NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

      Yaran baki daya sun saje da Familyn Jikamshi, ba zaka tab’a zata agololi bane, domin Alhaji Ahmad ya rike su kamar shi ya haife su. Suna shigowa suka mike kafa suna zuba iskancin su, dama Kim Eau bata ma kasar, Gong Yoo da ya ke nan baya shiga harkan su, domin dawowar shi Mahaifin shi yake kokarin bude mishi kamfanin shi na kanshi, wani abu da Gong Yoo yake alfahari da shi ne, yana da Masifar zuciyar nima, tun yana degree din shi ya bawa mahaifin shi shawara ya inganta musu jirgin ruwan shi, domin yana son idan ya gama karatu ya dawo ya bude kamfanin tafiye-tafiye wacce zata yi gogayya da manyan kamfanonin tafiye-tafiye na duniya.

A gefe guda suka kuma hada gwiwa da mahaifin shi wurin bude kamfanin sarrafa karo da wasu karafuna ana kaiwa Austria, china, Japan da Jamus. Wannan dalilin yasa aka bude Jikamshi Iron and  Mineral Resources,  sai na tafiye-tafiye inda aka bude Jikamshi international Transportation, duk wani tafiya da ta shafi manyan motoci zuwa wasu kasa shi da suke makotar Nigeria, ana samun motar kamfanin Jikamshi, dama suna da jiragen ruwa biyu masu dauko kaya, Allah ya taimaka shima ya gaji Mahaifin shi sai gashi Kakar shi na wurin uwa ya bashi wasu manyan kudade, babu shiri ya kara da na hannun shi da mahaifinsa, ya kara musu jirgin.

Hajiya Shuwa bata san ana wannan bidurin ba, sai lokacin da za a bude Jikamshi Family GRP, anan ne abin ya bata mamaki domin tasan akwai wanda suke na kasuwancin dabbobi, ashe akwai wani dan haka, ta fito ta kalubalenci Alhaji Ahmad abinda ya bashi  mamaki tunda yake da kim bata taɓa cewa akan me zai yi kaxa ba,akan me zai yi kaza. Toh wallahi ya kiyaye abinda zai faru gaba. So bai dauka wani abu, ba domin yasanta da zafin rai.

   Dan haka bai yi tunanin gayawa kowa ba sai Alhaji Abdul Hadi Shema, shine yasan abinda da ya faru, Washi gari a masallaci suka hadu da Alhaji Adamu, ya mishi magana.

“Kamfanin da na budewa Bilal ba nawa bane, domin kakan shi ya bashi kudi da ya bude kamfanin kafin nan ma Bilal yana niman kudi ba haka kawai yake zaune muna mishi hidima ba, dan haka naso na gaya mata tayi hakuri nima ba nawa bane kuma kudi na da yake cikin kamfanonin Æ™alilan ne idan na cire Kamfanin jiragen ruwa iya sune muka yi hadin gwiwa taki fahimta, tunda nake da Kim Eau bata taÉ“a samun idanu akan. Abinda zan yi ba, asalima kokari take taga na kyautatta mu’amalata da kowa, Amma ban da Murjanatu kome lallai sai dai ya zama a kasan ta. Ni kuma mutum ne da nake da ra’ayin kaina.”

A wannan lokacin hankalin shi ya tafi ga abinda yake ganin shi ne mishi dai-dai, Allah kadai yasan dai-dai domin bayan an bude Kamfanin Bilal da wata biyu, aka harbi Alhaji Ahmad tare da Aminin shi Abokin shi mijin Kanwar shi, haka aka kashe su har lahira. Duk yadda Bilal da Faisal suka so sanin abubuwan da suka faru babu wani labarin haka suka hakura suka sallamawa Ubangijin al’amarin, dan haka Hajiya Atikah ta cigaba da tsaya musu kasancewar tayi zurfin karatu addini da na zamani, wanda haka ya saka mata wata irin kwarjini  da cikar kamala. Ita take kula da Yaran har zuwa lokacin da Bilal ya watsar da lamarin kamfanonin shi yayi tafiyar shi Korea.

     Kamar ba zai dawo ba kafin Allah ya taimaka sai gashi nan ya dawowar shi ne, yana dawowa ya farfaɗo da kamfanin shi, bayan haka ya shiga Niman kasashen da zasu zuba hannun jari a kamfanin shi, wannan dalilin ne ya tafi har Somalia, ya hadu da Muneebah, model ce kamar mayya tunda ya ganshi ta Hauka ce kamar me dan haka suka fara kokarin shimfida soyayya duk da ita bata so soyayyar ya tafi haka ba, sai dai shi ya amshi ta a matsayin matar shi babu yadda ta iya haka Manyan suka shiga maganar su, itama babban abin alfahari ne a wurin ta, dan haka lokacin ƙalilan aka saka aka sha bikin su. Inda suka shiga zuba soyayya me ɗauke da kaunar juna.

Domin ana bikin ya dauke ta sai Korea a can aka yi honeymoon, na tsawon wata biyu, kafin ya dawo da ita. Tunda suka dawo ta fara fuskarta wasu abubuwan masu mugun daure kai. Da farko idan ta zauna zata ji kamar ana tab’a kofar ta, idan da zata duba ba zata ga kowa ba, bata dauki haka a matsayin wani abu ba, sai da aka fara idan ta ajiye abu sai a sauya mishi wurin zama, sai ta fara kokarin gaya mishi. Ranar suna shirin kwanciya ta kalle shi kafin ta ce mishi.

“Baby gidan nan fa akwai wani abu da yake cikin shi wallahi babu halin na ajiye abu za a sauya mishi wurin zama, idan kuma ina daki ko ina barci za ayi ta buga.”

Domin ya kashe maganar sai ce mata tayi.
“Kin ga zo nan it’s was Imagine ba wani abu bane domin babu kome a cikin gidan nan na razanarwa kece kawai baki sake ranki kin fi son Korea da nan “
Zama tayi tana kallon shi…..

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:52 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny
Na
Mai_Dambu
BUZHUWA Emphire🐪🐪
Assalamu Alaikum,Barkanmu da wannan lokacin ,Sannun mu da shigowa Halarar mu na buzaye.... Albishirin ku matan Aure💃💃💃 BUZUWA EMPIRE ta taho maku da sirrika na MALLAKAR mijin ki yar uwa a hannun ki ba tare da boka ko malam ba. Matan da yawa na fuskatan matsalolin su da maxajen wato kalubalen a gidan auren mu...kuma irin wannan maganin matan Asha tabaje...mene wani shirme wani gayinan dai ,bashi ne ba... Ina macen da daga zarar mai gida yy sallama gaban ki keda yara ya hau fadi?. Ina macen da mijin ta kullum idanun shi na akan matan banxa?. Ina macen da ga kudin mijin yanada amma babu ci sai dai duniya suci yy kyautan riya? Kai duk wani matsalan ki na gidan Aure kizo taskar BUZUWA EMPIRE. zata baki mallaka ta hanyar sirorin kur'ani da dai sauransu. Mallaka ta hanyar kwai Mallaka ta hanyar nama ,madara ,kifi , yan shila da dai sauran su.. Ga kuma mallaka ta hanyar suratul yusuf . Mallaka ta hanyar jauhara. Mallaka ta hanyar Yaseen Mallaka ta hanyar fatiha umul qur'an. Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su... Ina Yammata marasa farin jini ?💃 Kuzo kuma da naku ,sai kaji ana gata mummuna baka kirin amma sai farin jinin manyan alhajazai masu jifa jifai kome take dashi oho..!! Kuji ita tasan inda tazo ta taho taskar BUZUWA EMPIRE . sai kin taho yar uwa gaba daya sirrin nan na farin jini dana mallaka 5k ne duka . Idan kuma mallaka ne kadai munayin na 2k da kuma 3k. Na farin jini kacal 3k ne ,gamasu bukata zasu tuntu6a wannan number 08081202932/09061466409.

Ana dara!<13>

Tana kallon shi idanun  shi tayi, kwalla ne ya cika idanun ta, rike hannun shi tayi tare da cewa.
“Ina son ka fahimci yanayin yadda nake ciki, ba kome bane yake imangination ba, ba kome yake zama haka ba, Bilal wani abu yana faruwa   cikin wannan gidan ka fahimce ni.”

      Matso da ita yayi tare da rungume ta a jikin shi yana kallon yadda take zubda kwalla.
“Shi kenan gobe Insha Allah zan saka a zo a duba al’amarin.”
“A’a ina tsoron wannan yanayin, mu duba da kai sabida kana fita kome yake faruwa”  a hankali ya janye zaren rigar barcinta, wadatattun kirjinta suka bayyana, cikin wani irin yanayi ya kifa kan shi,daga nan aka shiga shagali.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button