WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
“A ina kasan wannan mutumin shine dalilin dawowar mu nan domin yazo sau biyu, karshe ya ce mu bar abuja, bayan mun dawo muka samu labarin an shiga cikin gidan an zata muna nan ne, yana da kirki ya ce mata Rebecca ya je nima” rike hannun ta yayi tare da cewa.
“Shi yasa bani shawaran nazo na duba ki”
“Allah ya mishi albarka, itama kuma Rebecca tana karatu ne?”
“Eh toh ina ga zata fara ne dai yanzu, ina jin zata cigaba ne a dakin ta ” cikin wani irin farin cikin ta ce mishi.
“Zaka aure ta ne?”
“A’a shi dai dai aure ta, shi ya fi dacewa da ita, mutumin da ya saka kan shi a hatsari sabida ita shi yafi dacewa da ita ba ni ba, kuma iyayen ta musulmai ne ba zai yiwu. A koma can ba ita kuma suna daka mata hope din zata dawo gare su”
    “Kuma haka ne, ka kyauta hakan na.” Tashi yayi Mama ta nuna mishi dakin shi.
 **
Lagos.
Duk inda Hajiya Shuwa taso, a dauki fansar Yarta abu ya ci tura, yarinyar idan ka ga yadda Yarinyar ta koma kamar ta shekara goma tana jinya tsabar matsalar da maranta ya samu ta fita hayyacinta, tayi wani irin mugun ramewa, sai yar wuya da ta saka kamar markin lema.
  Kallon Suhaima Hajiya Shuwa tayi tana faɗin.
“Ki kula da ita, bari na dawo” fita tayi sai da ta bar asibitin sosai sannan ta kira Bilal ta gaya mishi abinda yake faruwa.
 Bayan sun gama waya ta kashe wayar, sannan ta kira Bilal ma bata samu wayar shi ba, da bakin ciki ya dawo asibitin.
“Kiyi hakuri kin ji Zuhairah”
..
Gidan Hajiya Turai, kallon Humaidah tayi sannan ta ce mata.
“Uban me kika zo min?” Dariya Mimih tayi sannan ta cewa Maman ta.
“Maam nuna mata ta gani,. Ikon Allah har da yar gaba da fatiha” ta fada tana kallon Hajiya Turai.
“Ban san rashin kunya.” Mika mata ipad din suka yi hoton Nadrah Ali Ruma ce a zaune a gadon asibiti, tana shayar da Babyn ta, a bisa tsautsayi tana É—aukar ipad din ta wurga akan fuskar Hajiya Humaidah, abu yazo ga tsautsayi kawai ya daki gefen wuyar ta, faduwa tayi tana shure-shure. Kafin kace me jini ya fara fita daga cikin hanci ta baki.
“Wayyo Allah na, Maam” Mimih ta fashe da kuka, wani irin tsoro ne ya kama hajiya turai.
  Da gudu suka fita da ita zuwa asibiti, tsabar ta razana baki daya fada take.
“Wallahi ban kashe ta ba, wallahi ba da gayya bane” wannan abin yasa aka kira yan sanda, suna isowa kawai aka tafi da ita. Abun tausayi lokaci guda kome ya runcabewa JF baki daya, domin kamar hadin baki kome ya lalace.
    Hajiya Humaida a gadon Asibiti, suna cikin wannan yanayin, kawai aka kira su aka ce ga kamfanin su na JIKAMSHI Group campany ya kama da wuta, innalillahi Alhaji Abubakar da Alhaji Adamu, kamar zasu haukar kafin kace me wutar ta kona kashi saba’in na cikin kamfanin.
Ummyn da take cikin kamfanin, dakyar aka ciro ta, Asthma dinta ya tashi, kai tsaye aka kira su Bilal da Faisal. Alhaji Abdulkadir sai da ya fadi, jinin shi yayi mugun hawa.
**
Korea.
  Tun safe muka shirya, kallon shi nayi lokacin da na fito ina shirya abinci a cikin wasu irin warme masu kyau, ganin yadda na juya ina kai sai gan shi nayi ya dauki tsokar Nama ya saka a baki.
Juyawa nayi na gan shi kamar zai shige jikina.
“Amma wannan abin da kake bai dace ba, ajiye Dalla”
“Idan naki fa?” Ya kai bakin shi kamar zai sumbace ni, kauda kai nayi ina hararan shi.
“Matsa min Dalla” na take kafar shi ina hararan shi. Haka muka gama shiru muka nufi Rehab. Muna zuwa lokacin ana fito dasu, kallon mu tayi take fuskarta ya sauya.Â
“Ya Jamilah ya kike?” Na tambaye ta, kallon Rahmah tayi tana karban Deedat.
   “Wow Deedat ya girma” kowa ya mata magana ta amsa amma ban dani, shi kuwa Bilal yaÆ™i mata magana ya shiga tayani sauke abinci.
“Mr Jikamshi abinci ka kawo min?” Ta tambaye shi, wani irin kallo yayi mata. Nima kuma kallon shi nake, ina jiran naji me zai ce mata, hura min iskar bakin shi yayi yana faÉ—in.
“Kalli gabanki” Murmushi nayi na juya ina aikin sai jin sassanyar lips din shi a cheek dina, wani irin ware idanu nayi ban san lokacin da na rufe bakina ba, na juya muna kallon juna.
Bakin shi ya kai gashina ya sumbata, wani irin yanayi na tsintar kaina a cikin farin ciki mara misaltawa,kallon shi nake shi ya cigaba da shirya abin. Kwalla na cika min idanu ya ce.
“Ba zan bari wani ya wofatar min dake ba, You Are my little Queen, duk abinda zaki yi ki tuna ina tare da ke.” Gyada mishi kai nayi ina jin wani irin abu yana yawo a kaina.
  Baki daya sai farin ciki Yan uwana suke, idan ka cire Jamilah, da take wani harara ta.
“Mugun ido mugun baki, mugun zuciya ya sauka akan masu mugun nufi”
  “Amin” inji Wasilah, nan aka shiga hira Faisal shima dariya yake.
“Ke bude baki na saka Miki abinci bana son wannan rashin son cin abinci ba zan yi kiwon ulcer ba” tura baki nayi ina faÉ—in.
“Ni ba babyn ka bane, sai dai Kabawa Deedat.”
Muna cikin haka wayar shi yayi kara, kallon.wayar yayi sannan ya saka a kunne.
“Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha, gani nan zuwa”
Kashe wayar yayi sannan ya shiga bashi labarin abinda ya faru, Innalillahi.tashin hankalin da Faisal ya shiga babu iyaka dan haka ya ce zai tafi. Haka suka tafi shi da Bilal da Rahmah da wasilah ni kuma na zauna a wurin Jamilah.
  Daukar abincin da nake ci tayi ta dauki spoon din Bilal tana kallon abincin, dauke kai nayi na fara wanke hannu.
“Ina son Bilal! Kamar yadda ya iya kiwo nasan zai iya bawa mace kulawa a gado!” Murmushi nayi domin ta fara bani dariya.
“Nice zan gaya miki haka, domin duk lokacin da na kwana a dakin shi sai na gasa jikina da K’uguna, domin ina amsar Bulalar shi sosai ga kyau ga na nagarta, doguwa kakkaura….” Tass ta wanke ni da mari sai da kowa na wurin ya juya, Ashe ya dawo ta kowa yayi ya shiga hada kayan. Shafa fuskana yayi tare da kallon cikin idanuna..
“Jeki mota gani nan zuwa” ya fada min.
“Toh” har zan tafi na dawo tare da rike damtsen hannun shi, juyawa yayi ya Kalle ni.
“What?”
“Na yafe mata” dawo dani yayi gaban shi kawai ya daura bakin shi a saman nawa….🤔 Allah yasa kar ya iskanta musu yar mutane ðŸ˜ðŸ˜‚🤣 cicina
3/15/22, 15:30 – My Mtn Number: 81
Tun lokacin da yayi min daya a Paris, ba zance ban shiga wani hali ba, amma na yau ya sani jin kamar da numfashi na, yake tafiya dani baki daya mutanen wurin sai cewa suke.
“Wow.. wow!” A hankali ya janye bakin shi daga nawa, Ni kam idanu na a rufe, sai wani siririn hawaye da yake sauka daga idanuna. D’ago fuska na yayi yana kara sumbatar goshina.
“Open your eyes.” Kamar dama jiran haka nake na bude idanuna a hankali ina kallon shi.
“Jeki mota gani nan zuwa”
Gyada mishi kai nayi, har zan wuce na ce mishi.
“Please karka mata kome”
“Toh” ya faÉ—a a hankali, tattara kayan ya shiga yi na juya ina kallon Ya Jamilah, sannan na wuce Abuna ina jin wani irin daci a raina.
   Takawa yayi gaban ta, yana jan wani irin iska kafin ya san ciji lips din shi ya ce mata.
“Kinyi sa’a, ina son YARINYAR can kamar Hauka Kuma ba zan iya dauke kai daga alÆ™awarin da na mata ba, da na baki mamaki jaka wawuya sakarai Yo ko mata sun kare ba zan tab’a auren lust irinki ba wacce bata da kunyar abin kunya. Kin zata zan kyale ki ne, bari na barki sabida ita. Duk ranar da kika kuma sai na baki mamaki jaka kawai” ya fada kamar zai mare ta.