NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Toh me zan musu?”
“Kawai ki gani ne,sun samu matsala ne har aka Kore shi a wurin aiki, ita kuma Yarinyar ta mishi sharri.”

“Allah ya kyauta, bani wayar ka na kira Auta bamu yi magana da ita ba wallahi.” Ta fada kamar zata yi kuka, murmushi yayi yana faÉ—in.
“Ban san me yasa kike jin haushina ba”
“Toh ni dai ka bani” idan ba haka ta mishi ba, Alman bai da hankali baki É—aya sai ya nime wani abu bai da aiki sai Yaren d’aga buje.

     Saka number da Rahmah ta turo mata tayi, ta gwada kira. A sanyayye taji muryan Autar su.

“Auta Lafiya?” A hankali ta sake mata kuka, ita Wasilah ta zata ko itama Jarabar Bilal ne ya buwaye ta. Ta fara dariya itama, ai kuwa Rabi’atu ta kashe wayar, abin mamaki sake kira tayi taki d’agawa, dan haka ta kira Rahmah tana gaya mata ga yadda suka yi da Auta.  Haushi maganar yabawa Rahmah.
“Banza kawai da kika ji muryar ta a sanyayye ba sai ki tambaye cikin natsuwa da damuwar jin sauyi ba, tunda aka yi auren su babu abinda ya hadu su bata da lafiya kamar yadda kike, bata da V!”

   “Innalillahi, tana da shi wallahi na manta ne ban gaya muku ba, akwai abinda aka ayi ne babu wanda ya isa ya kwanta da ita matuÆ™ar ba a kunce ba” ta fada tana kara musu bayani, ai kuwa Faisal ya kwace wayar tana tambayar ta. Ta masa cikakken bayani.

Sannan ta kashe wayar, turawa Rabi’atu wani sako tayi na ban hakuri da kuma rarrashin ta, sannan ta gaya mata karta damu ai ba wani abu bane, normal take zata yi lafiya.

Duk da Rabi’atu taji ta amma bata wani d’aga hankali can zata samu lafiya ba, domin tasan kawai Bilal yana zaune da ita ne domin hakuri ba wai dan yana jin dadin ta ba, nata ya kare ai sai dai a tari gaba. Wannan abin ya sa ta janye sosai a jikin shi, bata da amfani babu dad’i tana shige mishi.

   **
A can kuwa Lagos, Allah sarki Malam Faisal da kan shi ya nufi Jigawa, daga nan ya wuce Jama’are anan yayi Sallah la’asar a gidan malam wanda girma ya cimma shi. Zama Faisal yayi tare da cewa.
“Sannu baba”  murmushi Malam yayi sannan ya ce mishi.
“Yawwa Saurayi koda yake sai dai ace baban wane ko? Kai ne kuka xo gaisuwar bikin Yaran Harirah ai?” Gyara zama Faisal yayi ya kuwa kawo mishi bayanin da yake tare da shi.
3/19/22, 21:54 – Nuriyyat: 90

Murmushi yayi tare da kiran wani jikan shi a cikin gidan ya nuna mishi kasan randunan nan yasa aka hako wurin aka ciro layar, kad’e ta yayi bayan yayi addu’oi sannan ya farke yana cewa.
” Gudun kar tsautsayi ya fada mata yasa aka yi haka, ka bawa mijin ta hakurin abinda aka mishi.”

  “Babu kome baba” sun jima suna hira kafin ya ce mishi.
“Lokacin da Harirah tazo akan Yaran ta tare da wani yaro suka zo,  da a lokacin na fadawa Harirah wani abu ba zai iya faruwa da Yaran ya baki daya toh zata iya mutuwa tun lokacin ta bai yi ba, shi yaron ba zai auri Wasilah ba, idan a lokacin na fada mata ba zata yarda ba zata yi ta damuwa da halin da Yaran zasu shiga. Akwai abinda zaka iya yi domin ka hana wanda kuke tare damar ya rayu cikin salama da kwanciyar.” Sannan ya cigaba da cewa.
“Idan ka san abu kan mutum karka gaya mishi,ka saka ido lokacin zai gaya mishi, da aka yi hakuri ba gashi ta wuce ba. Shi kuma Yaron yanzun zai tashi a barci da yake, ka gaida Matar ka da mahaifiyar ka”

      Haka Faisal ya ajiye mishi kudi me yawa sannan ya mishi sallama.

Tun da ya bar gidan yake kiran Bilal sai ya dauka sai ya fashe mishi da dariya.
“Allah ya shirya ka” ya fada yana me kashe wayar tura mishi sako yayi tare a cewa.
Malam ango ja gwada Wallhi Ammyn ce tasa aka rufe ta toh an bude idan kana ganin karya ne ka gwada wallahi

**
Ya karanta sakon ya kai sau bakwai dan haka ya tashi a hankali ya nufi dakin, kura min ido yayi yaga ina kokarin shafa mai sabida fitowar da nayi daga wanka.

   D’aga ni yayi ya sake towel din, daga nan ya fara niman yi min abinda ya saba, na ture shi sake matse ni yayi sannan ya cigaba a haukace da zafi zafi yake bina, har ya isa ga gado.

      Wato hmm yau nasan da gaske aure ake,da kuma dalilin da aka ware wannan bangaren ga ma’aurata, nayi kuka nayi rokon Allah da ya bar ni kar ba mutu, amma ina bawan Allah nan kamar me jin haushina, sai da ta shiga yayi min kaca-kaca, sannan ya k’amk’ame ni a kirjin shi. Yana sauke numfashi, kallon  yadda na koma kamar bani ba, nayi masifar laushi.

        D’ago kaina yayi yaga siririn kwalla yana zuba a fuskana, sumbatar baki na yayi, yana faÉ—in .
“Nagode my Adorable Queen” idanuna a rufe, ina jin shi barci muka yi na gajiya a jikin juna, sai karfe biyu ya tashi ya haÉ—a min ruwan zafi, da kan shi ya kai ni ban dakin ya taimaka min nayi wanka, na gasa wurin sannan yayi shima sannan ya fito ya d’aga farin bessheet din ya shimfida wani, sannan yazo ya dauko ni ya kawo ni daki nayi laushi. Sai da ya kwantar dani, ya tafi kitchen ya kawo min Coffee me zafi da madara, ina sha ina gyagyadi domin barci nake ji sosai.

Ina gama sha sai barci,  magani ya kawo ya kuma d’aga ni.
“Don Allah ka barni nayi barci jikina ciwo yake”  maganin ya tura min da ruwa na sha, sannan yayi murmushi. Ya kwanta.  Duk ya gama rudewa ban daki ya shiga da zanin gadon ya wanke, sannan ya koma yayi wanka da alola, sai da yayi Sallah sannan ya kuma tashi na nayi alola, dakyar da kyar nayi sallah ina kuka, ina idarwa a wurin na kwanta.

     Haka wunin ranar bana iya cin kome dan bakina babu dad’i, sallah da ruwan tea kawai nake sha, washi gari ban ko iya moran jikina ba, haka  yayi matse ni yana rage zafin shi, sai da muka samu kwana biyar ganin har makaranta na tafi yasa shi ina dawowa ya daura na shi karatun, dama Umma ta gaya min, dan haka na yi matukar hakuri da halin shi dukda kuwa ana yi ina kuka ina yarfe hannu be hana shi karawa an jima, gaskiya Bilal fitina ne, shi yasa Mahaifuyar shi ta tsimma ni tasan danta.

   Bayan sati biyu nayi wani irin kyau da rama, ranar juma’a muka tafi Busan, tunda Umma ta gan mu haka ta fahimci danta yana samun kulawar da ta dace, da kanta ta haÉ—a mana abinci da ganyayyaki, muka ci ta bani salat na wulnut na ci yayi min dadi, ai kuwa sa daddare ba dan muna namu gidan ba da sun ji ihun Bilal. Kamar zai zauce. Washi gari ban shiga wurin su da akan lokaci sai da na makara, shima din na gudu ne dan ya buwaye ni gashi ana aiki a cikin gidan,ina zuwa ta tare ni da abinci sai da naci ba koshi ta kara min wani maganin da ina zaune na fara jin kamar abu yana yawo a jikina, a saba’in na gudu wurin mijina ina zan iya wannan halin banza (😂🤣🤔 ta rika) yana gani na kuwa ya wuce dani daki, domin Gong Yoo yasan karatun d’aga buje.

Ai kuwa ya jinjinawa Mahaifiyar shi yakai sau dari, ni kuma ya ce.
“Allah ya baki ikon hakuri da halina”

  Zan iya cewa ta wannan bangaren ni ma ina bashi haɗin kai, domin Allah ya bashi lafiya.

  **
Bayan wata bakwai. Labarin haihuwar Wasilah tare da bikin Ya Jamilah, haka muka tarkato zuwa Nigeria. Idan ka ganni da Bilal sai ka sha mamaki domin na kara girma nayi kyau kamar bani ba, haka aka yi sunan sati na zagayowa aka sha bikin Ya Jamilah da Yaya Aaman,  lokacin da Mammy tazo sunan Wasilah fada tai min sannan ta saka ni a gaba zuwa gidan su, anan aka saka ni gaba kamar yadda takewa Ya Jamilah gyara haka nima aka min, tunda ta dawo dani sai da ta tambaye ni ina da ciki na ce babu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button