WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
     Gidan Alman suka nufa, tun daga bakin kofar shiga falon gidan suke sheka mishi kira, a matukar firgice ya fita da jallabiya.
“Don Allah Maman Deedat jeki duba ta don Allah nasan fyade na mata, wallahi ta kasa tashi” ya fada yana zubda kwalla.
  Dakin Rahmah ta shiga, taga yar uwar ta tana ƙoƙarin mikewa zaune amma ina sai ta koma ta kwanta, wani irin kuka me ban tausayi yana cin karfin ta.
“Sannun kin ji”
Cikin shashekar kuka ta ce mata.
“Ya Rahmah zoki duba ni, wallahi kamar ba a jikina ba”
“Eh zaki ji haka sabida bakon yanayin da kika tsinci kanki” ban daki ta shiga ta hada mata ruwan dumi, ba me zafi ba, shi sanjdai warware gajiyar jikin ta, haka ta taimaka mata tayi ta gasa jikinta sosai, sannan ta fito daga ruwan ta ce mata.
“Ki tsaya kiyi wanka wannan ruwan zafi ne domin ya fi wancan zafi zai taimakawa jikin ki”
   Gyada kai tayi haka Rahmah ta fita ta kwashe zanin gadon, ajiyewa tayi a kasa sannan ta nufi zuwa dakin Wasilah ta dauko sabon zanin gado, ta kawo dakin Alman. Ta kuma shimfida a dakin, fitowar Wasilah gwanin ban tausayi a hankali kamar wacce kwai ya fashe mata a cikin ta zo bakin gado ta zauna.
“Ko zaki koma dakin ki ne?”
“Eh” haka Rahmah ta taimaka mata ta koma dakinta, ta sauya kaya riga da zani na atamfar Super wax. Sannan ta fito ta samu tayi abin karyawa, zuba mata kunun alkama da tayi ta kawo mata dakin ta ce mata.
“Maza sha naso na kawo miki tea amma ganin wannan kunun hatsi ne zai taimaka miki sosai” baki daya ta shanye kunun sannan ta kwanta. Duba jakarta tayi ta ciro maganin zazzaÉ“i ta bata, sannan ta gyara mata kwanciya.
“Ƙarki mike kafa da kwanciya kina tashi ina gasa jikin ki, sosai sannan kiyi hakuri da halin shi wallahi haka suke basu da hakuri ta wannan bangaren sai dai ke kiyo hakuri da su, sannan zan mishi magana ta yadda ba zai kula ki ba sai bayan five days lokacin ciwon ya warke sosai. Ki kula da cin abincin sosai, sannan ko a cikin dakin ne karki sake kina yawo ba takalmi baki ga yan Korea bane ko masu aikin su Umma kullum da Safa a kafar su, a dakin su ne basu saka takami amma akwai na yawo a cikin dakin ai ki kula da jikin ki karki sake sanyi ya shiga jikin ki domin zai iya miki illar da baki zata ba, ki kula sosai.”
  Haka tayi ta bata shawara, sannan ta fito ta mishi bayani. Cikin tsannanin tsoron kar ya kuma aikata wani abu ya ce mata.
“Sati Daya ko? Domin shi zai taimaka jikinta ya warke da wuri Insha Allah, nagode don Allah kar ku gayawa Ummyn balle ta kwace min mata ta “
Haka suka bar gidan, suna kishi dariyar sabon shiga, har suka hau kan hanya dariya Rahmah take tana faÉ—in.
“Alman ashe haka yake da tsoro? Nace kwana biyar ya ce bakwai”
“Ba laifin shi bane ai, duk mutumin kirki idan ya mallaki dayar ku, dole ya girmama kan shi, ya kuma girmama ku, shi da yake matsoraci ai ba zai kuma kai kan shi ba, ni da nake jarumi ai sai da na dasa gwamantina a cikin kwanaki biyu. Kuma ta mishi gardama ne yasa shi kasa binta a hankali, kinsan irin su wasilah yan bin. A hankali ne idan ka matsa sai ka illata musu lafiyar su.”
“Haka ne”
*
“Humaidah kenan, Bilal yana sane dake ya barki ne sabida damuwar ba’a kike ciki, matukar kika ce zaki yi wani Hauka tabbas zai iya sakawa a kama ki a rufe ki na har abada. Kin gani nan,” hajiya Turai ta nuna kanta, sannan ta cigaba da cewa.
“Sanadin Nadrah na dauki darasi me yawa, dan haka zan zauna na rufawa kaina asiri, bana son na jefa kaina a damuwa” ta shi Hajiya Humaidah tayi ta tawo har gaban hajiya Turai, kafin ta kuma wani magana ta saka wukar da take rike da shi cikin rigarta ta yanke wuyar ta, tartsatsi jini ne ya wanke mata fuska.
“Duk wanda yayi yunkurin dakatar dani makomar shi kenan” sannan ta fita securityn din gidan ne suka fahimci abinda ya faru kafin tayi wani yunkuri sun saka mata bindigogi su, hakan yasa wasu suka duba Hajiya Turai ta mutu. Dole suka kira yan sanda. Aka tafi da ita.
Ummyn tana gida suna aiki Ita da Jamilah Faisal ya kirata, ya gaya mata babu shiri suka nufi can babban gidan a can aka mata jana’izar ta, Dole Irfan da Nadrah shigowa garin lagos domin suna can mahaifar Irfan ne Fika. Kuma wani ikon Allah ba karamin son Nadrah da Babyn ta suke ba, kuma shima yana da halin kwarai domin bai yarda da dangin mahaifiyar shi ba da na mahaifin shi duk abinda ya samu yana kawo musu.
Duk wanda ya gan shi sai yayi kuka sabida tausayin shi.
Haka suka bar garin zuwa Lagos idan ka ga Nadrah sai ka tausaya mata, karban Yar hannun ta Ummyn tayi sabida zazzaɓin da ya rufeta.
“Ki yaye yarinyar domin alamu ya nuna kina da wani cikin” wani irin kuka take tana faÉ—in.
“Idan na yaye ta waye zai rike min ita? Babu uwa babu Uba”
“Insha Allah zan yaye miki ita, karki dauka Turai ce kadai ta haife ki nima na haife ki….
3/18/22, 20:38 – My Mtn Number: 88
“Ba zan barki kiyi maraicin Uwa ba matukar kika dauke ni kamar mahaifiyar ki.” Wani irin kuka ne ya ci karfin ta, shi kan shi Irfan din tausayi ta bashi dan haka ya dauki Babyn ya ajiye a cinyar Ummyn sannan ya taimakawa Nadrah ta mike, suka fita daga cikin gidan .
  Da yamma Alman yazo, Ummyn na ganin danta ta fahimci ya shiga kwaryan manya, domin wani irin kunya da nutsuwa ce ta kama shi, tunda ya zauna ya kasa d’ago kai ya Kalle ta, koda ta tambaye shi Wasilah cewa yayi.
“Tana nan lafiya jibi zan kawo ta”
“Toh Allah ya kai mu” a hankali ta shiga mishi nasiha da tuna mishi amanar da ya dauka, har Rahmah da Faisal suka shigo. Sannan yayi musu sallama ya bar gidan. Ya nutsu sosai tare da kwantar da hankalinsa.
 A haka har aka yi addu’ar bakwai, daga nan Nadrah ta bar Yarta me kyau kamar iyayen a wurin Ummyn, ta koma gidan mijin ta, inda take fama da laulayi me zafi ga rashin uwa yasa ta zama wani irin, ciwon ya kuma karuwa.
  A can gidan Alman kuwa ya samu Wasilah kamar tuwo, ya hanata sakat. Haka zata yi ta kuka tana bashi hakuri, amma mayyen baya jin ta sai ya nutsu yake tunawa da tayi ta rokon ya barta haka, satin su uku ya dauke matar shi suka tafi honeymoon. Inda za a ci uwar Sabada (😂🤣)
 **
A gefen Mutanen Korea.
Umma ta saka ya mai dani part din ta, inda yq shiga kokarin nima min gida a cikin Seoul sabida makarantar da zan fara.
 Kayan gyaran jiki na Traditional Aphrodisiac, haka take hada min har da su Chocolate da markadadden Y’ayan itacce haka take bani, jikina kuwa wata mata ta dauko daga wani kauye can, ta saka matar tana min gyaran fata, ko ruwa ba watsa sai kaga yana wani irin watsewa.
    Kamar da wasa nayi wani irin kyau, har idan na zauna kama kamshi jikina yake, kwana ba bakwai ina shan wannan gyaran, kuma ban ji labarin shi ba ko a bakin Umma ashe yana can tayi mishi tas ne a kaina, shi kuwa yayi fushi ya tafi Russia kuma abinda take bukata kenan. A can ma dariya Thomas da Jessica suka yi ta mishi Solomon da Mansurah Abdul Salam, suka saka shi a gaba.
“Yanzun Sir akan Baby kake fushi kayi hakuri nan da sati biyu zaku haÉ—u” ganin zasu shiga masa kai da tsokana ya sashi.
  Dake yayi fushi ko kiran wayar su ba yayi.