NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A gefe guda kuwa wata irin kunyar shi ce ke damuna, dan tun faruwan wancan al’amarin na janye jikina daga gare shi, sai dai kuma haka ba karamin al’amari bane a wurin shi.

Wata Monday tun kafin nazo ake shirin karban wani babban bakon a kamfanin,suka shiga meeting, koda nazo na samu an shiga,. Office dina na wuce.

Tunda na shiga ban fito ba, sai karfe biyu saura, shima sabida hayaniyar mutane ce, ya sani fitowa. Kicibis mukayi da Ya Faisal.

“Karba wannan shi sabon partner ne na Jikamshi Transportation, ki duba kome a computer ki tura mishi.

Bude File din nayi naga sunan da Ba zan tab’a mantawa ba.
STEVEN Uchanna Joshua. Wani irin watsar da File din nayi na fita da mugun gudu.

Daga cikin office din shi yake kallon ta, yadda take ihu da farin ciki, bai tab’a ganinta cikin wannan yanayin kamar yau ba, wani irin bugawa zuciyar shi tayi kamar zata fado kasa, ya kura musu ido, bai tab’a yarda mahaukaciya bace sai yau, yadda ta rungume gayen ji yayi kan shi na masifar sarawa, zubewa yayi a saman kujeran office din yana ji Kamar ya fita yayi ta dukar su, daga ita har Mr Steven Joshua Uchenna. ganin sun fita yasa shi mikewa tare da nufar wurin glass din office din, dake building din office din da glass aka yi, ganin ma a wajen hannun su, sarkafe da juna ne. yaji wani abu ya tsaya mishi a ranshi.

Bai san lokacin da ya dauki wayar shi ba, ya shiga duba sunan ta.
ugly girl fasa kiranta yayi ya kira number, Faisal.
“Me Daraja Yarima Jikamshi?”
wani irin huci yake, zama yayi tare da shafa kan shi.
“Kana ganin abinda yarinyar can take?”
3/11/22, 23:49 – Nuriyyat: 72
“kamar Ya?”
cikin kunar Rai ya ce mishi.
“tambaya ta kake?” ya tambayi Faisal, da karfi dan ranshi ya gama É“aci,
“Allah ya baka hakuri” cikin zafin ya riko kofin glass din da yake table din ya damke da karfi, tsabar ran shi ya b’aci, haka kofin glass din ya shiga tsawa alamar zai fashe cikin zafin zuciya ya ce.
“ka kira min ita”
kit ya kashe wayar shi, daidai rugurhujewar kofin glass din hannun shi.

…..
a waje kuwa cikin farin cikin nake murna, kallon Steven Joshua Uchenna nayi.
“ina Mama? koda yake zan zo” ta fada cikin shashekar kuka,
Takowa yayi tare da zaro hanky ya shiga goge mata fuskar ta, ya ja habbarta.
“karki kuma kuka, Ina nan ne sabida ke.”

“Adawiyya!” da sauri ta juya, daidai lokacin da Yallabai Faisal ya mikawa Me Staven hannu a karo na biyu.
“excuse us, Ana kiranta ne Mr Jikamshi!” cikin wani irin faduwar gaba ta kalle shi.
“ok bari na tafi don Allah ka dawo” ta fada mishi. tare da juyawa cikin kamfanin da sauri, har ta nufi step ta juya zuwa elevator. tabawa tayi yaki budewa, dan haka ta juya step tana hawa da mugun gudu, tare da harhada hanya. duk inda ta tsaya ta rage yawan tafiyar sun kin bude mata dole a hankali ta koma bin step din.

….
Da kan shi ya bada umarnin kar a sake a bari ta hauro ta elevator, kuma duk wanda ya bari haka ya faru sai ya fired din shi. dakyar ta isa office din shi last building, tsayawa tayi a wurin water dispenser ta dina tasha, sannan ta nufi office din shi, buga kofar tayi. aka ki mata magana, sake bugawa tayi Hallo dai haka ce, tsayawa tayi cikin tsananin shakkar shi domin tasan ta karya sharadin da ya gindaya mata.
Bude bakinta tayi tare da cewa.
“Na shiga uku” saka hannunta tayi a jikin handle din kofar, ta tura yana zaune kamar baya jin buga kofar da tayi.
Dan latsin Hammata ta fada a kasar ranta,. a fuskar ta kuwa murmushi take sakewa,
“Assalamu alaikum, Mr Jikamshi”
Ta fada cikin matsanancin tsoro da faduwar gaba, sakamakon yadda hannun shi yake zubda jini. da sauri ta nufe shi.
“karki sake ki tako nan, get out.”
“but kana kana kana zubda…”
“Ai da gaske?Ok zaki fita ko sai na kore ki a Kamfanin?”

“Mr Jikamshi me nayi kuma?” Na tambaye shi kamar zan yi kuka.
Wani irin juyar da kai yayi cikin tashin hankali, kafin ya fada da karfi.
“Ki fita nace” da sauri na fita, har ina kokarin bangaje Ya Faisal.

    “Kayi hakuri” na fada ina kokarin mai da kwallar da take cikin Idanu na.
“Kayi hakuri” ya fada min,
“Babu kome” na fita, da sauri na koma da elevetor, na samu yana yi da sauri na sauka tare da fita daga cikin kamfanin. Motar Steven yana kofar shagon mu.

         Budewa yai yana kallona,  wani irin kuka ne ya zo min, na shiga tare sa daura kaina a kafadar shi.
“Rubi”
“Hmm!”
“Kin haÉ—u da dangin k”
“Hmm” na faÉ—a.
“Kinyi farin ciki?”
“Hm”
“Muje na kai ki gida”
“A’a kawai ka barshi”

     “Toh ina xan kai ki”  ya tambaye ni,
“Me yasa kike kuka?” Girgiza kai nayi tare da cewa.
“Na tsani kaina, Bilal ne kawai a gefena, sauran sun juya min baya.  Na rasa kome da kowa.”

   Shiru yayi yana tuki, kafin ya ce.
“Kiyi hakuri zai wuce” ya cigaba da tukin da yake yi.
**
Bilal.
Dafe yake da Kirjin shi, idanun shi rufe.
“Bilal kayi hakuri. Amma dole ka rage abinda kake mata, yarinya ce har yanzu.”

Shiru yayi yana me kara lumshe idanun shi,
“Zata mutu ne, ita kanta rayuwar ta mutuwa ce, balle kuma ta shiga wancan haramtacciyar gidan,  jami’an tsaron kasa da kasa nimanta suke, idan ina son ta rayu dole mutuwarta ya fito ya zaga duniya”

   “Kamar Ya?” Faisal ya tambaye shi,
“Ita din ta samu horo ne dayawa bayan nan”
“Meye ya faru?” Faisal ya tambaye shi, a matukar firgice, janyo drower din gaban shi yayi ya ciro mishi, File din da Namir ya bashi.

     “Duba ka gani, zaka damu abin dubawa ita kuma Adawiyya ka bar zancen ta zamu yi wani lokaci” ya fada tare da mikewa ya nufi ban daki ya wanke hannun shi, sannan ya saka platies ya fito.
“Ikon Allah amma biri yayi kama da mutum. Yanzun me zaka yi domin naga kome da yake cikin File din ba kamar shi Adawiyya ta bani na tura maka hatta mutuwar Ha Na”

   “Ai matsalar itama Hajiya Shuwa bata san dan ta yana cikin hatsari bari muga wani mataki Jamilah zata dauka domin nayi mamakin shirun ta nan yayi yawa.” Inji Bilal.

   “Zata magantu ai” inji Faisal,

   Abinda yake cikin File din shine tsarin yadda aka kashe Iyayen su,tun daga shirin farko har izuwa yanzun da kashe matan Bilal da ake duk yana cikin file din, shine kuma a cikin Laptop din Khalil, wanda suka yi canji da Bilal. Dan haka wannan shine abinda Rubi ta gani, ya kuma saka son sanin me yasa ake son kashe Bilal. Shi yasa babban makamin da tayi amfani da shi, shine na samun kusanci da Faisal,daga baya ta samu shiga jikin Bilal.

        Ta tura musu kome, sannan ta kara mai da hankali sosai akan suwaye ne, suke bibiyar shi sai dai abin takaici Matar Uban shi ne da wanda bata sani ba, tana kuma kan binciken Jamilah ta shigo da nata matsala.

   **
Gidan su Faisal ya kai ni, dama a can nake da zama, ina shiga na hango Wasilah da Rahmah. Wuce su nayi zan shige É—akina.
“Amma da kin saurare mu”
“Ya Wasilah zan saurare ki, amma ban da macen da bata san darajar auren ta ba”
“Kiyi hakuri Auta” inji Rahmah.
“Meye zan muku?”
“Ammyn tana bukatar ki”
“A’a tana bukata Jamilah dai ko? Ita ta dace tayi farin ciki ba ni ba”
“Auta me yasa kike haka ne?”
“Ya Wasilah! Maza uku aka sa suna bibiyar ki. Ya Rahmah hatta inda kike aiki umarnin ake jira a baki mamaki, na san mutuwa zan yi, duk wanda zai shigo rayuwata shima kashe shi zaa yi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button