NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

    Idan ya ce zai zurfaffa binciken hmm zai iya tono abinda da zai dame shi, yana ganin ya yanke alakar shi da duk wata halittar  mace da zata shigo rayuwar shi, idan ba haka ba zai yiwu ko da wasa ya nime aure a kashe yarinyar kafin ta shigo rayuwar shi.

(Wow Masha Allah hmm labari nan a dankare fa mallaki naki a 300)

Jigawa. Nigeria
Daƙayyawa

Da sassafe sai ga Gwaggo Lami, ta daka musu sammako, basu bude dakin su ba, ta buga musu. Zuwa tayi ta rufe Rahmah da duka tana faÉ—in.
“Yar iska wato shine zaki je kidauko min su, masu mugun hali ku kam kun shiga uku, dan haka maza tashi ku tafi.”

“Wallahi Gwaggo bani na dauko su ba, dawowa suka yi nima anjima zan tafi asibiti wurin Ammyn mu” inji Rahmah tana kuka,

“Ku kuka sani idan kun gadama ku cigaba da karuwancin ku can ta matse muku.” Ta finciko hannun Rabi’ah,

Da gudu Wasilah ta dira a gadon tare da fita, ta bar gidan ana kiranta amma fir yarinyar nan taki dawowa, dole ta saka Rabi’ah a gaba suka tafi gidan ta, domin ta san Rahmah asibiti zata tafi, basu zame ba sai gaban kashin kunun koko, wanda aka zuba a wasu kananan robobin kunu, ko wanke idanu yarinyar nan bata samu yi ba, haka aka daura mata tallar ta fita.

Dama gata a firgice lokaci guda ta zama abar kyama a wurin mutane, ko fuskarta bata wanke ba, dan sun makara sakamakon farkawa da tayi tana kuka da firgita. Abin da ya hana su barci da wuri har wurin asuba, sai da Rahmah ta kuma kunna wutar dakin ganin haske ya sata makale kanta a jikin Rahmah tana sauke ajiyar zuciya.

    Domin bata son duhu ko kaɗan. Hakazalika zaman ta a wurin Mutane, ya haifar mata da wani irin tsoro dan haka ta koma gefe da kayan kunun har wajen karfe takwas bata sayar ba, domin idan ma saya Zakaria kuka take saka maka, wani irin tsoron mutane da tashin hankali take  shiga, domin gani take kamar baba Haliru ne yazo wurinta wannan yasa baki daya ta koma kamar mahaukaciya, tana kuka da ihu, dan haka babu wanda ya sayi kunun haka aka bar ta har karfe sha biyu, sai ga Bahari dan bana Haliru.

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:52 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR..!
The Beginning of Destiny
Na
Mai_Dambu
EWF…

BUZHUWA Emphire🐪🐪
Assalamu Alaikum,Barkanmu da wannan lokacin ,Sannun mu da shigowa Halarar mu na buzaye.... Albishirin ku matan Aure💃💃💃 BUZUWA EMPIRE ta taho maku da sirrika na MALLAKAR mijin ki yar uwa a hannun ki ba tare da boka ko malam ba. Matan da yawa na fuskatan matsalolin su da maxajen wato kalubalen a gidan auren mu...kuma irin wannan maganin matan Asha tabaje...mene wani shirme wani gayinan dai ,bashi ne ba... Ina macen da daga zarar mai gida yy sallama gaban ki keda yara ya hau fadi?. Ina macen da mijin ta kullum idanun shi na akan matan banxa?. Ina macen da ga kudin mijin yanada amma babu ci sai dai duniya suci yy kyautan riya? Kai duk wani matsalan ki na gidan Aure kizo taskar BUZUWA EMPIRE. zata baki mallaka ta hanyar sirorin kur'ani da dai sauransu. Mallaka ta hanyar kwai Mallaka ta hanyar nama ,madara ,kifi , yan shila da dai sauran su.. Ga kuma mallaka ta hanyar suratul yusuf . Mallaka ta hanyar jauhara. Mallaka ta hanyar Yaseen Mallaka ta hanyar fatiha umul qur'an. Mallaka ta hanyar turaruka da dai sauran su... Ina Yammata marasa farin jini ?💃 Kuzo kuma da naku ,sai kaji ana gata mummuna baka kirin amma sai farin jinin manyan alhajazai masu jifa jifai kome take dashi oho..!! Kuji ita tasan inda tazo ta taho taskar BUZUWA EMPIRE . sai kin taho yar uwa gaba daya sirrin nan na farin jini dana mallaka 5k ne duka . Idan kuma mallaka ne kadai munayin na 2k da kuma 3k. Na farin jini kacal 3k ne ,gamasu bukata zasu tuntu6a wannan number 08081202932/09061466409.

Son zuciya.. <14>

Yana isa wurinta ya kalle cikin mugunta, ya ce mata.
“Tashi ki kai mata kayan ta, tunda bai kare ba.” Kamar saukar aradu ta ji muryan shi, abin tausayi haka ta tashi jikin ta yana rawa ta dauki kayan, tana tafiya tana tuntube, haka kunun ya zube, bai fasa bin ta ba har suka shiga unguwar su, kasancewar rana tayi dan ana niman karfe daya na rana, ya sha gabanta tare da saka mata kafa ta fadi, jin Haushin abinda aka musu na rufe musu baban su, yasa shi dukar ta, kamar ya samu babban mutum. Ganin duk dukar da yake  mata, tana takure wuri guda jikinta yana rawa yasa shi kwallo da ita, ya tafi ya barta a wurin.

      Tsoron kamar yana tsaye yasa bata iya d’ago kai ba tun sha biyu da arba’in take wurin har karfe biyu na rana, duk rashin imanin mutum sai ya zubda kwalla domin a tsora ce take. Haka dai aka samu wanda suka iya mata magana aka kwashe mata kaya, da gudu ta dauki tiran ta kwasa da gudu sai gida, duk ya fasa mata baki, tana shiga cikin gidan tayi tozali da Gwaggo Lami da Nairah, sosa kanta take tare da kallon gefe da gefe, kamar mahaukaciya, sai wani jijjiga hannu take ta kasa magana, ga tsoro da firgici da ya bayyana Æ™arara akan fuskarta.

        “Kee” suka daka mata tsawa, fashewa tayi da kuka, tana ja da baya, aikuwa ta tafi ta zauna dabas, jikinta yana rawa, rige rigen tashi suke domin su mata dukar kawo wuka, cikin rashin Imani da tausayi suka shiga dukarta suna kwallo da ita, abinda ya kuma sakata cikin tsoro da firgici,  ta koma gefe ta makure da jikin kofar gidan, tana kare fuskarta.

  Haka suka mata dukar da ko nishi da kyar take jan shi,  anan suka barta babu wanda ya kuma bin ta kanta.

      **
Bayan tafiyar Rabi’ah da Gwaggo Lami, Wasilah ta koma gidan dan ba zata iya zama a gida ba idan Rahmah ta tafi asibiti dan haka tayi wanka ta shirya ta tafi makaranta.

  Tunda ta nufi makaranta dalibai suke nunata, baki daya sai ta muzanta ta kasa katabus, a hankali ta nufi ajin su ta zauna. Shiru tayi sai ya zama duk yaran ajin suna zuwa zasu kalle ta, su koma wani wurin su zauna, abin tausayi sai gashi tana danasanin zuwanta Makarantar, har aka tashi bata yarda tayi magana da kowa ba, sai da zata tafi gida wasu dalibai suka tare ta suna tambayar ta.

“Wai da gaske anyiwa yayarki fyade ta haukace?” Kasa magana tayi kanta a kasa, tana share kwalla da yake zuba mata, wuce su tayi bata kuma kallon su ba, tunda ta iso gida ta shiga dakin su ta zauna, ta samu sauran abin karyawan da Rahmah ta ajiye musu, bata iya ci ba, ta kwanta barci ne ya dauke ta,  ta cigaba da barcin ta.

  Har sai da aka yi sallah ta tashi tayi itama ta, ci abincin ta nufi gidan Gwaggo Lami, amma tsoron kar su dake ta yasa ta nufi asibitin da Ammyn suke sa kafa, domin ba zata iya zaman jiran Rabi’ah.

         Lokacin da ta isa ta sha tafiya, kafin ta shiga cikin asibitin, tana ta rab’e rab’e, har dai ta isa dakin su Innah,  sai ta leka su ta window. Sai ta koma  can ta tsaya dan tasan Ammyn zata mata fada na zuwa ita É—aya.
A dakin kuwa Ammyn na zauna ita da Rahmah, Jamilah tana barci. Idanun sun na kanta,  duk wani motsin ta akan idanun sune, idanun su ya kumbura domin sun ci kuka har sun godewa Allah. Kallon Rahmah Ammyn tayi tana faɗin.
“Anya ba zaki tafi ki duba min su auta ba, zuciyata taki min dadi wallahi ina jin su a raina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button