WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Yadda take maganar zaka fahimci damuwa ya taba brain dinta domin maganar da take tayi yawa kuma bata hadiye numfashinta take sake wasu dan haka ya juya tare da shiga dakin su, ya dibo mata ruwa ya mika mata.
Sannan ya ce mata.
“Zauna ki sha” babu musu ta zauna a kujeran tsuguno na matar shi da ya dauki mata, shan ruwan tai sosai.
“Ki godewa Allah, Ammyn” ya fada mata,
“Alhamdulillahi” a hankali taji wani abu ya taso tun daga cikin ta, sai da ya hauro wuyarta ya tsaya cak, shi bai sauka ba,. Shi bai fita ba kuma sai ya haifar mata da shakuwa, haka ta sha ruwan sosai kafin ta daina shakuwar..
This is the Beginning….
Alhamdulillahi Ubangiji ya bani ikon kawo karshen free pages na wata alkaryar labari me cike da darussan rayuwa, labari me cike da faffutukar rayuwa faffutukar Æ™addara, zamba cikin aminci, yaudara da butulci, cin Amana da zalinci, kuka akan kuka. Al’amarin Soyayya me girma, al’amarin zamantakewa me dadi, Barkwace da Drama gudun ceton Rai…. Dari uku ne babu yawa.
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
Mai_Dambu
3/1/22, 18:53 – Nuriyyat: Uwa mana da Mama<17>
Last Free page
Ganin bindiga a kugun Sadam ya sa shi barin wurin ba dan yana jin ya hakura ba, sai dan tanadin da yayi musu na idan ba a fito mishi da Uban shi ba sai ya illata su baki daya, dan haka ya kudiri Aniyar samar kan shi hanyar da zai na samun su yana cin Uban su.
      A hanyar komawa gida Sadam yana tuki, wayar shi tayi kara, bai dauka ba sai da ya isa kofar gidan su, kafin ya dauka ya ga number Aaman ce. Zai kira wani kiran ya shigo mishi dauka yayi tare da sallama ya ce mishi.
“Man baka da kirki, kayi kokarin ganin kazo domin kome ya lalace fiye da da can baya”
A kage ya tambaye shi.
“Meke faruwa?”
“Hmm bari zan maka bayani an jima ya kashe wayar sai da ya ga sun shiga cikin gidan sannan ya juyar da motar yayi tafiyar shi a hanya ne ya kira Aaman yayi mishi bayanin halin da ake ciki, kamar zai yi Hauka kafin ya kashe wayar dan Ihu yake da masifa, sai kace Sadam din ne ya kai ta aiki dan haka ya shiga masa masifa.
  A cikin gidan kuwa sun sami Ammyn tasha kuka ta koshi, idanunta basu daina zubda kwalla ba, kuma sun tambaye ta taki gaya musu halin da ake ciki, tayi tasan halin Yaran ta, sau su kuma dulmiyar da Jamilah cikin wani hali, dan haka tayi shiru, tana jin a ranta kuka ba shi bane mafita, ta karfafa zuciyar ta, yadda Yaran suma zasu tsaya da kafar su,.ba yadda zasu koma bayan wani suna kuka ba, sai abu na gama da ta ji a ranta babu makawa Allah yana tare da su, shine addu’oi. Dan haka ta rike wannan gam a ran ta.
  **
Dutse.
Dake me motar dama mutumin Yar duwala ce, yasan inda zai ajiye ta Yaran, dan haka wani Unguwa ne can irin tsofin unguwar nan ya kai ta, suna isa aka bude Yaran, suka yi ta fita kowannen su yana komawa gefe.
 Duk cikin Yaran Rabi’atu ita ce karama kuma mara lafiya, akwai wasu yan mata biyu manya sunan dayan Altine dayan kuma Hinde,. Tunda suka shiga cikin motar Altine take kula da Rabi’ah, dan tayi mata kyau, ita kuma haka Allah yayi ta da son abu me kyau, gashi tana mata dibi da kanwarta Hansiya, haka yasa ta rike hannun Rabi’atu, har suka shiga cikin gidan da aka nuna musu, yar Duwala na tare da driver.
“Gaskiya kin kara min wani abu, ko kuma ki zab’a min wacce kika san wani kato bai fasa ta ba, nazo na rage dare da ita” ya fada tare da zama cikin motar shi yana dariya. Itama cikin ko in ta ce mishi.
“Amma kasan kan duniya ba zaa rasa ba, kuma zaka samu me dadi dan kasan Yan matan kauye ba irin na birni bane masu taurin kai.”
     Tab’e baki yayi cikin kwarewa da iskanci ya ce mata.
“Anya ba zan koma gurguran kananun Yara ba? Domin na fahimci manyan nan basu da wata kamun kai kamar Yaran”
“Hmm! Akwai su kuwa amma kasan idan ka tab’a karamar yarinyar zai zama laifin cin zarafi ne, ka gwada manyan mana.”
“Toh na amince, amma da sharadi ku kawo min wacce zata nutsu dan idan ta bani zan gwada mata karfi, wacce mazaunin ta yake had’e ba wacce take da budadden mazaunai ba” ya fada yaba jifanta da wani irin dariya.
“Toh ai shikenan an gama magana, indai dan wannan ne akwai yan mata dayawa.” Ta fada tare da shiga cikin gidan.
 Babban gida ne me É—auke da dakuna biyar a jere, sai ban daki a tsakar gidan, akwai mata matasa da tsofaffi da suka baro garin su, niman kudi a zauren gidan akwai manyan dauka biyu na maza ne, da suka zo cirani wasu suna zama a gidan kasancewar sana’ar su a nan take,wasu kuwa suna tafiya ne basu zama. Sai ya kasance gidan a idanun jama’a gidan Yan cirani ne da masu aikin karfi a zahirin gaskiya a cikin gidan ana buga badakala ce me mugun zafi, sannan Yar duwala tana kai Yara yan mata gidan aikatau, manyan Yan mata tana fita da su Kaduna, Kano, Abuja, wurin mashahuran maza da mata, karkashin jagorancin wata hatsabibiyar mata me suna Adizah.
  Dukkan su yan kasar Camaru ne, suka yada zango a nigeria, Adizah tana zaune a garin Kano, dan haka idanunta itace Yar duwala duk da matar ta manyan ta, amma bata rike haka a matsayin abinda Allah ta bata ba. Aikin Adizah a Kano shine diban yan mata Kano to Jidda, kai su aikatau da karuwanci. Dan haka daga nan idan Yarinya ta isa hannun ta duk bayan wata biyu ake turawa Iyayen dubu Hamsin, sannan idan aiki kike kuma za a na turawa Iyayen yaran dubu ashirin ya danganta da aikin da Yarinya take ne.
  Dan haka a tsarin Yar duwala, idan ta kawo Yara daga kauye likita na zuwa ya duba su, daya bayan daya domin yasan abinda ta kawo babu matsala a cikin shi, sannan akwai cimmar da ake basu na tsawon wata guda zuwa wata uku, domin duk kudin da za a cire a kaiwa iyayen yarinya daga jikin su ake cirewa, gwargwadon yadda suka kula da Yarinya idan ma gidan aiki aka kai ta, TOH haka zasu fanshe kudin su. Domin basu kai Yara kananun gidan aiki sai inda suka tabbatar ana biyar Albashin duk wata 15k, wasu ma ba wani aiki Yaran suke ba, ana kai sune ana lalata da su, sai ka zata aikatau yarinya take nan kuwa ba kome ne, ila an ajiye ta ne, matar gidan ko me gidan yana lallubeta.
 Kowa ya baje a tsakar gidan ana hira, aka shiga fito musu da abincin masu rai da lafiya, shinkafa ce da miya sai salad da juice, Dakyar wasu suka yi sallah masu Æ™arfin hankali, Rabi’ah tana can makure da Jakarta, sai zare idanun take, d’aga kai Altine tayi ta ganta a can gefe, mikewa tayi ta zuba mata abincin tare ita, domin ta lura Rabi’ah tana da tsoro, dan haka ta jata suka shiga daki, ta saka mata abincin a gaba, kallon hannunta tayi da faracunta (kumba ko farce) da suka hada wani shegen datti.
“Tashi muje na wanke Miki hannu” haka suka fito, ta wanke mata hannu, ta dauki ruwan goran su da Yar duwala ta ce mata.
“Altine baki dauki ruwan goran ba”
“Mun gode” inji Altine, sannan suna shiga dakin suka fara cin abincin, tana kallon yadda Rabi’ah take zuba loma, Sabida abincin akwai ma’aikata na musamman da suke girkin dan haka abinci ne me kyau da lafiya, ganin haka yasa ta tsame hannunta tana kallon ta har taci kusan rabin abincin kafin ya kalli Altine.
“Ci idan baki koshi ba na karo Miki” sake dunkular abincin tayi ta cika bakinta, tausayin yarinyar ya kuma kamata, dan shaka tayi ta shafa kanta har ta gama ci, sannan ta koma jikin bango tana nishi, kafin kice me har tayi barci, gyara mata kwanciya tayi akan ledarta sannan ta fita, itama ta É—ibo abincin tazo taci, tana idarwa ta kwanta a kusa da Rabi’ah.