WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  **
Tun da dare da ya ga ta samu barci ya juya ga aikin shi, a daren ya turawa Faisal sakon abinda yake faruwa, take ya turo mishi da cewa. Ya dauke ta su bar gidan shi da masu aiki zasu zo gyara gidan, haka kuwa ya faru.
Washi gari suka fita, Faisal da masu aiki suka shiga gidan,Dakyar da sidin goshi aka samu wasu camera har guda biyar, daya a falonta daya a falon shi, daya a kitchen sai sauran a cikin dakunan abin da suke zargi ma an san da zuwan su gidan kenan tunda wurare masu muhimmanci daban daban an same su, haka ya sa Faisal ya kira shi tare da mishi bayanin halin da gidan shi yake ciki, dole ya hakura da wannan gidan ya ko daya daga cikin Apartment da yake bakin estate din da ita, sai dai wani abinda basu sani ba, wanda yafi kason abin ka, yafi ka dabara dan haka sai da aka cire kome na gidan aka sauya sabo, sannan suka dawo a lokacin ta fara laulayi me mugun zafi.
Dan haka har gida likita yake zuwa zuba ta, wani ikon Allah idan ka gan shi da matar shi ba zaka zata zai iya biye soyayyar shi ba, ko bai iya bane oho amma tabbas babu wani abinda mace zata nuna cewa miji yana ji da ita, samuwar cikin Mubeenah ya haifar mata da wasu tashin hankali, wanda ta daina ko barci matukar baya gida toh bata iya barci sai da wani domin yadda ake shirin haukata ta yasa ta zama kamar mahaukaciya, ga me ciki da barcin jaraba. Amma ita babu halin domin ko tayi tashinta ake da buge buge da motsi, dalilin da yasa bata samun barci sai idan yana gida.
   Haka ce ya faru da Ita, ta gaya mishi bai wani dauki mataki ba, sai ma tsiro da Masifar da yake mata akan bata da hakuri so take ya kare a gindin ta, wannan abin ya bata haushi dan haka ta tafi gidan Hajiya Atikah ta gaya mata, dan haka ta same shi ta mishi magana,da farko ta zauna har ya kashe zaman office ya bude office a gidan shi domin Hajiya Atikah da suke kira Ummi. Gaya mishi tayi.matukar ya cigaba da b’ata mata rai zasu iya rasa babyn cikin ta, wannan ya sashi tattara kome ya tara a gefe.
   Watan cikin jikinta hudu, wata Alhamis da ya shiga cikin kundin tarihin shi, suna zaune da ita a cikin deep down pool da yake cikin gidan su. Dan ta falon shi ake shiga, aka kira shi a waya, ba wani waje ya tafi ba a cikin gidan shi ne ya fita wayar abin mamaki yana dawowa ya samu fa ta sha ruwa ta koshi, ga wuyar ta da aka saka abu aka shaketa, wannan abin ya firgita shi domin kasa motsi yayi ya kira Faisal yana salatin,. Lokacin da yazo shida Khalil, sun tausaya mishi domin baki daya ya kasa magana ta kasa kome, idanun shi yayi jajjur sai kaduwa yake, kamar wanda aka watsa mishi ruwan sanyi kalau, haka ya suturta jikin ta, tare da kiran motar asibiti, kasancewar ita din da iyayen ta da mijinta sanannun mutane ne yasa take mutuwar ta ya zaga duniya, abin tausayi haka aka gama bincike abu daya aka samu Shine kashe ta aka yi, domin ga alamu a wuyarta.
  Koda suka dawo gida aka mata jana’iza iyayenta suka ce kar a kai ta a bari su zo, babu yadda suka iya haka suka jira har suka zo aka yi sallah ta, sannan aka kaita gidanta na gaskiya, ana cikin wannan a gidan Bilal din ana bincike ta CCtv camera, amma babu wani labari, haka dai aka gama .
Idan ka gan shi a lokacin sai ta baka tausayi domin kuwa baya uhm balle humm, haka ya kara mai dashi wani miskili mara kirki baki daya, ya zama kamar monsters abin tausayi, baya cika magana sai da Faisal da Khalil sai ko mahaifiyar shi da Hajiya Atikah, baya ma ta Hajiya Shuwa, balle yan uwan Baban shi baya ma ta kansu sai,
  Ana cikin wannan yanayin Bioden ta matsa mishi tun daga ranar da ta ganshi a wurin bude wani taro, ita kuma Yar jarida ce, tun da ta addabi rayuwar shi, haka yayi ta mata wulakanci da koranta a jikin shi q..a bata fasa makale mishi ba, karshe haka aka yi maganar auren su, amma bai tab’a sonta ba ko kaunarta yayi hakan ne domin yadda take makale mishi ya zab’i ya kyautatta mu’amalar shi da ita ta hanyar aure.
  Hmm har gwara Muneebah ita kashe ta aka yi, amma ita guba aka saka mata, kuma da karamin ciki a jikin ta. Haka ya fusata shi har ya ce sai ya kore kowa a cikin estate din shi. Domin duk wani binciken da ake babu wani abu labari. Haka rayuwa tayi ta garawa da shi, babu wanda zaka gani kace yana da hannu a cikin kisar,. Lokacin Abdulkadir yana Yemen yana jakadanci a can,baya ma nan balle a ce shi yana da hannu a cikin kisar, sai dai ana zargin wasu amma sabida babu shaida yasa aka jingine kome.
 Sau tari yana yawan zargin kan shi abisa laifin mutuwar matan shi har biyu, yana cikin dalilin da yasa baki daya yaki maganar aure, haka ya kuma d’agawa mahaifiyar shi hankali domin atufar yaki maganar aure, sai da Ha Na ta ganshi itama ta nace, babu yadda Mahaifiyar shi bata yi ba dan kar a fasa auren, amma ina alkalamin Æ™addara ya gama zanata a cikin zanen Æ™addaran shi. Toh itama ta shiga sawun sauran matan shi da aka kashe su.
A dawo labari.
Garin Busan yau an tashi da hadiri, garin yayi wani irin lum. Ta kowane fanni ka duba ya bada wani irin yanayi ne na musamman, zai yi wuya ba a sake ruwan sama me karfin Bala’i ba, Mr Park Yun, yana tsaye sanye da bakaken kaya, duk da ya tsufa amma haka ba zai hana ka hango kyakkyawar kulawar da ake bawa fatar shi ba, domin na zaka kawo shi ya Haifi Kim Eau. Baki daya suna tsaye ne inda ake binne gawar Ha Na, hawaye na zuba idanun mahaifiyar Ha Na.
     Kowa a wurin yana dauke da lema, domin ganin yanayin garin da alamar ruwan da yake shirin farkewa, motar Audi Q1 ce sai Benz A3, suka shigo makabatar a hankali, tsayuwar motar yayi daidai da sake wata irin Chida me karfin gaske tare da sake ruwa me nauyi sosai, haka ya sa kowa ga bude leman shi, da sauri escort din da suke bin motar shi suka fito, tare da bude mishi kofar motar bayan sun bude lemar da zata kai su har wurin da ake rufe gawar matar shi da dan shi.
Yana fitowa a hankali, fuskar shi babu glass kamar jiya. Gyara zaman kayan coat din shi yayi yana kallon gefen shi yayi, Faisal ne a damar shi. Daya gefen kuwa Khalil ne rike da lema, shima bayan shi ana bin shi da lemar, hannun shi daya yana cikin Aljuhun wandon shi,daya hannun yana sake sa ita, a hankali ya lumshe idanun shi. Ya bude akan Baffan shi Dr Abubakar Abbas Jikamshi, sannan ya dauke kanshi zuwa wurin Hajiya Turai da Humaidah da suke sanye da bakaken abaya sai bakin madubi da suka saka a fuskar su, dauke kai yayi ya dire akan Alhaji Adamu,. Kafin ya sauke akan Hajiya Atikah, da mahaifiyar shi. Yana zuwa inda ake jiran shi ya É—ibi kasa ha zuba akan akwatin Ha Na, sannan ya koma kan dan shi wanda ya zuba mishi, kafin ya koma gefe ya haÉ—e hannun shi a biyu ya tsaya, kowa ma haka yayi qka gama addu’a, sannan aka rufe ta, har suka watse amma shi bai watse ba, baki daya abin ya zame mishi kamar a mafarki mace ta uku ya binne, matar shi uwar dan shi.
   Har aka watse yana gaban kabarin su, a tsaye yana kallon su.
“Bilal muje” sai a lokacin ya d’ago kai ya kalli Faisal, da yake tsaye shima cikin damuwa.
Lumshe idanun shi yai a karo na biyu, sannan ya bude akan shi. Ya d’an juya kadan yana kallon wurin motar su, kafin ya ya juyo ya kalli kabarin matar shi da Dan shi, kafin ya sauke ajiyar zuciya. Tunda aka fara kashe matan shi bai taba magana sama da ayi bincike ba, sai dai yau ya kasa magana ma ayi bincike tabbas me kashe mishi mata ba haka kawai yake haka ba, ba dan kudi ko suna yake haka ba, akwai manufar shi na musamman, idan da shi ake bukata toh ba makawa da an jima da kashe shi.