

Bilal Ahmad Abbas Jikamshi, jam’i’in tsaron kasar Korea ne, bayan ya  gama karatun shi na siyasa da kasuwanci, kakan shi ya bashi shawara shiga aikin jami’in sirrin Æ™asar korea, kuma sai aka yi dace ya samu goyan bayan kasashen guda biyu Korea da Nigeria sun cimma yarjejeniyar kasuwanci da harkan tsaro,. Babban matsalar da take addabar yankuna kasashen Afrika da yankin Asia itace harkan sarrafa da harkan bakar kasuwa, shine fita da shigar miyagun kwayoyi da manyan makamai, wanda idan haka ta cigaba da da faru toh zai zama tashin hankali ga al’umma.

Wannan yasa shuwagabannin kasashen suka cimma wannan burin na kawo karshen, amma kuma da matukar wahala dole idan kana son samun labarai kamar haka sai an shigar da wasu masu fasa kori a cikin manyan mutanen.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button