WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  Kayan ya kwasa yayi gaba abin shi, bin shi tayi da wani irin kallo na tsannanin kauna da sha’awar shi ya bishi da shi. Har ya b’ace mata, ajiyar zuciya ta sauke daidai lokacin da matar da take kula da ita ta iso, wato caretaker da take kula da Jamilah. Ba wata babba bace kallon Jamilah tayi ta ce mata.
“Barka dai” cikin gurbatacce turanci da ya sha mazga da sambadede Koreanci.
“Hmm”
“Uni sarauyinki ne da ya koma wurin wata?” Kallon ta Jamilah tayi tare da cewa.
“Eh” cikin wani irin yanayi kamar zatayi hauka.
“Toh a dawo miki da shi wurin ki mana” kallon ta tayi sannan ta gyara zama ta ce mata.
“Kamar Ya?”
Kallon gefe da gefe tayi sannan tace mata.
“Uni zamu kai su wurin Shaman ne(wato boka in Korean language) “
“Shaman” ta fada a hankali,
“Eh ban san yadda zan miki bayani ba, amma amma kin san bakin sihiri (wato Black magic)?”
Saka hannu Jamilah tayi a bakin ta, manyan idanun ta masu shegen kyau, ta ware su akan Matar.
“Ban taba yi ba kawai manta da shi kawai”
“Amma idan kuma babu alamar zai dawo dole a kawarda wacce yake so a dasa mishi soyayyar ki” inji matar.
“A’a kar a musu kome, kawai a sauya soyayyar ta da nawa a ran shi.”
“Toh zamu je wurin shi” matar ta gaya mata.,
“Taya zamu fita?” Dariya matar tayi sannan, ta ce mata.
“Kwantar da hankalinki, zamu fita indai nice”
   “Toh” ta fada tana kallon, Matar har suka koma dakin su,
 *
A daren ranar da aka fadi labarin halin da su Ummyn suke ciki a daren suka bar korea, suka barni tare da Umma domin sun dauki Junainah. Da zai tafi sai da yazo gabana ya tsaya yana faÉ—in.
“Ƙarki kuma zuwa wurin Jamilah idan ta miki wani abu zan saka a rufe ta har karshen rayuwarta”
“Amma”
“Gaskiya na gaya miki, kika sake kika tafi wurinta tabbas Abinda zan aikata kenan” ya fada min.
“Kayi hakuri ita kamar Amma ce a wurina, Ammyn ce ta bani amanarta don Allah kayi hakuri naje.”
Murmushi yayi sannan ya ce.
“Ok” ya juya zai tafi, rike rigar shi nayi.
“Karka kace yi fushi ba zan je ba” murmushi yayi sannan ya juyo gare ni, yana dauke kwallar da yake sauko min.
“Ƙarki damu ba zan yi fushi dake ba, ba zan taba fushi da ke ba, idan ta miki wani shirme ne dan dauki mugun mataki akan ta” gyada mishi kai nayi, ins ce mishi.
“Kuka kake kai ma?” Na fara kokarin leka fuskar shi, buge hannuna yayi yana faÉ—in.
“Ke meye haka?”
“Leka fuskar ka nake ko kana kuka” abin dariya, girgiza kai yayi sannan ya ce min.
“Akan me zan yi kuka?”
“Na sani ko dan zaka tafi ka barni ne” murmushi ya saka yana kallon yadda nake kokarin saka shi dariya, haka ya wuce yana d’aga min hannu, da gudu na tafi wurin shi ina cewa.
“Idan ka tuna dani, kasan me? Ka sayi ice cream. Minti choco kasha min kai kuma sai ka sayi drink kasha naka”
“Mahaukaciya” ya fada yana jan kumatuna, haka suka shiga jirgi, ina kallon su, suka bar garin da kasar baki daya.
  **
Kallon su Shaman yayi sannan ya ce musu.
“Kinsan abinda ake kira Kaddara? Idan har kin san me ake kira hakuri ki janye maganar saurayin Kanwarki, domin zaki mutu a wulakance, idan da maganar ki zai raba su tabbas da tuntuni yayi hakan? Amma ina ba a yiwa Æ™addara kutse ita ke da damar yiwa mutum kutse a rayuwar shi”
 Shiru tayi kanta a sunkuye kafin ta d’ago kai.
“Babu yadda za ayi a raba su baki daya?” Ta tambaye shi.
” Ba zasu iya rabuwa da juna ba, idan har zasu rabu tabbas kece zaki mutu, kuma mugun mutuwa dan ko gawarki ma ba za a gane shi ba” wani irin tsoro ne ya kamata tunda take bata tab’a ganin wanda ya gaya mata gaskiya haka ba sai wannan bokan.
“Aikin ki me sauki ne amma ina son rayuwata, domin duk wanda yayi miki wannan aikin karshen shi baya kyau, ina iya hada soyayya na raba masoya. Amma wannan soyayyar su ba zata rabu ba, dan ita din kusan dukkan rayuwar shi ne, dan haka kina da wanda yake son ki, Kuma ba iya shi ba akwai wasu ma suna son ki. Ki tafi gare su, idan kika matsa dole ayi aikin zaki wahala kuma zaki mutu. Nima kuma zan rasa hanyar cin abinci na kin ga duk mun yi asara kenan, amma ki tafi wani wurin a yi miki aikin”
   Ya fada mata, ta zata wasa ne ta mike tare da ajiye mishi. 40k won na kudin korea, ta fita. Ita da matar suka nufi wani gidan bauta na Buddish. Suna shiga malamin majami’ar ya ce mata.
“Ba zamu iya raba miki su, idan kika nace Æ™addara tana bibiye dake”
   Mamaki ce ta kama Jamilah, dan haka ta juya suka fita, a hanyar su ta komawa ne, wata babbar mota tayi kan su.
Idan kika nace ƙaddara tana bibiye dake wani irin ihu suka saka motar ta takka birki. Ajiyar zuciya suka sauke lokaci guda.
  Haka suka fito daga motar suna haki, a matukar tsorace suka koma Rehab. Tun daga ranar take shirya yadda zata cusawa Rabi’ah bakin ciki.
 **
Sun isa najeria da safe, dan haka suka nufi gidan Ummyn suka yi sallah, Rahmah da wasilah suka kwanta, su kuma Mazan suka wuce asibitin, ajiyar zuciya suka sauke lokacin da suka samu ta farka, zama suka yi a gefen ta.
“Ummyn Sannun hankalin mu ta tashi wallahi”
“Da sauki ai.” Nan suka gaya mata yadda suka ji labarin, itama ya gaya musu yadda kome ya faru domin tafi zargin gas ce ya fashe.
  “Ance Yaya Abdulkadir yana nan, Shuwa da Humaidah suna nan basu da Lafiya.” Ta fada musu, a dame.
“Allah ya basu lafiya” inji Bilal.
“Ina Yyana da Mamar shi? Ya dotana take?”
“Tare muka zo tana gida suna barci ne da wasilah, sai anjima zasu zo” daga nan suka wuce sauran dakunan suka duba Hajiya Shuwa da yar ta, tana ganin Bilal ta fashe da kuka tana gaya mishi abinda aka yiwa yarta, ganin yadda yarinyar ta koma. Lallai dan Adam ba a bakin kome yake ba ganin yadda yarinyar ta koma yasa shi jin wani irin tsoron Allah a ran shi.
 Hakuri ya bata sannan ya wuce zuwa dakin Hajiya Humaida, wacce Mimih take zaune tana kuka, tana ganin Bilal ta mike da sauri ta fada jikin shi yana cewa.
“Oppa kaga yadda Hajiya Turai tayiwa Mamana”
“Allah ya bata lafiya.” Baki daya kan shi ya tsaya kome kallon shi yake,.yana fitowa suka yi karo da Nadrah da Irfan, mika mishi hannu yayi suka gaisa sannan yake mishi jajjen Abinda ua faru.
“Hakki ne ke tambayar kowa, ita Zuhairah wai challenges suka shiga na Sex shine suka yagata, ita kuma Hajiya Humaidah taje kai saran Nadrah domin ta kuntattawa Hajiya Turai Æ™addara ya fada musu.”
Amsar yarsu Bilal yayi ya kalli yarinyar babu abinda ta bar wa iyayen ta, sumbatar goshinta yayi.
“Allah ya mata albarka. Gata kamar Maman ta”
“Sai dai ko ni” inji Nadrah,
“Yanzun wani bom zai tashi domin Shuwa bata sani ba, yanzu zata sani”
  Dariya suka yi tare da cewa.
“Fatan nasara” suka wuce dakin Ummyn, nan Faisal ya kira Rahmah yasa ta kawo abinci,. Sannan suka nufi kamfanin su.
  Tunda suka ka tafi, Alman ke fama da kamfanin baya nan baya can. Kallon su yayi tare da zabga musu harara.
“Na gaji nima yanzu lokacin hutuna ne yazo sai kuyi ta fama” ya tattara ya bar musu kamfanin yana wani irin mika.
“Kai Yau kan na samu yanci” yana tashi ya nufi gida, tun daga bakin get kamshi ya cika mishi hanci, yana shiga Falon ya samu Wasilah da Deedat. Tana mishi magana yaron yana bin ta da ido.
“Hmm” ya gaya murya, juyawa tayi tana kallon shi.
“Baka iya sallama bane?” Kasa magana yayi yana kallon ta, domin gidan daga ita sai Rahmah ce, shi yasa bata wani damu ba, riga da wando iya gwiwar ta ne a jikinta, rigar kuma ta gaba net ne, dukiyar Fulanin nan ko arzikin saka mishi bra bata yi ba, kana iya hango shatin boons din ta. HÃ diye yawun yayi yana faÉ—in.
“Kina saka hijab sabida tuzurai irina, zasu iya fada miki baki shirya ba.” Yq fada yana kashe mata ido, da sauri ta kare kirjinta, wuce ta yayi yana murmushi.