NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

   …
Ina fita na gayawa Yoona inda zai kai ni, tunda na fita na zauna tare da shiru ina nazarin rayuwar da muke ne baki daya babu dad’i,

   Waiter din ne yazo ya ce min.
“Me za a kawo miki.”
“Americano coffee” gyada kai yayi can sai ga shi da shi. Yana kawo min na fara sha, ina jin kamar na fasa ihu, baki daya na rasa yadda zan yi da Jamilah, wallahi babu yadda xan yi da ita baki É—aya, bana son a fahimci matsalar da ke tsakanin mu balle ayi tunanin akan namiji muke wannan yanayin.

        Tashi nayi tare da shan rabin Coffee din sannan na tashi na ajie musu kudin su, nayi tafiya ta. A motar taxi  na tafi Rehab, ina shiga nayi na shiga hada kayan ta. Tana inda na barta.
“Ki zo mu koma gida, abinda Bilal yake bani ya baki kema kar ya hanaki”

Na fada mata, tare da fita na kai kayan taxi. Haka itama ta fito muka tafi gida. Ban gaya musu zan dawo da ita ba sai ganin mu Umma tayi, bata min magana ba, bayan na shiga dakina zube a gadon nayi. Kwalla ne ke zuba min, taya zan musguna mata? Amma idan na tuna last word na Ammyn mu sai naji na tsani kaina, domin ina gani matukar na mata wani abu Ammyn zata iya jin fushi dani dan ban rike amanar da ta bani ba.

         Ban san lokacin da kuka ta kwace min ba...

Kuyi maneji don Allah
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/16/22, 18:39 – Nuriyyat: 83

Haka muka cigaba da zama, kawai abinda na sani bana shiga harkan ta ne gudun kar ya min abinda raina zai b’aci amma ita niman hanyar da zata kuntatta min,  ban damu da abinda take ba domin bani da lokacin ta. Na kuma mata uzuri me tarin yawa, dan bana son ta gane ina jin zafin abinda take min.

      Ina zaune da yamma ya kira ni,
“Hello!” Na fada a sanyayye,
“Ashe kin dawo da Jamilah?”
Shiru nayi kafin na sauke ajiyar zuciya,
“Yeobo!”
“What!” Ya fada da Æ™arfi, murmushi nayi domin yazo bazata ne nima kaina kiran shin haka.

“Me kika kira ni da shi?” Ya kuma tambaya na,
“Babu kome, dama na ga zamanta a gidan shine mafi alkhairi, kawai ta dawo nan din zai fi akan zaman ta  can”
“Ok haka yayi miki?  Nan da sati biyu zan dawo sabida makarantar ki, itama zata dawo nan Nigeria muna kan gyara wasu abubuwan ne”

Ban san ya aka yi ba sai tsintar kaina nayi da cewa.
“Kai ma idan ka gama min kome nigeria zaka dawo?”
“Eh Rabi’atu!”
“Hmm” nace ina jin kamar na ce na fasa karatun anan korea ya mai dani Nigeria.
“Ko akwai wani abu ne?”
“A’a babu kome” sama sama muka yi hiran ba wai dan ina jin dadi ba, sai dan babu yadda na iya ne, kuma bana son ya fahimci raina ya É“aci da hukuncin shi, dan haka na share muka gama hiran na kashe wayata.

“Barka karamar karuwa” jin Ya Jamilah,
“Barka dai ya kike?”
Na fada mata, ina murmushin gefen baki.
“Kina nan sai manyance, kin zata kina da daraja ne? Ki cire Bilal a ranki zai fi miki sauki”
“Toh mahaukaciya! A gidan Uban waye ya gaya miki zan yi wannan kuskuren? Kin manta lokacin da aka kama ki domin shirya kisan kai bai miki ba? Ya Jamilah ko mutuwa nayi Bilal ba zai aure ki ba, kuma ko akan ki zan ga Bilal wallahi ba zan tab’a tsanar shi ba, mutumin da yayi grabbing din boons dina da suke tsattsaye, cikin natsuwa shine zai tab’a na wacce kowani mahaukaci ke tab’awa idan ya samu dama?  Kin san me? Idan har iskanci zan yi wallahi bari na gaya miki ko a cikin karuwai baki isa ki zama me gogen min takalmina ba, kuma idan na ce zan yi karuwanci Bilal bai isa kallon mace ba, sai da izinina. Hmm idan kika sake na fitar miki da tsantsan rashin kunya da rashin mutunci, kare ba zai ci ba, Jahila me halin dabbobi.” Na fada ina mikewa, tare ni tayi zata mare ni na rike hannun ta sai da kashin hannun yayi kara.
“Ki fita harkata bani da lokacin ki” na gaya mata sannan na wuce abu na, na barta da bina idanu.

     Ko a wurin cin abinci ina jin irin hiran da take da Umma wanda baki daya labarin halin da ta shiga take bata, ma rasuwar Ammyn.  Tana magana tana kuka, dukkan su sun zata har zuciyar ta ne, nan kuwa tsabar makirci ne, dan a kafaice kai kara na take.
“Umma ko zaki saka baki Rabi’ah ta daina fushi da ni, tunda ba zan tab’a auren Bilal ba ya gaya min ita nake so amma har Yanzu kish…”
“Enough! Ya isa haka karki zubda min kimata a gaban ta, don Allah bana son magana”

Sharrr hawaye ya wanke mata idanu, cikin shashekar kuka ta riko hannuna.
“Little sister ki daina jin zafina, wallahi ko ni da Bilal muka rage ba zan tab’a son shi ba” tashi nayi na bar wurin.
“Kiyi hakuri bata da matsala zan mata magana” ta fada tare da lallashinta.

   A hankali Jamilah take kokarin mamaye kome na gidan,har tasa Umma da yaran ta jin Haushina, gani suke kar ina cutar da ita, nice karama amma bani da kirki, haka yasa ni daina zama a gidan ta boye mugun halin ta, ta fito da na gari ana zaune lafiya da ita. Wannan dalilin yasani, tura mishi da sakon zan dawo Nijeriya na gaji da zaman nan din,shi bai san me ya faru ba, amma baki daya ya gama Yarda akan kawai ina kewar shi ne, dan haka ya ce min yana hanya.

   **
A yau aka fara saurarron shari’ar su Hannan da Na Maroko, Adizah, yar duwala.  Tare da tsohon ministan harkokin waje. Da wasu yan majalisar dokokin da na wakilai.

     Kuma Alhamdulillahi tare da shaidan da aka samu, yasa aka kama Alhaji Adamu Abbas Jikamshi, da Alhaji Abdulkadir Abbas Jikamshi, sai Hajiya Shuwa, itama ta samu damar shiga cikin case din, domin an samu bayani daga Hanan tace su suka bukaci ta shigo case din Alhaji Abdulkadir shi ya shigo da Jikamshi,  kotu ta basu zabin biyan magudan kudade,  ko zaman gidan Yari. Haka yasa babu shiri suka biya. Tare da manyan gidajen su duk aka karba. Hajiya Shuwa da Alhaji Adamu sune aka yanke musu zaman gidan Yari na har abada, sabida samun su da laifi masu yawan gaske. Taran farko na yaran da suka fitar ne,tara na biyu na yunkurin saka Jamilah cikin case din, tara na uku na kashe iyaye Mazan su Bilal tare da turawa a kashe su Bilal din hatsarin da aka yi. Sannan aka kwace kamfanin su.

      Bayan nan an kwace sauran abubuwan da ya zama mallakar su, kuma kotu ta wanke Jamilah. Sannan ta saka a rufe duk wasu abubuwan su Hajiya Shuwa a kamo mata Hilal.
“Alhamdulillahi, kome ya tafi da Yardan Allah saura kuma mu fuskanci abinda yake gaban mu.”

   Shima a nashi bangaren yayiwa Iyalan su adalci idan ya bar su, a Jikamshi Mansion, sannan suka nufi gidan Alhaji Muhammad Lawal, da maganar Rabi’atu. An karbe su hannu bibbiyu sannan suka kuma taya su murna na samun nasarar da suka yi kafin Bilal ya kai kokon baran shi na niman auren Rabi’atu.

   “Alhamdulillahi duk da ban ganta ba, amma a matsayina na abokin mahaifin du zance na baka ita, na baka ita Insha Allah sati me zuwa xan tafi har can muyi magana da iyayen ta maza, sannan ina kara bawa Wasilah hakuri naji labarin Abinda Alkasim yayi mata, tayi hakuri aure babu fashi a gaya mata”

    Shiru suka yi domin sun san Alman yana sonta.

   Haka suka dawo gida a jikin su a mace suka bawa Ummyn labarin abinda da ya faru.
“Da gayya kuka ki nima mishi auren ta bayan kunsan cewa yana son ta.”
“Sai yayi hakuri”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button