NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

“Toh na amince, amma da sharadi ku kawo min wacce zata nutsu dan idan ta bani zan gwada mata karfi, wacce mazaunin ta yake had’e ba wacce take da budadden mazaunai ba” ya fada yaba jifanta da wani irin dariya.

“Toh ai shikenan an gama magana, indai dan wannan ne akwai yan mata dayawa.” Ta fada tare da shiga cikin gidan.

  Babban gida ne me É—auke da dakuna biyar a jere, sai ban daki a tsakar gidan,  akwai mata matasa da tsofaffi da suka baro garin su, niman kudi a zauren gidan akwai manyan dauka biyu na maza ne, da suka zo cirani wasu suna zama a gidan kasancewar sana’ar su a nan take,wasu kuwa suna tafiya ne basu zama. Sai ya kasance gidan a idanun jama’a gidan Yan cirani ne da masu aikin karfi a zahirin gaskiya a cikin gidan ana buga badakala ce me mugun zafi, sannan Yar duwala tana kai Yara yan mata gidan aikatau, manyan Yan mata tana fita da su Kaduna, Kano, Abuja, wurin mashahuran maza da mata, karkashin jagorancin wata hatsabibiyar mata me suna Adizah.

   Dukkan su yan kasar Camaru ne,  suka yada zango a nigeria, Adizah tana zaune a garin Kano, dan haka idanunta itace Yar duwala duk da matar ta manyan ta, amma bata rike haka a matsayin abinda Allah ta bata ba. Aikin Adizah a Kano shine diban yan mata Kano to Jidda, kai su aikatau da karuwanci. Dan haka daga nan idan Yarinya ta isa hannun ta duk bayan wata biyu ake turawa Iyayen dubu Hamsin, sannan idan aiki kike kuma za a na turawa Iyayen yaran dubu ashirin ya danganta da aikin da Yarinya take ne.

    Dan haka a tsarin Yar duwala, idan ta kawo Yara daga kauye likita na zuwa ya duba su, daya bayan daya domin yasan abinda ta kawo babu matsala a cikin shi, sannan akwai cimmar da ake basu na tsawon wata guda zuwa wata uku, domin duk kudin da za a cire a kaiwa iyayen yarinya daga jikin su ake cirewa, gwargwadon yadda suka kula da Yarinya idan ma gidan aiki aka kai ta, TOH haka zasu fanshe kudin su. Domin basu kai Yara kananun gidan aiki sai inda suka tabbatar ana biyar Albashin duk wata 15k, wasu ma ba wani aiki Yaran suke ba, ana kai sune ana lalata da su, sai ka zata aikatau yarinya take nan kuwa ba kome ne, ila an ajiye ta ne, matar gidan ko me gidan yana lallubeta.

  Kowa ya baje a tsakar gidan ana hira,  aka shiga fito musu da abincin masu rai da lafiya, shinkafa ce da miya sai salad da juice, Dakyar wasu suka yi sallah masu Æ™arfin hankali, Rabi’ah tana can makure da Jakarta, sai zare idanun take, d’aga kai Altine tayi ta ganta a can gefe, mikewa tayi ta zuba mata abincin tare ita, domin ta lura Rabi’ah tana da tsoro, dan haka ta jata suka shiga daki, ta saka mata abincin a gaba, kallon hannunta tayi da faracunta (kumba ko farce) da suka hada wani shegen datti.
“Tashi muje na wanke Miki hannu” haka suka fito, ta wanke mata hannu, ta dauki ruwan goran su da Yar duwala ta ce mata.
“Altine baki dauki ruwan goran ba”
“Mun gode” inji Altine, sannan suna shiga dakin suka fara cin abincin, tana kallon yadda Rabi’ah take zuba loma, Sabida abincin akwai ma’aikata na musamman da suke girkin dan haka abinci ne me kyau da lafiya, ganin haka yasa ta tsame hannunta tana kallon ta har taci kusan rabin abincin kafin ya kalli Altine.
“Ci idan baki koshi ba na karo Miki” sake dunkular abincin tayi ta cika bakinta, tausayin yarinyar ya kuma kamata, dan shaka tayi ta shafa kanta har ta gama ci, sannan ta koma jikin bango tana nishi, kafin kice me har tayi barci, gyara mata kwanciya tayi akan ledarta sannan ta fita, itama ta É—ibo abincin tazo taci, tana idarwa ta kwanta a kusa da Rabi’ah.

   Sauran Yaran suma da suka gama barci kowa ya fara, sai la’asar suka tashi, aka basu sabulu me kamshi da soson wanka, sai man shafawa me kyau da turaruka, manyan matan aka basu shaving cream su gyara hammatar su,  Altine soso biyu ya dauka ita da Rabi’ah, dan haka ta je musu ruwan wanka ta shiga ban daki ta farawa Rabi’ah, ganin yadda take tsoron ruwan sanyin yasa ta fitowa niman ruwan zafi.
“Yar duwala babu ruwan zafi ne?”
“Yana can baya ku diba.” Haka ta nufi bayan ta diba musu, ta kai ban daki ta mata wanka tass, sannan ta wanke mata sumarta duk da ta ganshi a yanke, amma ta wanke shi da suka fito aka shiga tambayar su.

“Waye yake da kwarkwata, amasali, kyashi da kuraje, yayi magana za a bashi magani, masu gashi suyi magana a fara gyara musu kan su.”

Haka yaran suka fara fitowa ana gyara musu gashin su, sai da Altine ta gama wanka ta fito ta shirya Rabi’ah, sannan ya dauki kayanta ta wanke, wanda ta cire, ta saka mata wani. Sannan ta kawo ta aka fara gyaran gashinta, masu gyaran gashin sai da suka yi magana da cewa.
“Waye ya sake mata gashinta? Yarinyar tana da kome me kyau sai a sake mata kar a kuma tab’a mata gashinta”
“TOH” inji Altine,

     Har dare duba su ake ana basu kulawa, zuwan likitan da wasu abokan aikin shi, aka shiga duba su kamar me, tun karfe bakwai na dare har zuwa sha biyu na daren aikkn su ya tsaya akan Rabi’ah ce, dan haka suka kalli Juna, kafin Dr Musa ya ce mata.
“Yar duwala wannan yarinyar a kawo ta asibiti, domin zamu duba ta, ki lura yadda take komawa gefe bata son zama cikin jama’a, sannan da muka zo zamu dubata kin ga yadda ta razana tana niman suma mana, a kaita birnin kudu zan duba lafiyarta a can, muga abinda hali zai yi.”

   “Shi yasa da na ga ta kawo min ita naso naki, Allah na tuba Meye za a yi da wannan domin dai tayi kankanta, kawai shegen son kudin mutanen kauye ne na tsiya.” Dariya suka mata sannan suka mata sallama suka bar gidan tare bada nufar asibitin su da suke aiki.

     Ita kan Rabi’ah tana samun jikin Altine ta lafe, sai ajiyar zuciya take, shafa bayanta Altine tayi tayi har suka kwanta, kasa barci tayi tana kuka.  Dole Altine ta tashi tare da janyota ta sakata a jikinta, ita kuwa ta k’amk’ame ta, kamar zaa kwace ta daga jikin Altine.

   Daƙayyawa

Kowa yana barci amma ban da Ammyn da take tsaye a bakin kofar gida, Ammar yana tsaye a kofar dakin su, wannan shine karo na biyar da take fitowa tana leka waje, tare da kokarin kwala kiran sunan Rabi’ah,  kunnenta ne yake jiye mata ihun Rabi’ah shi yasa take fitowa ta duba, ko ta wajen babu ita babu labarin ta, haka ta rufe Kofar gidan ta koma.

“Ammyn Jamilah, kiyi hakuri Rabi’ah fa bata nan, Kiyi hakuri Allah zai dawo Miki da Yarki cikin koshin lafiya. Amma ki mika Alamarinki zuwa wurin Allah yana ji yana gani shi rayayyen nan ne da baya mutuwa, haka da kike yi zai iya haifar Miki da wani ciwo na daban, kin ga idan aka yi rashin dacen sai ki rasa rayuwar ki baki ga Rabi’atu ba, amma idan kayi hakuri Rabi’ah zata zo kamar daga sama, balle nan da wani lokaci ne zata dawo gare ki Insha Allah.”

“Toh shi kenan, tunda kace zata dawo bari naje na kwanta, toh wa ya sani ko bata ci abinci ba, a ina take kwance, a hannun waye take? Tayi barci ko bata yi ba? Kaga duk ban sani ba, dole na damu Rabi’ah tayi kankanta tunda abin nan ya samu Jamilah Yan uwanta suka gaya min bata barci, waye ya sani ko bata da lafiya ne, ai ko jiya da naje gidan Lami na samu bata da lafiya, ka ga dole zuciya ta, ta damu waye zai yi jinyarta?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button