NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

       Bayan fitar shi da minti goma,sai ga kiran Mr Jikamshi. Hararan wayar nayi ina murguda bakina.
“Hmm!”
“Kizo” ya fada, tashi nayi bayan na kifa wayar.
Na fita sannan na nufi office din shi.
Ina shiga na hango shi wurin zaman shi.
“Iso nan”
Ya fada min, ba musu na isa duk abinda mukayi da Khalil ne. Da hararan shi da nayi, da murguda bakina  da nayi. Kallona yayi tare da juyar da kujeran.
“Tun yaushe kuka san juna?” Ya tambaye ni.
“Kawai na san shine a Paris da suka zo niman a rusa kamfanin ka, shine naga bayanin kome a laptop din shi da yadda zasu kashe ka.”

  “Ok, Meye naÆ™i idan suka kashe ni?” Tura baki nayi tare da cewa.
“Ina tausaya maka ne karka mutu Gwauro”
“Ke” ya daka min tsawa, hararan shi nayi kasa kasa.
“Are insane me?” Ya tambaye ne,
“A’a” na fada kamar zan make shi.
“Out” daidai Steven ya kirani.
“Hello ok gani nan zuwa”na kashe wayar.
“Waye?” Ya tambaye ni,
“Steven ne zamu cin abinci”  na fada ina kokarin fita.
“Babu inda zaki!” Ya fada min, kallon shi nayi tare da cewa.
“Idan na zauna me zan maka? Fada da tsawa shi zaka min, shi kuma idan na tafi wurin shi zai rarrashe ni, zai saka ni dariya” daga haka na fita a office din,  na tafi office dina, ina cikin hada kayana ya shigo. Hannun shi daya a cikin Aljuhun wandon shi.
Kallon shi nayi kafin na dauke kaina.
“Hmm” na gyara murya.
“Wani abu ne?” Tambayar shinayu
“A’a”  ya ce min, a hankali na juya na hada kome na fita, abina. Tunda na fita na same shi ya zo, da wata shaidaniyar mota, fitowa yayi ya bude min kofar. A hankali na taka har wurin.

      Ina shiga ya rufe kofar,sannan ya dawo ya shiga tare da jan sitbelt ya saka min, muka bar kamfanin.
“Faisal ya tafi da ita”
“Uban me zan maka?  Gwara ya tafi da ita tunda baka da mutunci kona miskazarata, banza kawai” ya kashe wayar.

   Zama yayi a cikin office din shi har aka tashi bai fita ba, sai da Faisal yazo da kan shi, ya ja shi suka tawo gida, daidai Steven ya fito ya bude min kofar motar na fita, sannan ya kwaso bags din da ya min sayayya, ya mika min.
“Thanks”
“Baka gaya min kome akan Mama da Obinna da Mom ba?”
“Next time zan gaya miki kome” gyada mishi kai nayi,ina tsaye har ya bar gidan. Sai lokacin Suka shigo harabar gidan, shiga cikin gidan nayi bayan naga irin kallon da yake min.  Tun ban kai cikin gidan ba, yayi mugun tsorata ni.
“Ka bani tsoro” na fada ina kallon wurin da motar Faisal yake. Kwace kayan yayi.
“Wallahi ka tab’a min kayana, zaka janyo abubuwa dayawa mara dadi, ina son kayan dan daga hannun mutumin da ya fara kokarin inganta rayuwata ce,shine mutum na biyu bayan Dr Musa da iyalin Dr Hayat Abdulwahab Moddibo karka watsar min da kayana.” Na fada, tare da amsar kayan na shiga cikin gidan, na samu Ya Rahmah sai Ammyn.
“Auta!” Kallon su nayi, kafin na cewa Ummin.
“Good day Ummina” daga haka na wuce dakina. Na zuba kayana ina kokarin cire takalmina Ammyn ta shigo.
“Don Allah ki saurare ni mana” d’ago kai nayi ina kallon ta.
“Tunda kika bar gida ban kuma barci cikin kwanciyar hankali ba, Auta ba zaki tausayawa Rayuwar mahaifiyar ki ba?”

“Allah ya baki lafiya” na fada bayan na nufi ban daki, ruwa na bude,na zauna a gefe guda, ina jin magiyarta, kawai kuka nake a cikin ban dakin. Sai da na daina jin maganarta nayi wanka na fito. Rahmah ce zaune ta bude kayan da naxoe dashi tana kallon chocolate cake da sauran kayan zakin.

   “Ammyn tana bukatar ki” ta fada min bayan ta bude chocolate din tana cikin.
“Tana dai bukatar ku, amma ba ni ba, ita da take da Yaran irin ku me zan mata?”
“Mahaifiyar ki ce fa?” Ta fada min.
“Sallamawa duniya Ni tayi, me kike so nayi?”
“Amma hakkin uwa fa?” Juyawa nayi ina kallon ta.
“Ban san shi ba” na fada mata,
“Baki da kawazuci ne?”
“Bani da shi”na gaya mata,
“Allah ya baki hakuri” ta fada muryanta na rawa.
“Amin” tare da É—aukar bra na saka sannan na dauki rigar da skirt English wear na saka. Kafin na fito falon.

   “Kiyi hakuri inshallah idan muka dawo zan duba al’amarin” ya fada yana kallon Ammyn. Wurin cikin abinci na wuce na dibi tuwo miyar kubewa, na zauna ina ci.
“Adawiyya baki ga Ammyn bane?” Inji Faisal,
“Na ganta, sannu Ammyn Jamilah” daga haka na cigaba da cin abincin. Zuwa Bilal yayi ya zauna a kusa dani.
“Iyaye ba abin wasa bane, ki daina yin haka domin da zafi ko ke aka yiwa sai kin ji kamar ki mutu ki huta.”

  Daga glass cup nayi na sake shi akan tales,ya fashe.
“Zaka iya gyara fashewar da tayi?  Idan da tana sona saurarron ba’asin bakina zata yi, sannan ta janyo ni ta ce min. Abinda kike bai da ce ba,Bana cikin yaranta domin ita ta cire ni da kanta kasan me yasa nake zaune da kai duk abinda kake min bana jin zafi. Idan nayi wani abu kana min fada, kasan me yasa nake son kasancewa da Steven idan ina tare da shi ina jin farin ciki mara misaltawa. Ina tare da Ya Faisal ne domin ya kirani kanwar matar shi tun haduwar farko. Umma ta kirani da suna me daraja, Ummin ta kirani da Dota. Ammyn na ta ce ta yafewa duniya ni? Bilal kasan dare nawa na ketare ban yi barci ba?

Kasan iya yawan tears din da suka zuba daga idanuna? I love my Mother much love da ban tab’a sanin ina mata ba, Bilal tun kafin na bar gida bana barci a jikin kowa sai a jikinta,  amma Ammyn tayi recject dina, sabida Ya Jamilah. Kowani cuta tana da magani ni tawa cutar bata da magani. Dukkan su sun fasa min zuciyata. Sun lalata min gobe na, kuma sun juya min baya” daga haka na bar falon,daki na nufa na dauki sweater coat. Da takalmi na fita,

“Na sani nayi laifi, kuma nayi kuskure. Wallahi ban ki Rabi’atu dan bana son ta ba, nayi haka ne dan Farin cikin Jamilah. Hajiya Atikah na bar miki amanar ta, zan koma gida” ta fada tana share kwalla.

   Can garden din gidan na nufa na zauna ina kuka, zama yayi kusa dani yana faɗin.
“Ya isa iyaye ba abin wasa bane, dan haka ki tafi ki bata hakuri, idan kina son Rahman Allah” kallon shi nayi.
“Ina jin zafi kamar zuciyata zata dirko daga kirjina”
“Toh ko bata hakuri” tashi nayi nazo inda Faisal zai mai da ita gida,  shiga motar nayi, na zauna a kusa da ita. har Rahmah zata shiga sai ya ce mata.
“A’a dawo dare yayi kin ji”
Kallon Bilal tayi kamar zata yi kuka, ta ce mishi.
“Karka manta Baby yana tare da kai”. Fitowa yayi daga motar, ya durkusa gabanta, dai dai shigowar Alman.
“Zo nan”  ya kira shi.
“Ga Mata ta, da Babyn mu bari na kai Ammyn gida “
“Ban gane ba, kawai ka tafi da ita ko Oppa”
“A’a muje dai kai ka zauna a gida da ita Rahmah bari mu dawo” haka suka shigo matar.
Har Mun fara tafiya Bilal ya ce.
“Ammyn ki bani Yarki mana da aure?”
“Toh Bilal na baka ita da aure Allah ya baku zuri’a ta gari, don Allah ka kula da ita, tana cikin maraicin Uba aka raba mu, yau gashi ina jin wani irin kewarta sosai.”

“Nima haka nake jin kewar ki Ammyna, ina son ki sosai ba zan kuma tafiya na barki ba.”
“Idan Allah ya nufa zan tafi na bar ki, amma Æ™arki manta duk abinda zai faru ki tsaya a tare da Jamilah, ko dawo min da Jamilah na…..”
Garaaaaaaaaaa, wata babbar mota ta daki motar mu….
Bilal, Faisal, Ammyn, Rabi’atu…. Me zai faru next.
3/11/22, 23:49 – Nuriyyat: 74

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button