NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:52 – Nuriyyat: WATA ALKARYAR…!
The Beginning of Destiny
Na
Mai_Dambu
Inda Ranka<15>

“Wato ina kai ki, kayan nan sun kai wata goma da kamshin matar gidan domin idan d’agawa zaki ji wani kamshin turare me mugun dadi, hmmm” abinka da mutumin da rashin godiyar Ubangiji ta cika mishi zuciya a tare ta fara ganin ina zata iya kome domin samun abin duniya a hannu  masu kuÉ—i tayi shiru kafin ta kalli Asabe ta ce mata.
“Ina ce zamu je naga inda suke domin na kafa hujja?”

     Cike da mamaki take kallon Gwaggo Lami kafin ta karkace kai ta ce mata.
“Sannun amka Sarkin Yara, kaza me y’aya ko? Toh ki ji an gaya Miki da kyau, birni ba kamar garin nan bane ko yan lema ba zaki musu kad’ibiri ba, idan ba zaki bada ita ba kalas magana ya kare amma kuma dauko wani batun zaki bita ki ga wata Uwar? Ban san Æ™addaran da ta ajiye ni a nan ba kin ga tafiyata tunda so kike ki gani da ido sai ki shirya.”

Cikin sauri ta tare ta, tana bata hakuri dake idanun ta ya makance da Masifar son abun duniya dan haka ta shiga bata hakuri,
“Kiyi hakuri naga ranki ya b’aci,  ba zan kuma ba, taya arziki ya zo min zan kore shi, waye zai ki wannan damar da take zuwa sau daya a rana, dan haka na amince gaskiya gobe ko jibin a zo a dauke ta.” Ta kalli Inda Rabi’ah take takure, toh me zata yi mata yarinyar da ba kawo mata cigaba take ba, maganin haka ta tafi aikatau domin ta samu rarran abin shiga idan ba haka ba, karshe sai auren Rabi’ah yazo a ce ai tana mata talla ta bada wani abu karshe ita bata ba yarda ba, ba a bata ajiye ba dan ma kar a ga zallamarta ce da tattara yaran baki dayansu, su tafi mata aikatau.

“Lami ina magana kin b’ata shiru kamar me nazarin kujeran aikin hajji?” Inji Asabe tana washe yala-yalan hakorin ta.
“Ke dai bari ai dan kar a ce na cika son kai da na had’a yaran baki daya na tura su aikatau, har da wancan da maza suka mata kwaf daya su tafi ina dalili, ga Yaran dama tabarkalla kamar su suka yi kansu,taya zan zo wannan damar ya wuce ni.”. Girgiza mata kai Asabe tayi sannan ta ce mata.
“Kuma wallahi keda arziki bibiyu, wanda yayi miki hassada ai sai dai ya mutu”
  Sake shiga rudani tayi domin baki daya tana son kudi amma bata son tayi abinda zai dame ta, tace mata.
“Bar Rabi’ah ma tayi Allah ya saka albarka a abunda zasu domin nima zan fita me kyau na sha me kyau. Ita kuma Uwarta na hanata sakat na kuma hanata  magana, domin ba zan yarda ta b’ata min cigaba ba, dan haka kawar Arziki bani mu tafa”

      Tafawa suka yi sannan suka shiga kulla makircin da zata ficce su, Rabi’ah tana jin su, ita kan bata ma san me zata yi ba, domin kamar kanta ya juya. Sai zare idanu take kamar wacce aka bata yaji, nan kuwa ba kome yake sakata haka ba, illa yunwa domin takai kwana biyu me kyau bata ci abinci ba, tsoro da firgici tare da kwana a dakin me duhu ya sata kasa cin kome, abin haushin sam Gwaggo Lami bata duba halin da take ciki ba, ganin ta take kamar da gayya take mata hana shi yasa take azabtar da ita.
  **
Duk yadda Ammyn taso danne al’amarin Rabi’ah sai da ta kasa, dan haka bata ce musu zata zo gida ba, kawai ta tattaro tazo domin tace musu bari ta dawo nan zata, tana isa gida wankin kayan Yaran tayi, sannan tayi musu girki, Sabida kulafuci irin na Uwa matar nan bata iya zama taci ba, ta yafa mayafinta sai gidan Gwaggo Lami, ta shiga da sallama bata nan, sai dai bata ga Rabi’ah ba, sake sallama tayi.

Can  hango Rabi’ah ta leken ta, sai kuma ta koma dakin, bata kuma lekenta ba, cikin wani irin damuwa ta nufi dakin, da sauri tana kiran sunanta.
“Adawiyya? Zo Ammyn ku ce kin ji” ta fada tana shiga dakin, yarinyar tayi kaishi tana tsugune, ga tulin gashin kanta da ya lullube mata fuska, da sauri ta isa gare ta, abin ka da uwa. ÆŠaukar ta tayi cak ta nufi waje da ita, yarinyar ta fita hayacinta,goyata tayi zata fita daga cikin gidan, Gwaggo Lami ta shigo.

“Eheeee” ta fada tana sake baki,
“Yaya Lami wallahi bata da lafiya idan na kaita ta ga likita zan dawo miki da ita, amma don Allah na fara kaita ta ga likita”
“Ke dalla rufe min baki, sauka ta kafin ranki ya b’aci, dan bakin ciki yarinyar da take lafiya lau zaki goya salon ki ja min magana, toh nan da kika ganta ma godiyar Ubangiji zaki yi da kuka gana da jibi kika zo ba zaki ganta ba” inji Gwaggo Lami,
“Don Allah kin ga yanayin da take ciki, ki bari na kaita asibiti”
Kallon ta Gwaggo Lami tayi sannan ta girgiza kai.
“Naji Asibiti zaki kaita, toh ni kuwa sai na rabaki da ita na kuma rabaki da sauran Yaran domin sai na fadawa mutanen gari cewa tura su kike ga karuwanci, kin ga za a Kore ki. Ƙarki manta kowa zai hango sharrin da kuka yiwa Haliru. Sannan kuma zaa raba ku dai ki tafi da Ita”

  Wani irin tashin hankali ta shiga, tana hango halin da Jamilah take ciki, ga shi itama Rabi’ah babu lafiya, har gwara na Rabi’ah da jamilah, tunda ita abin bai kai haka ba, sauke Rabi’ah tayi hawaye na zuba mata, bata iya juyawa ba ta kalli Rabi’ah domin karta ga hawayen da yake zuba a idanunta. Sannan a cikin yanayin da Rabi’ah take ciki, tsoro ya hanata gane wacece ta dauke ta, domin ta rigada ta dimauta, idan da zaka tambaye ta Meye ya faru bata sani ba, bata gane kome yanzu kawai sai yadda aka yi da ita, dan haka Gwaggo Lami ta finciko hannun ta, suka shige cikin gidan.

Kunu me zafin Bala’i ta shiga dura mata, abin tausayi tana ki tana kome sai da ta shanye, take fatar bakinta yayi jajjur. Duk da kasancewar ta me dan duhun fata, duk da ba dubu ne can ba, domin da zata samu kulawa zata iya gogewa.  Tana takure a gefe tana sauke numfashi, amma kuma haka ya taimaka mata daga halin yunwar da zata kashe ta, mikewa Gwaggo Lami tayi ta ja ruwa a rijiya, ta kama ta mata wanka ta kuma yanke mata tsawon gashin kanta, tana gama mata, ta dauko mata wasu riga da zani ta cilla mata, bawai tayi haka dan zuwan mahaifiyar Yarinyar ba a’a tayi ne domin amfanin kanta.

   Domin kuwa yar duwala ta shigo har gidan, ta ga yadda Rabi’ah take ta ce mata.
” A haka zan kai musu yarinya kamar mahaukaciya? Toh ba dani ba, idan zaki san yadda zaki yi da ita toh jibi ne tafiyar babu b’ata lokaci”

          Shine babu shirin ta fita ta sayo mata wannan kayan da ta saka mata a jikin ta a wurin dilalliya, sannan tana gab da cimma burinta shine Ammyn zata zo ta raba bata da nasarar ta.

Fitar Ammyn daga gidan tayi alkawarin ba zata kuma rokon su akan Yaran ba, ila iyaka ta bar musu Yaran, ta fada tana kuka. Duk da fushi tayi amma bai kai har zuciyar ta ba, domin tana komawa gida kasa nutsuwa tayi duk da matar Ammar tana mata magana amma bata iya bata wani amsa mata ba, har ta shirya ta dawo asibiti bata da nutsuwa, da Rahmah zasu dawo gida baki daya ta rungume, tare da musu addu’a duk inda suka shiga Allah ya kare al’amarin su.  Bayan tafiyar su sai gashi baki daya ta kasa nutsuwa, kamar zautacciya haka ta kasance a wannan daren, domin tashin hankalin da zuciyarta take ciki, ganin barci ba zai dauke ta ba, ta shiga ban daki tayi alola, tana kuka tana nimawa Yaranta sassauci a wurin Ubangiji, ya kare su ya shirya mata su sa sauran Yaran al’ummar musulmi ajama’in.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button