WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
   Lokaci guda al’amarin ya juyawa kowa baya, sai da Bilal ya ga fitar su baki daya daga Kasar, sannan ya mai da hankalinsa kan niman Dr Musa. Tare da taimakon Steven, suka yi ta shiga inda aka ajiye Rabi’ah, sun yi aiki kamar me, amma aikin nasu kawai bincike ne basu magana da junan su, sabida kowannen su yana ganin shi ya dace da Rabi’ah.
 **
Garin Maradi.
 Kallon Junainah Hajiya Anum tayi tana tsaye tana kallon waje, kasancewar tana barandar bayan ne, dafa kafadar ta tayi ya juya tana kallon ta.
“Mama!” Ta fada tare da share kwalla,
“Adawy ko?” Gyada mata kai tayi.
“A ina zan ganta?” Allah yana sane,
“Assalamu alaikum! Ummee Abba yana kiranki” inji Muhammad, me sunan Baban Anum.
“Ok” ta fada tare da fita, kallon Junainah yayi, kasa Æ™asa yana dauke kan shi.
“Jiya da mace kar na kuma ganin ki da Aliyu baki ji ba ko? Wallahi sai na mugun saba miki” ya fada mata bayan ya tawo gaban ta.
“Ya Muhammad don Allah ka daina bana son abinda kake min” wani banza kallo ya watsa mata, sannan ta fita yana murmushi. Ya lura tsoro ne ya cika ran ta, amma da wata yar bala’in ce da tuni ta kwaci kanta.
  Sauke idanun ta tayi kasa tana jin wani irin kwalla na kara zubo mota.
A kasa kuwa Zama Hajiya Anum tayi tana kallon shi kafin ta ce mishi.
“Yallabai ya batun?”
“Zaki fara isata da magana ko abinci baki bawa Dan tsohon mutum ba” mikewa tayi ta shiga shirya mishi abinci,. Sannan ta zauna yana ci suna hira har ya gama sannan ga shiga bata labarin sakamakon binciken da yayi a Nijeriya.
“Na tafi har Jigawa, inda na samu labarin shi Mahaifin Junainah, sai dai abinda na samu ya daure min Kai domin dai basu kashe shi ba, sai dai na samu wani Yaro da yake bincike akan Rabi’ah shekaru biyar baya ya sake samun daukar shi. Inda nake da yakinin ya tafi da shi.” Cikin zakuwa Anum tace mishi.
“Waye yaron?”
“Eh toh naji suna kiran shi Steven. Dan sun ce ba musulmi bane amma ya tafi da shi duk inda yake Inshallah yana cikin kwanciyar hankali, sannan yayi kokarin nima yaron ta hanyar internet ban samu ba, sai dai zan kira Baban Bauchi ya duba min tunda na fahimci Allah ya mishi bai akan computer”
  Gyada kai tayi tare da mikewa,.tana fadin.
“Ai kasan Babana sai du’ai wai yana son Junainah amma sai bata wahala yake, bai da aiki sai fada da tsawa, don Allah ka mishi magana, kawai dan ya ganta da Abba ne fa yake wannan dacin ran”
  “Toh, ai ba laifin shi bane ina ke ba dan na kai zuciya nesa ba Meye baki min ba, har rashin darajan da kika min kawai dai ina da hakuri ne da ban da haka waye ina ji yana ganin ki zai kyale ki” wata Æ™atuwar harara na mishi.
“Ina cewa kai har a shago baka barni ba, wallahi babu irin muguntar da baka min ba” ta fada tana tura baki.
“Aikin kenan ba a girma sai na jiki, zauna ki ga jika tazo miki”
“Allah ya shirya ka”
“Amin”
**
Kano.
 Bompai Police headquarter.
Mikawa Na maroko hotunan Yara yayi tare da cewa.
“Ba nazo ka bata min lokaci bane, ina yaran nan suke, idan na cire Altine da Rabi’atu suna ina sauran?” Sunkuyar da kai yayi kafin ya ce mishi.
“Sauran yan matan wasu suna Æ™asashen waje, wasu na nan tafa kamar Altine tana nan Tafa.”
  “Ok! Sannan ba iya su Rabi’ah aka fitar daga DaÆ™ayyawa ba akwai wasu suna ina?” Shiru yayi kafin ya ce.
“Ka tambayi Hajiya Yar Duwala”
“Ok Ya maganar Dr Musa”
“Shekaru biyar da suka wuce an samu labarin ya tsare a inda muka ajiye shi, iyalin shi ma basu nan domin an ce ya same su.” rufe file din yayi yana kallon Mataimakin Kwamishina, kasancewar daga Office din IG aka basu binciken.
“Nagode sosai Yallabai Nagode da hadin kan da kuka bani, sannan idan da hali a tura su kai tsaye Abuja can za a yi Shari’a”
“Ok sir” yana gama abinda zai yi ya fito.
“Mr Jikamshi, yanzun na samu sakon nan daga Nijar akan Yar Dr Musa, kuma dama ina son na gaya maka Dr Musa yana hannuna, yanzu haka yana garin Gombe a can Asibitin Dr Hayat Abdulwahab Moddibo.”
  “Tun yaushe?”
“Kamar Five years”
“Good Job” ya fada mishi bayan ya wuce abin shi.
  Haka suka yi ta bincike,.har suka dawo Jigawa, inda suka tafi har Daƙayyawa. Nan ma binciken da suka yi tare da goyan bayan Hukuman kare hakkin dan Adam, aka yi akan Yaran su da suka fita, kofar gidan Baba Haliru suka nufa.
  Yana zaune a kofar gidan, sai haukar shi yake idan yayi surutun sai ya kama gaban shi ya rike gam, yana wasu irin maganganu.
“Wannan Kanin Baban su Adawiyya ne, wannan shine karo na uku da nake ganin shi bayan na fadadda bincike na”
“Hmm” ya fada tare da jan motar suna barin kofar gidan.
Wayar Steven ne yayi kara ya duba.
“Trouble maker! Hello Sabrina!”
“Ka samu kawata kuwa?”
“Eh na same ta wata uku da suka wuce wani abu ne?”
“Kai Uncle Steven shine ba zaka bani ita mu gaisa ba”
“Kin ga Sabrina bata kasar xan turo miki number ta na Korea”
“Yawwa Nagode” ta kashe wayar.
“Wacece?” Bilal ya tambaye shi,
“Kawarta ne lokacin da kawuna suka yi Adopt dinta, suka saba sosai itace Yar Dr Hayat Abdulwahab Moddibo.”
“Ok na gane, amma me yasa baka koma gidan ku ba?” Kallon Bilal yayi.
“Akwai matukar damuwa ace uwar da ta san zafin haihuwa ita ce zata sayar da dan wani, kasan yadda abin yake? Ta damu dani amma bata samu da dan wani ba, kasan yadda nake ji? Hmm”
“TOH ya za ayi iyaye ne sun wuce gaban kome, kayi kokarin ganin ka gyara tsakanin ku, Bamu da na biyon su a duniya.”
“Ok Nagode”
Bayan sun gama hiran kowa ya dawo da sabon rashin darajan shi, wato share juna da suke yi.
  **
Busa Korea.
   Rike nake da Deedat, yana niman abincin shi. Kallon Umma nayi naga hankalinta kwance, tana haɗawa Rahmah abincin.
“Umma wai Ya Rahmah ba zata fito ta bashi abinci bane naga sai Rigima yake”
“Eh kinsan tana fama da baban Shine bari ta gama ta fito ko” ta fada tana kallon Yaron, tana mishi wasa.
A can dakin kuwa majinyaci ne da nanike matar shi, duk da danyen goyon da take da shi bai hana Faisal zakewa yana kwasar gara ba, domin sosai ya samu yadda yake so….
3/13/22, 07:06 – Nuriyyat: 76
Domin sosai Umma take gyara ta, kuma ta lura bai da hakuri a ta wannan bangaren shi yasa take sake hada mata wasu abincin masu kyau da gyaran jiki, musamman traditional Aphrodisiac na asalin albarkatun tsirai. Irin su Walnut da salat, idan aka haÉ—a da ganyen da purple cabbage, ba karamin al’amari bane domin har tab’a mace yake na fitar hankali, haka Yasa shima Faisal din Umma take hadawa da shi.
  —
Can waje na fita na samu Ya Jamilah zaune tayi shiru tana kallon tsuntsayen cikin garden din.
Zama nayi kusa da ita, ina kallon wasu tsintsaye.
“Ya Jamilah.” Goge kwallar da ta cika mata Idanu tayi.
“Meye yasa kika fita a cikin mu?”
“Babu” ta bani amsa a takaice.
“Toh meke damunki?”
“Babu”
“Kinsan inda matsalar take?” Juyawa tayi tana kallona.
“Matsalar da aka samu kina da son kai, kuma zuciyar ki a rufe take, da tana buÉ—e da zaki fahimci yadda rayuwa take, koda kaddaranki ta same ki, makantar dake yai ya hana ki kallon gaban ki! Kiyi hakuri na fada miki magana mara dadi. A kasashen da suka cigaba ba a barin masu irin matsalar ku su kadai, sai an yi musu treatment na musamman domin. Samun irin wannan yanayin. Tun zuwan mu na samu Yoona zai kai ki ganin likita next week”