NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

A motar shi ya gwada kiran Number Ummi mahaifiyar shi.
“Hello Ummi kin fito?”

“Eh gani nan.”
“Ok”

    Minti goma sha biyar ya kai shi airport din, inda ya  ga abin mamaki. Domin dangin mahaifiyar shi ne a tare, dan haka suka wuce inda zaa saka gawar Ha Na, ana gamawa suka nufi cikin jirgin, wuri na musamman suka keb’e shida mahaifiyar shi, ya zuba mata ido.
“Ummi kin ci Abinci kuwa?”
“Eh toh na tab’a kad’an dazun.”  Mikewa yayi yaji ana sanarwar kowa ya zauna a cikin jirgin ya daura belt,shima zama yayi ya daura belt din, yana kallon mahaifiyar shi. Sai bada jirgin ya tashi sama sosai sannan ya cire belt din ya nufi cikin jirgin inda ake girki ya basu umarni a kawo abinci da abin sha. Kafin ya dawo wurin zaman shi.

Bayan minti biyar aka kawo abin shan nan babu wanda ya amsa, domin kowannen su bai yarda da dan uwan shi ba, shi daga shi sai Ummin shi suka ci abincin.

**

Karfe daya na dare suka isa airport na Busan, sun samu security kaca kaca. Dan haka suka nutsu.

Ko ina ana sane da zuwan su, kasancewar Kakar Ha Na babban mutum ne a garin mahaifin ta kuma shugaban garin ne baki daya kamar a ce gwamna.

Manyan motar alfarma aka kawo suka kwashe su, yayinda aka nufi gidan Mrs Kim Eau Jikamshi. Babban mansion ne da ya amsa sunan shi, gate biyar ne a cikin gidan, kafin ka isa gidan, dayawan su basu tab’a zuwa Busan ba, amma Hajiya Atikah ita kamar gida ne a wurinta domin bata wata uku me kyau bata zo wurin Kim Eau Jikamshi ba,. Suna fita a motar suka fara haduwa da hoton Ha Na, gwanin ban tausayi mahaifiyar Ha Na da Mahaifinta suka amshe su, duk da Yayun ha Na maza biyu.

Dook Jom Sa  da Mim Yop Sa, haka suka musu iso har cikin gidan, abin tausayi. Sun samu Kim Eau tana zaune ta saka hoton Ha na da Yaronta a gaba tana kuka. Da sassarfa Hajiya Atikah ta isa gare ta, suka rungume juna. Gwanin ban tausayi suna kuka.

“Yaushe Gong Yoo zai farin ciki a rayuwar shi Atikah? Na zata idan na kwashe Yarana na bar Ahmad da dangin shi Gong Yoo zai yi farin ciki, ashe hasashe na ce ba ta sauran jama’a ba, an kashi Biyoden an kashe Salmah yau kuma Ha Na da yaron da bai ji ba bai gani ba, laifin Gong Yoo da bai isa ya ajiye iyalin shi ba? Idan dan mallakin shi ake wannan rigimar ba zai koma ba, ya zauna anan ina son shi ba zan tab’a sakewa yayi rayuwa me cike da kunci ba”

Ta fada tana kuka kamar yarinya karama, shigowar wasu yan mata biyu, kyawawan masu yanayi da hausa fulani.

      A hankali suka fito daga dakin suna masu gaida yan uwan mahaifin su cikin jikakkiyar yaren Hausa da bata kama harshen su ba.
“Ya hakuri kuma?”
“Alhamdulillahi”  suka koma gefe babban ta dauki kwalin tissue ta mikawa mahaifiyar cikin tausayi ta ce.
“Um Ma! Ki daina kuka mana, Kiyi hakuri mana Allah yana tare da masu hakuri”
“Seyo Na yaushe zan daina kuka bayan rayuwar Bilal ake kashewa” matsowa karamar tayi itama tana kuka.
“Um Ma.”
Riko hannun ta tayi tana faÉ—in.
“Meye NaNa?” Kwanciya suka yi a jikinta suna kuka. D’ago kai Seyo Na tayi tana kallon Mahaifiyar su ta ce.
“Um Ma, Oppa bai iso bane? “

       “Ina kyautata zaton yana hanya ki ma ya iso, tunda ban ga Faisal ba suna tare da juna. Ki kira Lim shin ta kai bakin nan Apartment din baki da yake estate din nan”

Mikewa ta tare da nufar cikin gidan, can sai gata tare da wata mata wacce ba zata wuce shekara arba’in da bakwai zuwa da takwas.

    Cikin  girmamawa ta gaishe su, sannan ta ce musu.
“Zamu iya tafiya.”

Babu musu, suka bi bayanta sai dai Hajiya Atikah da suka barta a wurin Kim Eau Jikamshi, Sabida sun jima basu hadu ba, sarkafe hannun juna suka yi tare da kallon juna.
“Kim Eau! Nasan yadda kike ji? Domin abinda ya same kamar ni ya sama dan haka Kiyi hakuri ki danne kome..
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:51 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny
Na
Mai_Dambu
LITTAFINA NA KUDI NE DON ALLAH IDAN KIN SAN ZAKI SAYA KI FUTAR MIN DON ALLAH DA GIRMAN SHI KI BAR MIN ABINA DON ALLAH BANA SON RIGIMA IDAN KIKA FUTAR MIN DAN KI B’ATA MIN HMM AKWAI Allah

Wata tafiyar<11>

D’ago kai tayi tana kallon ta, kafin ta iya bude baki ta ce.
“Yaushe Atikah? Yaushe Bilal zayi farin ciki? Zan cigaba da kallon shi ne yana bakin ciki haka kawai? Hmm zuciyata ta fara kangarewa, idan na fusata za..”

      “Ai shi yasa bana son ki fusata, kiyi hakuri lokaci yana zuwa da kina daga nan zaki yi dariya, Æ™arki manta nima ina da buri naga Faisal ya bi kaddin mahaifin shi haka kawai ba zan zuba ido kome yana tafiya haka, sannan idan kika ce zaki dauki mataki kamar kin kashe mishi kwarin gwiwar shine,ki taya shi da addu’a. Allah yana tare da mu.”

    Mikewa suka yi a tare, suka nufi cikin gidan. Inda suka haura sama. Wani luxurious farlou suka wuce iya haduwa farlon ya haɗu daga paint din farlon zuwa sofar farlon ya amsa sunan shi, domin kome na falon dark purple ne hatta sofar, ga wani katon hoton frame da aka kawata farlon da shi, sai wata cinema da ya cika wall din farlon.

            A hankali suka nufi wasu dakuna,manyan manyan guda biyu daya an rubuta BAJ,dan kadan rubutun an yi bracket an saka (Gong Yoo Jikamshi) bude daya kofar tayi nan ma wani part ne me ɗauke da wasu unique farlou, kome na ciki cream colours ne,  hoton Ha Na da danta ne a falon, kafin sukayi yar tafiya mara tazara kafin suka isa kofar dakin, a sanyayye suka shiga cikin dakin. Wow kome na dakin light blue ne me ɗauke da wani irin yanayi me daukar hankali, wani tabkekken gado ne Hajiya Atikah ta nufa da yake cikin dakin kwali daya. Sai wasu manyan labulen da suka kara haukata tsarin dakin.

     Zama Hajiya Atikah tayi tana kallon Kim Eau.
“Amma ya kamata Alimah da Amilah su yi aure sun girma fa, dan ba yara bane yanzu a sanina Alimah shekaru ashirin da takwas tana niman talatin, Amilah kuma Ashirin da biyar, ki duba mana idan da mahaifin yana raye kin san da ana maganar auren su ne ko”

    “Yanzun ba tasu nake ba, ta Yayan su nake dole na fara kashe matsalar shi kafin nabi tasu.” Ta fada tare da nufar waje, tana cewa.
“Ki shiga ban daki akwai kome nasan ba zaki bukaci abinci ba, amma zan gayawa  Lim shin ta gabatar musu da abinci idan ba zasu ciba su tafi ko ina su ci.”

      Jikin Hajiya Atikah ne yayi mugun sanyi, domin tasan dabi’ar su ce, basu cika yarda su ci abincin junar ba, gani suke kome kashin sakacin da zasu tabbas mutuwar su zasu ci, kuma duk abinda yake faruwan nan iya mutum biyar aka kashe ta ma bambanta yanayi. Shi yasa ko wani wurin zasu hadu kowa tsoron kar dan uwan shi yazo da mugun nufi ne.

“Baki tambayi Shuwa ba?” Cak Kim Eau ta tsaya, kafin ta juya tana me hard’e hannun ta a kirjin ta.
“Tunda bata zo ba ai nasan har yanzun kishin Ahmad yana ranta, bayan duk abinda zata samu saura na ne” ta fita tana murmushi.

    Girgiza kai Hajiya Atikah tayi tana kallon bayanta, ban daki ta shiga, ta jima a cikin ban dakin sannan ta fito, wanka tayi tare da alola, sannan ta gabatar da sallah kanta, tana zaune har kusan asuba ta tashi ta gabatar da sallah nafillah, kafin ta daura na asuba. Tana idarwa ta kwanta a wurin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button