NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ok Sir” ya fada,
“Thanks” shima ya nufi gidan su, yana isa Rahmah dama sun koma gidan su ita da Faisal da Wasilah, yana shiga Falon Ummyn yaga Namir akan Alman.
“Assalamu alaikum,Lafiya Ummyn?” Ya tambaye ta matukar damuwa.
“Dan Banza ashe bai da lafiya har ya suma bamu sani ba, sai da Alhaji Muhammad Lawal Dambatta ya kirani akan Maganar Wasilah da yayi mishi kawai na shiga daki na hango shi dafe da Kirjin shi kasan shashasha ne”

       Sake baki yayi yana kallon Alman da yayi muguwar Rahmah a hankali ya ce mata.
“Ummyn ya ake ciki? Zamu bar shi ne ya mutu akan ta ko zamu nima mishi ita? Allah sarki Bilal da yana nan nasan ba mamaki zai iya yin wani abu” ya fada a matukar sanyayye. 

     “  Insha Allah babu abinda zai Faru,  Namir maza ka kira Asibitin JF Hospital” da sauri suka juya baki É—aya.
“Kai ya bakon da aka raka ya dawo”
“Ummyn a jikina naji.akwai matsala kafin muyi nisa naga sakon wannan dan banza” ya make kan Namir.

Ya kalli Ummyn sannan ta cigaba da cewa.
“Idan maganar wasilah ce, Inshallah yau za ayi ta baki daya idan yaso a hada bikin su da Rabi’a amma ba zamu zuba ido ya mutu da sonta ba, idan aka daura auren sai ki saka ido akan su” kallon Bilal Ummyn a ranta a ce.
A yadda Allah ya muku baiwar lafiya ne zan zuba mishi ido? Kowani nan ai dauke matar yayi ya ajiye sai da ya cinye rabin sannan ya dawo da ita

A zahiri kuma ta ce.
“Babu wani bikin da za ayi kawai ayi kome lokaci guda amma a ce daga bayan nan ba yarda ba.” Ta fada tana tsare su da idanu. Faisal ne ya d’ago dalilin haka, kunshe dariyar shi yayi. Motar Asibiti ne yazo aka fitar da Alman aka tafi da shi.

Babu wanda ya san da abinda Bilal zai yi kawai ua nufi gidan Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, suka yi magana. A take aka kira Me gari aka gaya mishi. Shi kuma Bilal ya tura har da kome su zo Jigawa gobe za a kawo su goben Insha Allah.

      Kiran Umma yayi ya gaya mata halin da ake ciki, shiru tayi kafin ta ce mishi.
“A daura auren kawai,idan yaso sai ba tura sai muzo jibi.”

Suna gama wayar ta kira kawar ta, domin akwai matar tsohon gwamnan Katsina, ita ta gayawa ta haÉ—a mata kayan aure, a shigo da shi nan da kwana uku. Kasancewar matar suna zaune yanzun a Swed mijinta an bashi Jakadar Nigeria a swed.

     Dake abu ne na kudi da kudi nera da bera, kafin kace kwabo an hada kome. Ranar Alhamis har an turo domin a can ɗin akwai shagon dan India nan yan Nigeria suke sayayyar kayan aure.

   Kayan Alman kome na Wasilah peach colour ne, yayinda kayan Rabi’atu ya zama kome special.  Haka aka sako kayan a jirgin sama. Ita kuma Umma suka tawo da su Rabi’atu da Jamilah, baki dayan su.

Babu wanda ya gaya musu labarin, sunan isowa aka shiga tura sakon auren ga abokan kasuwancin su Bilal, da ko ina bikin da ba’a sani ba, sai gashi yayyadu ko ina.

   Dole aka kai daurin Aure Saturday, ranar Friday aka yi Mother night, su kansu basu sani ba, sai da aka kawo musu kayan su da masu makeup.

           Kallon Rahmah Jamilah tayi jikinta yana rawa ta ce mata.
“Ramcy meke shirin faruwa?”
“Ban sani ba?” Ta bata amsa, haka shirya Rabi’ah da Wasilah,.suna cikin haka Faisal yazo daukar su.  Babu wanda ya kawo kome duk suka tafi, a babban Harabar JIKAMSHI HOUSE aka yi kome. Lokacin da aka shigo da su Yan jarida suka musu caa.

         Sai da aka fitar da wasilah ta shiga cikin, Ina cikin motar.  A hankali ya bude motar tare da kallona.

     Mika min hannu yayi, na fito a hankali ina kallon yadda aka mana caaa da Camera.
“Mr Jikamshi! A shekarun baya kace matar da zaka aura zaka bata kariya da dukkan rayuwar ka da zuciyar ka shin ya makomar wannan maganar?”

   Kallona yayi sannan yai murmushi ya cewa Yar jaridar.
“Ban goge shi ba yana nan har kwanan gobe” sannan muka wuce wurin da aka tanadar mana, sai da muka zauna naga katon hoton Ammyn. Sunkuyar da kai nayi, sai bayan mun nutsu aka fara abinda ya tara mu, inda aka fitar da kome a bayane. Ranar Ammyn,  tunda Ummyn ta fara bada labarin Ammyn nake kuka, na kasa magana sai kuka, d’ago ni yayi aka kuma mata addu’oi sannan aka cigaba da abinda ya tara mu.

          Kiran Bilal aka yi ya tafi tsakiyar taron, ya tsaya sai Alman shima aka kira shi can muna zaune aka kira mu. Kamar ba zan tashi ba sai na mike ganin yadda Ya Wasilah ta tashi. Muna isa wurin aka dauke wutar baki daya.
“Za a rufe idanun ku sannan za a baku damar duba mazajen ku” da sauri na Kalle shi.
“Miji?”
“Yes zan rufa miki asiri ne dan nasan kafin ki gama karatu kin tsofa”
“Na fasa kiran ka da Yeobo!”

“aigu uri aegi” ya fada yana kallona,
Wato yana nufin (oh my God, Baby) da korea. Banza nayi mishi ya kuma yin kasa na murya ya ce.
“Toh kiyi hakuri!”
“Na zata zaka cigaba da zagina ne da Yaren ku”

“Am sorry Naekkeo!”  Kallon shi nayi kafin nayi magana an kuna wuta, sannan Seyo tazo da wani farin kyale biyu ta mikawa wasilah daya, Ni kuma ta rufe min fuskana. Sannan ta koma wurin wasilah ta rufe mata. A hankali aka fara bayanin kowacce ta nimo mijin ta.

Kallon wurin Jamilah tayi, tsabar bakin ciki jini ke d’iga a hannu ta, sakamakon yanke hannun ta da tayi da wukar da aka tanadar domin cin abinci. Shiru nayi ina nazarin kamshin turaren shi kafin na bude idanuna a cikin farin yadin, na shiga matsawa a hankali. Sai da nazo gaban shi a hankali na furta.
“Sarangy”
“Me too Mine” wani irin cire kyallen nayi na gan shi durkushe yana rike da wani irin zobe me mugun kyau a cikin kwalin ta, rufe bakina nayi tare da fashewa da kuka, na mika mishi hannu ya saka min, yana saka min ya rungume ni.

       Itama wasilah daga baya ta sami Alman da baya jin dadin jikin shi, gashi an ki gaya mishi yadda aka shawo kan matsalar.

  Mimih ce ta zuba ido tana kallon abinda yake faruwa, kamar zata yi kuka ta ja kujeran da yake kusa da Jamilah ta ce mata.
“Mun gama shan wahala ita ta É—auke shi abinta kin ji sa’a da rabo”

    Lumshe idanun Jamilah tayi tana kallon wurin.
“Hm! Zan iya kome domin farin cikina bana fatar Rab’iah ta zama tashi har abada”

   “Me yasa?”
“Sabida nice na dace naji hannun shi akan K’uguna” inji Jamilah.
“Ni kuma rako mata nayi duniya da zan kyale ku? Idan har zaki iya raba tsakanin su ne yarda ki aure shi ba zo a ta biyu”
“Ina tsoron cin amana!” Inji Jamilah, murmushi Mimih tayi mata sannan ta ce mata.
“Nima haka” a hankali suke fadar abinda zasu shirya. Mikewa Mimih tayi sannan ta ce mata.
“Zan iya aikata kome idan na cigaba da ganin su a haka”

     Itama tashi Jamilah tai suka fito, suna canza kalamai. Wata yarinya ce ta fito daga motar Mimih suka rungume juna. Tare da sumbatar junan su.
“Hodayah ga Jamilah Ishaq,!” Ta nunawa Yarinyar Jamilah.
A yatsune yarinyar ta ce mata.
“Hello, Babu ina kewarki baki daya zan iya mutuwa idan ban kwanta a jikin ki ba”

   Kallon su Jamila take baki sake kafin ta samu damar tambayar Mimih.
“Are you a lesbians?” Murmushi Mimih tayi sannan ta ce mata.
“Idan na auri Gong Yoo zan daina” sannan ta wuce suka sakale juna, sannan suka shiga Motar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button