WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
    Ban san me yasa na fada wannan yanayin ba, ina so nayi farin ciki. Amma dole sai na hakura da tawa rayuwar ko su cimma ni ko na kashe kaina fa hannuna,. Kuce mata ina son ta.”
  Daga haka na shiga cikin dakin, na rufe kofar ina kuka, tare da jinjina da kofar.
   Abubuwa dayawa da suka faru, ko abinda zai faru nan gaba, A kafadar Rubi a kwai zanen tattoo, ta stamp na safara da aka yi da ita, wannan kuwa ya samu asali ne daga wasu miyagun kungiyar Mafia da take kasar Rome, kuma tana karkashin jagorancin gidan marayun da ta zauna, a ka’idar aikin ta, idan ya gama kashe su ake, sai aka yi dace ita ko an samu labarin mutuwar ta, za aji tana raye saboda wani na’ura da suka saka mata a arm dinta, shi yake nuna duk inda ta shiga.
   Tun barinta office din Yan sanda tane ganin sakon ana ce mata.
Ahalin ki ko Shi Bilal É—in! Ko kuma ki kashe kanki
Wannan sune sakon da kullum take gani ba dare ba rana, ita kanta tasan iya abinda ya dawo da ita komawa gida da kuma Bilal. Kuma gashi nan zata tafi ya barsu.
  **
Surulere.
“Mansurah Abdul, Yarinyar nan tana cikin hatsari, taya aka yi kika ta fada hannun dragon?”
“Sir ba aikin kowa bane sai Hannah, ita É—aya ce ta san Yarinyar tana raye?”
“Meye kike ganin zamu yi?” Shiru Falon yayi.
“Me zai hana a shirya hatsari mana, sannan ba mamaki akwai abinda yasa ake ganin ta.”
  Kurawa Faisal ido yayi, kafin ya ce mishi.
“Taya za ayi hatsarin”
“Ta yadda kullum kake shirya tuggu” ya bashi amsa.
“Zata rayu?”
“Eh TOH abu me muhimmanci, ita ta rayu koma meye”
“Ka shirya kome, idan aka yi hatsarin a fitar da ita sannan a kona motar yadda ko gawar ba za a samu ba”
**
Tun safe da nazo ban fita ba, sai famar aikin tunani nake. Tashi nayi na had’a Coffee na sha, zama nayi kafin na fita kamar an mintseni.
Hango shi nayi shima kuma na tabbatar ya gani,akan Idanu na ya riko hannunta.suka wuce office din shi.
“Mimih” na fada a hankali, sannan na koma office din na zauna ina juya kujeran. Kiran wayar office din yayi na tashi na fita.
“Na shigo?”
“Eh”
Shiga nayi tare da dauke kaina akan su. Sannan na wuce gaban table din na tsaya.
“Gani nan”
“Akwai tafiya da zamu yi zuwa Malaysia, ki duba ga passport É—inki nan.”
“Ok Amma Mr Jikamshi”
“Ok ba zaki ba?”
“Shi kenan”
Na fada mishi tare da, dauka nayi zan bar office din ta ce mishi.
“Oppa kana dawowa za a mana baikon?”
“Eh”
Fita nayi daga sama office din, na sauka kasa, tsabar na rude. Kuka nake ji zafi nake ji, ban sani ba amma kamar zuciya ta zata kama da wuta haka na kasancewa kamar mara gata bana jin dadin rayuwa ta baki É—aya. Fita nayi ina share kwalla, ban san yaushe na fara jin haka ba. Amma tabbas ina jin kuna.
  Haka na isa shagon cikin abincin. Ina shiga na wuce dakin sauya kayan mu, na zauna tare da fashewa da kuka me mugun zafi da kunna Ni daya na san yadda nake ji dan akwai zafi akwai ciwo, dukan inda yake min zafin nake ko zan ji sauki. D’aga kai nayi ina jan numfashi na. Ruwa aka mika min.
“Sometimes muna jin zafi da ciwo, amma bagararwa da nunawa bamu damu ba yana rage mana zafi. Adawi, kina son wani ne?”inji Natasha,
“Natasha shi ya cilla Rayuwata hatsari, na rabu da kowa dan bani da inda xan zauna yau shi da kan shi yake wofantar dani bayan san halin da ga cilla Ni? Me yasa sai ni?…..
Ayi hakuri babu yawa… Ya babu
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/11/22, 23:49 – Nuriyyat: 73
“Rubi, kiyi hakuri kome yana da lokacin sa, amma kukan ba zai miki maganin kome ba, Bilal ba irin sauran Mazan nan bane, idan kika ce zaki takura zai sallame ki” ta fada min a hankali.
“TOH”
Na fada tare da gyada mata kai.
“Wai ma na tambaye ki, Meye Yasaki kuka?” Ciro mata passport nayi tare da ajiye mata.
“Toh wannan shine matsalar?”
“A’a, kawai yadda yake watsar da kashi na ne, yanzun haka baikon shi za ayi idan muka dawo”
“Sure?” Ta tambaye ni,
“Really” na fada kwalla na kara zubo min.
“Am sorry bestie, na fahimci abinda yake damun ki, but inshallah zan miki wani bayani.” Zama tayi na zuba mata ido, ta shiga tsara ni.
“Bakin gaya min zuwa Steven kamar zai yi Hauka ba?”
“Hm” na fada mata.
“Toh yanzun zai yi haukar gaskiya, kuma ki duba lambar Steven koda kin tafi can keep yourself busy da wayar Steven”
  “Nagode Nagode sosai” na fada ina rike hannunta.
“Karni nuna mishi kin ji zafin abinda yayi miki kawai nuna babu kome, ayi baikon mana,sannan Karki damu a can duk wanda yayi miki magana ji bashi amsa.”
Gyada mata kai nayi tare da yarda da abinda ta faÉ—a, haka tayi ta bani shawara. Bayan na gama hiran na nufi kamfanin, a wurin parking lot na gan su, kamar zata shige jikin shi, sai wani yauki take, dauke kai nayi na nufi cikin kamfanin. Ina shiga na hango Baba Tunde. Isa wurin shi nayi muka shiga hira,har da dariya irin yaushe gano, ba iya shi ba hatta sauran ma’aikatan suma haka muka taru muna hira, tun daga bakin kofar, yake watsa min harara. Aikuwa naki kallon shi, har zai wuce ya dawo tare da cewa.
“Aiki ku kazo ko hira?” A hankali suma shiga watsewa, tare da nufar inda suke, ban d’ago kai ba. Sai wasa nake da wayata. Garin latse latse na,na latso number Steven bugu daya yayi, nayi maza na kashe sai ga kiran shi. Idanuna da suka jima cike da kwalla na mai da, sannan na dauka.
“Bro I miss you”
“Me too lovely, nazo na dauke ki ne?” Wuce Mr Jikamshi nayi, ina faÉ—in.
“Eh kazo muje, ina jin yunwa” na nufi Elevetor. Cikin zafin nama ya biyo ni, cikin elevetor din, da gangan na shiga karya murya tare da narkewa ina zuba shagwab’a.
“Aahh! Wallahi ba zan yarda ba tunda ka sumbaci, kumatuna…” Fisge wayar yayi yana huci, sannan ya kashe. D’ago kai nayi ina kallon shi.
“Meye matsalarka dani?” Takowa yayi kamar zai shige jikina.
“Sai na sab’a miki idan kika sake na ji labarin kin fita lokacin tashi bai yi ba”
Kasa kasa nayi da murya.
“Fa sai na fita,haka kawai dan ana min bakin ciki da samun saurayin da nayi” buge min baki yayi.
“Dan ka ga bani da kowa shine kake wulakantani” tsaki yayi lokacin da kofar ta bude, ina shiga office na zauna ina mita,na bar kara maka kuka.
      Ban gama abinda yake ba, Khalil ya shigo.
“Ke baki san kwanakin ki a kirge suke? Kina ta kokarin kare shi ance miki ya damu dake ne? Karuwa ki saka ido”
  Ya fada min har zai fita na ce mishi.
“Wild dog!” A fusace, yayo kaina. Tashi nayi na tawo gaban shi.
“Tafi can,ragon maza idan ka isa ka tafi ka tun kare shi idan har na miji ne kai. Kai ko ni baka isa ka min Iskanci na kyale ka,Balle Bilal ka zata bai san waye kai bane? Ya sani dan tuntuni na tura mishi sakon ka, da kuma kome akan ka,ka rufawa kan ka asiri ka bar kamfanin kafin mu tasaka a gaba da gudu” nafada ina tura baki.
  Wani irin yanayi na gani a cikin idanun shi.
“Kina nufin Bilal yasan ina farautar rayuwar shi?”
“Ji min sakarai! Tun yaushe ba iya shi ba hatta Yallabai Faisal ya sani,kowa ma ya sani kawai muna jiran action dinka ne dan basaja” da sauri ya fita. Dariya na saka ina bin bayan shi da harara.