NOVELSWATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai ilimin hanyoyin kwantar da hankali zai yi amfani da cikakkun bayanai da kuka ba ta game da halayen ku na É“acin rai don taimaka mata yin daidaitaccen ganewar asali.
Lokacin Neman Taimako don Maganganun Farko
Akwai nau’ikan phobia guda uku: phobia na zamantakewa, agoraphobia, da takamaiman phobia. Alamu, ko halayen son zuciya, na iya zama na tunani, kamar tsananin rashin jin daÉ—i ko É“ata rai; na jiki, kamar kuka ko ciwon ciki; ko hali, wanda ya haÉ—a da dabaru iri-iri na gujewa.

Halin ku na ɓacin rai ya cancanci tafiya zuwa likita lokacin da alamun ku suka tsoma baki tare da ikon samun kuɗi, kula da kyakkyawar alaƙar ku, da aiwatar da muhimman ayyuka na yau da kullun, kamar wanka ko siyayya.
Magani don Ra’ayin Phobic
Dukkan nau’ikan phobia guda uku ana iya magance su sosai tare da taimako daga Æ™wararrun lafiyar hankali kuma suna daÉ—a yin muni cikin lokaci idan ba ku nemi magani ba.

Magani na yau da kullun don phobia ya haÉ—a da fasahohin ilimin halayyar halayyar ciki har da rashin hankali a hankali, kwatanta tsoron ku marasa ma’ana ga ainihin haÉ—arin, da canza tunanin ku na rashin hankali zuwa masu inganci.

Ra’ayin Soyayya A Cikin Zamantakewa Phobia
Rashin tsoro na zamantakewa, ko rikicewar tashin hankali na zamantakewa, tsoro ne na yanke hukunci daga wasu. Yana da tsananin tsoro na kunya ko wulakanta kanku a cikin ƙanana ko manyan ƙungiyoyi.

Halin phobic ga abin da ke haifar da phobia na zamantakewa na iya haÉ—awa da:

   da yawan damuwa za ka bata wa wani raia
   tsananin tsoro na yin zance da baki
   guje wa duk wani yanayi da za ku zama cibiyar kulawa, kamar bikin ranar haihuwqa
   tsammanin mafi munin yanayi yayin yanayin zamantakewa
Ra’ayoyin Phobic a cikin Agoraphobia
Agoraphobia ana yawan tunaninsa azaman tsoron faffadan sararin samaniya. A haƙiƙa, wannan matsalar tashin hankali tsoro ne na rashin iya tserewa zuwa aminci ko neman taimako lokacin da kuka fara jin haushi. Alamun jiki sun dace da na takamaiman phobia (a ƙasa).
Tunani mara kyau a lokacin phobic dauki ga agoraphobia na iya haÉ—awa da:

   Ina rasa hayyacinta.
   Zan iya rasa iko kuma in sami amsawar bayyani a fili a cikin jama’a kuma wasu na iya kallo.
   Ba zata iya fita daga nan ba idan ta fara samun ɓacin rai.
Wasu halayen halayen agoraphobia ne, gami da:

   rashin iya barin wurin zama na dogon lokaci
   kyamar zama nesa da gida
   buqatar wanda ka yarda dashi lokacin fita
Maganganun Ra’ayi a cikin Takamaiman Phobia
Takamaiman phobia yana gabatarwa azaman mai tsanani, ƙari, da tsayin daka na tsoron wani yanayi ko abu. Yawan takamaiman phobias yana iyakance ne kawai ta adadin sunaye kuma ya haɗa da, tsoron wanka (ablutophobia), tsoron lambar 8 (octophobia), da tsoron mutuwa (thanatophobia).

Halin phobic ga takamaiman phobia yana faruwa lokacin da kuke tsammani ko haÉ—u da abin da kuke faÉ—a kuma ya haÉ—a da:

   Ka na kusantar halaka
   jin duhu ko haske mai kai
   tashin zuciya ko gudawa
   dabarun gujewa don hana haduwa da abin tunzura ku”
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

Mai_Dambu

3/1/22, 18:53 – Nuriyyat: 19

“Wadannan sune abubuwan da suke haifar da Phobia, ba mamaki inda take ana yawan takura ta, ko ana yawan bata tsoro, ko kuma ta ga wani abun da ya firgita tunanin ta, shima yana haifar da wannan yanayin. Dan haka a nisanta ta da duk abinda aka san zai d’aga mata hankali ko ya jefa ta cikin mugun yanayi a nisanta ta dashi idan ba haka bata iya kasance cikin mugun. Na har abada ga wannan zai taimaka mata wurin samun wadataccen barci, sannan yawan janta a jiki zai taimaka wurin warware matsalar ta, domin ba dawamamme bane zata iya rabuwa da shi.”inji Likitan.
“Toh babu damuwa Insha Allah zan musu cikakken bayanin da kai min, mun gode sosai” Dr Musa, ta fada yana me barin office din.

Sai dare ya samu zuwa, gidan Yar duwala ya shiga falonta ya zauna a hankali, yana kallon ta kafin ya ce mata.
“Ina Yarinyar nan?”  Tab’e baki tayi sannan ta ce mishi.
“Tana dakin su, tun dazun sai kuka take.”
     “Da zaki ji nawa da kun daina sakata kuka domin kuwa matsalar da take fama da shi zai uya shafar harkallarku, Kiyi nazari yarinyar tayi karama, aka kawo ta aikatau matukar matsalar tayi girma Socila warfare zasu shiga daga nan sai Human right, Kinga akwai matsala kenan?” Gyara zama tayi sannan ta ce mishi.
“Meke tafe da kai?” A nutse ya mata bayanin halin da Rabi’ah take ciki da yadda matsalar take cin rayuwar ta, take ta zauna tana zare mishi ido.
“Yanzun ya zan yi?”
“Yadda zaki yi kenan, ki bar budurwar da suke tare tayi jinyarta, nan da wata uku insha Allah zata iya kome da kanta ba sai an raba su ba, yin haka zai iya shafar lafiyar ta, amma idan aka samu lafiyar ta shi kenan”

     Shiru tayi kanta a sunkuye, tana jin bakin cikin wannan asara biyun, kafin fa d’ago kai ta ce mishi.
“Babu damuwa haka za ayi tunda zata samu lafiya kome yayi Nagode sosai, ga wannan” ta tura mishi bakar leda. Dauka yayi yana murmushi.
“Nagode sosai”
“Nice da godiya da irin kokarin da kake min baka gajiya nagode sosai” tashi yayi tare da mata godiya shima sannan ya fita, a bakin kofar yaji muryan Rabi’ah, a hankali ya taka har bakin kofar su, ya leka taba k’amk’ame da Altine, juyawa yayi ya koma dakin Yar duwala ya amshi maganin tare da ruwa ya kaiwa Altine ta bata tashi, sannan ya durkusa a gabanta, yana kallon yadda take tsotsar hannu gwanin ban tausayi, kwanciya tayi a jikin Altine tana zubda kwalla.

    “Meke damun ta?” Ya tambayi Altine da ita take kokarin boye kwallar ta.
“Wallahi tun dazun take wannan kukan, idan na tambaye ta sai ta ce min Ammynta” bayan nan sai tayi shiru bata kuma magana”

“Zo nan Rabi’ah zan saya miki sweet” ya fada yana kallon ta, sake k’amk’ame ta sakamakon jin muryan shi dab da ita.

“Ki kula da ita, kin ji ban da mata fada ko yi mata tsawa, a kula da ita ban da yawan hayaniya ki kula da ita sosai” ya fada yana me fita a dakin.

Har waje ya fita tare da shiga cikin motar shi ya zauna, dafe goshinsa yayi wannan shine karon farko da ta fara jin wani abu akan wani dan yana cikin damuwa, har yaji a ran shi ya tausaya mishi. Zama yayi a cikin motar yana shafa kanshi, kafin ya tadda motar ya bar kofar gidan.

      Dr Musa Nuruddeen, dan garin Hadija ne, Babba ne domin ya kai shekaru arba’in da wani abu,  yana da mata da Yara biyu, babban dan shi yafi Rabi’ah, yana da shekaru goma sha biyar, sai kanwar shi da ba zata wuce sa’ar Rabi’ah ba, ya fara aiki da Yar Duwala shekara biyar baya, kuma iya kan aikin shi ya tsaya ya duba al’amarin yara da matan da ake kawowa, idan kuma an samu wata babu lafiya ya tsaya mata, kamar dai yadda ya tsaya akan Rabi’ah.

Mutum ne da bai cika shiga abinda bai dame shi ba, sannan yana mugun jin zafin wannan abinda yake yi, domin kuwa sau uku yana yunkurin lalata abinda yar duwala take yi, Allah baya bashi nasara, sakamakon karfin da suke dashi tun daga sama, dan haka ya shi ya zuba musu ido, a gefe guda kuwa, yana kallon abinda suke.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button