NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Mutanen su na danbatta yan uwan Alhaji Muhammad Lawal Dambatta ba karamin jin dadin ta suke ba, saba’in Hajiya Karimah yar nan Lagos ne, Uwarta Bayarabiya Ubanta Dan Sokoto. Hajiya Karimah irin mutanen nan ne da babu ruwan su da kowa daga ita sai Yaranta, tana da Yara guda uku, Shamsudeen, sai Abdul Fatah, da kuma karamar su da ba zata wuce Sa’ar Rahmah ba wato Jawahir. Matsalar su yaran sakaltattu ne babu ruwan su da kowa sai Uwar su har dama dama Shamsudeen yana makale a part din Mammy, ita kuma Hajiya Karimah suna kiranta da Momma, duk da wannan halin nata, tana da mugun kirki, idan kuma jinin ku ya hadu ba a magana domin ita din uwar Dakin Alkasim da Badi’atu ce,, shi kuma Aaman Dan Mammy ne bai yarda da kowa ba sai mammyn shi. Duk da wannan yanayin nasu yaran baki daya suna da tarbiyya da hankali duk yadda ka zauna dasu sai sun nuna maka sun fito daga babban gida, gashi Allah yayi musu Baiwar ilimi.

A dawo labari
      A halin da ake ciki abinda ya hana Aaman komawa mugun kishi kuma yana jiran Mahaifin su da baya kasar shi yasa tsayar da shi bai tafi ba sai ya dawo su tafi tare.

   Koda ya shiga dakin shi ban daki ya shiga yayi alola sannan ya gabatar da sallah nafillah, bayan ya idar ya daura da istahara domin yana son Allah ya zab’a mishi mafi alkhairi. Har aka kira sallah asuba ya tashi ya tafi masallaci, koda aka idar da sallah ya jima a cikin masallacin kafin ya fito ya nufi cikin gidan su.

Sai da ya shiga dakin Mammyn su ya gaida da ita, sannan ya nufi wurin Mommah, ya gaishe ta kafin ya nufi dakin shi ya kwanta.

**
Daƙayyawa

“Ammyn!!!” Ta d’ago kai da sauri tana kallon Rabi’ah da ta kirata.
“Ya dai Auta? Me kike so?” Ta mike tare da tambayar ta tana kuma nufar ta. Gani tayi kamar ana jan Rabi’ah É—in.
“Ammyn ki rike Ni?”  Ta mika mata hannu ko kafin ta isa an kuma fisgarta wani irin duhu me matukar baki ya ratsa tsakanin su.
“Ammyn!!!” Ta kwalla mata kira, wanda yayi daidai da farkawanta daga mafarkin da take, addu’a tayi tare da mikewa ta shiga ban daki ta kuma alola, sannan ta zo ta fara sallah nafillah daidai ana kiran sallah shiga Masallaci, sai da ta idar kafin ta mike ta gabatar da sallah asuba, addu’a takee akan yaranta, tana yi tana kuka tana gayawa Allah kukan ta tare da niman kariyar Ubangiji akan Yaranta, ta dauki wannan a matsayin Æ™addara Ya Allah ya kare mata Yaranta a duk inda zasu shiga a faÉ—in duniya, dan tasan ko sun yi aure zasu fita karatu ba zata kashe musu rayuwar su dan abinda ya faru da Jamilah ba, a yanzu take jin daidai ta sayar da Rayuwar ta Yaranta su yi ilimi koda kuwa haka yana nufin barin numfashinta daga gangan jikinta ne, dan haka tana ta addu’a Allah yasa su Rahmah su zo da wuri.

   **
Can kuwa kasancewar mijin Gwaggo Lami dan Union ne, asuban fari ya bar gidan shi. Dan haka yana fita itama ta tashi Rabi’ah da take dakin duhu a zaune kamar mayya, ban da tsoro babu abinda yake kara kashe ruhin yarinyar, mika mata wani kunshi tayi a leda ta bude mata ido tana faÉ—in.
“Idan kika je gidan duk abinda kika samu ki dauko ki bawa Yar duwala, sannan ko wani yace zai tab’a wandon ki ya baki kudi ki amsa, kinji ko idan naji labarin baki bada kome an kawo min ba sai na yankaki” ta zaro mata manyan idanun ta, tana nuna mata wuka sabo fil, wani irin rawa jikinta ya dauka ta zube a wurin kamar zata suma.

Ganin haka ta daka mata tsawa tare da d’agata, domin ko tayi mata tsawan baya sata tayi yadda take so, Asalima kara gigita mata kai yake, dan haka ta riko hannun ta,suka nufi waje. Bata tsaya ba sai gidan yar duwala, wacce take kofar gidnta ana ta zuba yara a J5(Yes labarin nan haka yake haka suke lallaba mutanen kauyen tare da basu labarin zasu samu alhalin babu kome sai danasani.)

    Haka aka shirya su kamar yadda ake makare dabbobi a cikin motar haka suka zauna, sannan suka yi sallama da iyayen Yaran ita kuma Yar duwala ta ce musu.
“Insha Allah nan da wata biyu zuwa uku zan kawo muku kudin aikin Yaran ku, dan haka zasu tafi ku saka musu albarka domin su samu aiki me kyau da gidan mutunci”

       “Aiko mun gode da wannan halin karanci da kika mana, Ubangiji ya kara budi” yadda suke mata Addu’a zaka rantse akan wani aikin Allah ne nan kuwa hm.

    Tun kafin a fito masallaci suka tadda motar,aka bar garin da Yaran. Kowa ya kama gaban shi da fatan nasara akan dan da ya tura birni..

    Tana dawowa kuwa ta haura gadon ta, tayi kwanciyarta o sallah bata yi ba, kamar ba dan mutum ta tura wani wurin ba, kamar irin kazarta ta bada a tafi dashi garin. Dan haka ta gyara kwanciyar barci me cike da mafarkin tayi kudi ya dauke ta.

     .
Karfe bakwai Sadam ya kawo su Rahmah ya shigo cikin dakin ya gaida Ammyn.
“Zaka tafi ko? Don Allah ko zaka sauke ni a unguwar hayi”
“Toh babu damuwa, ya me jikin dai?”
“Alhamdulillahi jikin dai sai godiyar Ubangiji, tana dan sakewa amma sai da Rahmah.” Ta fada cikin wani irin murya me ban tausayi, domin kuwa a jikinta take jin kamar Rabi’ah tayi nisa da ita.
Anya ba mutuwa tayi ba?
Kai ina bata mutu ba
Ta shiga zullumin haka ya saka idanunta zuba da kwalla, dafe kirjin ta tayi tana zubda kwalla me yawan gaske tana faÉ—in.
“Alhamdulillahi, Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha, Ya Allah Nagode maka Ya Allah Nagode maka.” Abinda take fada tana nanatawa kenan, har kusan minti talatin kafin ta mike. Har ita Jamilah kuka take dukkan su, sannan ita kanta Ammyn idan ka tambaye ta bata san meke damunta ba, amma deeply inside dinta tana jin wani irin ciwo da zafi a ran ta, wannan yasa ta kasa magana, haka ta bar su Rahmah suka nufi gidan Gwaggo Lami, Allah ya taimaka Sadam bai bar gidan ba, haka ya tsaya. Ta shiga cikin gidan.

Gwaggo Lami tana tsaka da barci ta ji muryan Ammyn gabanta yayi mugun faduwa, a gigice ta farka tare da hantsilowa daga gadon bononta,  jikinta yana rawa, ta fito haka kawai taji wani irin tsoro da tashin hankali ya cika mata Zuciya, bata san lokacin da ta fara rabtabo bayani ba.

“Ayya Harirah nayi gaban kaina, na tura Rabi’atu birni aikatau, wallhi ko jiya naso gaya Miki sai dai ban san yadda zan gaya Miki ba, domin kar ki ce zaki hanani ita” a wani mugun razane Ammyn ta rike kirjin ta, idanun ta a waje, bakinta a bude kamar me cutar asthma, sai kokarin jan numfashi take amma kamar wanda aka kwace daga kirjinta, zama tayi dabas tana mata alama ta bata ruwa. Ita kan ta Gwaggo Lami bata taÉ“a shiga tashin hankalin irin na yau ba, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba domin tasan bata kawo abinda ta aikata zai zama kalubale a gareta ba, sai da taga Ammyn a cikin wani mugun yanayi. Dakyar ta ce.
“R…u…w…a” ta fada a rarrabe, da sauri Gwaggo Lami ta shiga cikin dakin ta, ta É—ibo mata ruwan. Tana karb’a bata yi wani jinkiri ba ta kai ruwan bakin ta.

           Tana sha yana zuba hawaye na zuba a cikin idanunta gwanin ban tausayi, haka ta jika rigar ta da mayafinta. Kafin ta ce.
“Alhamdulillahi aka kulli ahalin, Allah ka tsare ta da hijabinka, ka kareta da karfin mulkin ka, Ya Allah ka bata kariya daga karfin ikon ka, Ya Allah.” Fashewa tayi da kuka ta rasa ina zata cusa ranta, duk cikin Yaranta tana Masifar kaunar Rabi’atu, wani irin mugun so takewa Yarinyar me dafa ruhi da jinin jikin ta, bata jin zata kuma ganin Yarta domin ta ji haka a jikin ta tun lokacin da ta farka daga mafarkin nan Allah sarki shi yasa tace Ammyn rike hannuna.” Wani irin kuka ne ya kuma kamata ta rushe da kuka wiwi kamar Yarinya tana faÉ—in.
“Da kin gaya min aiki zaki tura ta da na baki Rahmah kin tura ta, Wallahi zan iya hakuri da dukkan su amma Rabi’ah ba zan iya hakuri da ita ba, don Allah idan kin san inda zan same ta ki gaya min don Allah ki gaya min, idan ba a tausaya min ba halin da nake ciki ba, ba za a kuma turani cikin wani tashin hankali ba,lallai yau na kara tabbatar da azancin masana harshen Hausa da ake cewa da É—a zuci gobaran mahaifi, Haliru ya tozarta mu, nazata ku da kuke mata ba zaku iya tozarta ni ba, ashe kallon kitse nakewa rogo,  bai zama dole kowa ya zama me jin kai a gare mu ba.”  ta faÉ—a kuka, a hankali ta mike tare da a dafa bango tana wani irin kuka me ban tausayi. Ta kalle ta sannan ta ce mata.
“Baki gaya min inda zan same ta ba.  Domin bana son na cire rai da zan same ta, bana son na rasa ta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button