WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
  Amma tabbas da yana da halin karya karfin su Yar duwala da tuni yayi, sai dai yana fatan Allah ya kawo karshen su, domin sun salwanta da rayuwar Yara da mata dayawa, har yanzun ana kai domin basu fasa ba. Babban burin shi yasan daga ina ake basu duk wani kullawa, sannan yasa su waye suke tsaya musu, wannan shine dalilin da yasa yake jikin su a koda yaushe.
  Yana shiga cikin gidan shi, ya samu matar shi da Yaran shi suna zaune, ana hira shima zama yayi aka fara hira dashi.
“Daddy kace zaka samo min abokin hira idan Yaya Mu’aruf ya tafi makaranta?” Inji yar shi, murmushi yayi sannan ya zuba mata ido, kafin ya ce mata.
“Junainah! Kyale shi zan kawo Miki kawa kwanan kinji? Madam a bani abinci na” ya fada yana kallon matar shi. Mikewa tayi tana dariya, sannan ta ce mishi.
“Oga yau da alamu kana cikin damuwa meke damun ka?”
“Zan Miki bayani bani abinci tukun”
Nufar kitchen tayi sannan ta xubo mishi abincin, ta kawo ta zauna a gefen shi.
  Shiru ne ya ratsa tsakanin su, sai karan cokali da yake tashi a falon har ya gama ci yayi godiya ga Ubangiji kafin ya kalle ta.
“Jiya an kawowa yar duwala Yara ko nace ta shiga kauye ta kwaso Yaran mutane,.matsalar da aka samu yarinyar da aka kawo tana da karamin shekaru ne kamar Junay take, wallahi ban tab’a jin tsoron da damuwa akan Yaran da suke kawowa ba, kamar wannan Yarinyar, a yanzun haka tana fama da cutar Phobia shine nake tunanin ko zan dauko mana ita ne, domin kin ga Nuhu yana nan kuma yana jami’a idan yana gida suna tare da Ma’aruf idan aka samu wata a matsayin abokiyar Junay haka zai taimaka ai yarinya ce sosai.”
     Shiru tayi sabida a rayuwar Saudatu ta tsani a kawo mata wani yazo ya zauna a kusa da ita matukar ba dan uwan mijin ta bane ko yan uwanta, sabida mugun kishin mijinta, wannan dalilin ya sa taki koda yar aiki kenan, gwara ita tayi koda zai kashe ta, kai ko mijin nata bata had’a shi da kowa ba, dan haka tayi shiru yasan idan tayi shiru haka bata son maganar ne, sai dai shi ya kudira a ran shi kida baya yarda ba, zai dauko Yarinyar duk abinda zata yi sai dai tayi amma ba makawa Yarinyar sai tazo gidan.
 Ganin taki magana ya sashi, share ta bai kuma bin ta kanta ba, har kusan karfe goma, ta saka yara a gaba suka shiga daki, sannan ta kashe kayan kallon ta wuce dakin ta, shima dakin shi ya shiga yayi wanka ya kwanta, yana zaune har wajen sha biyu sannan ta shigo dakin, hawa gadon tayi tana me kwanciyarta a gefen sh. Dake yana aiki a laptop bai bi ta kanta ba, sai da ya gama sannan ya juya yana kallonta, yadda tayi kici kici da fuska, share ta yayi tare da juya mata baya.
 Tunda ta ga haka,.sai gata da kanta ta juya gare shi tana kallon shi kamar zata yi kuka, har wani lokaci kafin ta matsa jikin shi. Tare da sakalo hannunta kafadar shi, zata yi magana ya ce mata.
“Ƙarki damu zaki iya kwanciya ba sai mun kai ga haka ba.”
   Duk yadda taso ya kulata yaki, sai basar da ita yake, karshe ganin haka ta koma wurin kwanciyarta, tana jin babu dad’i. Shima kuma bai cika son haka ba, amma babu yadda ya iya dole ya hukuntatta.
   Washi gari.
Da sanyin safiya ya bar mata gidan, domin yasan idan ba haka yayi mata ba, toh ba zata shiga hankalin ta ba, Nuhu kaninta ne, yana karatu a federal university, duk weekend yana gidan koda wasa Dr Musa yaki bata kofar da zata bashi hakuri, duk da yasan abinda yake faruwa a tsakanin su ba wani babban al’amari bane sai dai yana son yayi amfani da wannan damar ya taimaki Rayuwar Rabi’ah daga wannan gidan, domin ta haka ne zai iya sama.mata nutsuwa bada kwanciyar hankali.
 Dan haka ya kudira a ran shi zai yi wannan aikin da zuciyar shi domin taimakon ta,
     Bayan sati ɗaya
Daƙayyawa
Alhaji Muhammad Lawal Dambatta ne da Iyalin shi, sai Ammyn da su Rahmah da suka zauna, Jamilah ta cikin dakin ta takura kanta,s sakamakon yadda mutane suke damunta musamman Yara da yan mata matasa Irin ta, da suka tambayar tana nan ko kuma su shigo cikin gidan suyi ta mata dariya, haka ya kara haukata matsalar ta, dan haka Alhaji Muhammad Lawal Dambatta ya cewa Ammyn.
“Harirah kiyi hakuri zamu tafi Lagos dake, domin akwai wani abinda nake bibiyar na Ishaq ne, kuma ina son ki kasance a can haka zai bamu damar cimma nasarar”
Shiru tayi Hajiya Fatimah , ta saka baki tana me cewa.
“Ayya Maman Jamilah Kiyi hakuri inshallah akwai wadanda zasu zauna domin jiran Rabi’ah a halin da kike ciki kina bukatar ganin likita ne, ba zama a nan ba, don Allah ki tashi muje baki ga halin da Jamilah take ciki ba.”
    “Mammy yanzun haka ma na tura har office din Yan sanda ana binciken inda Yar duwala take, Ammyn inshallah Rabi’ah zata dawo” inji Aaman, dakyar da jin jibi aka shawo kan Ammyn ta amince zata tafi Lagos, amma ba wai dan ranta yana so ba, dan haka ya Umarci Rahmah ta shirya kayan su, zasu wuce dutse. Haka ita da Wasilah suka hada kome basu, sai da suka zo kan Kayan Rabi’ah ne suka kama kuka, dakyar suka fito. Sannan suka shiga bayan sienna, sun barwa Ammar da wasu yan sandan farin kaya damar zama a gidan tunda nan da wasu kwanaki Rabi’ah zata dawo. Aaman ya umarce su, da matukar ta dawo a kawo ta airport zai zo daukar ta.
 Kuma sun tabbatar mishi da inshallah, tana dawowa zasu kai mishi Airport. Hka suka nufi dutse.
Karfe bakwai na dare suka isa, dan haka Aaman ya kai su, masaukin da yake kusa da Airport din, sannan ya nimo musu abinci, bayan sun yi sallah suka zauna, shiru Ammyn tayi ta kasa cin abincin.
“Maman Jamilah Æ™arki manta na zata b’ata ba, aikatau ne Insha Allah zata dawo ai babu abinda zai same ta da Yardan Allah” inji Mammyn Aaman.
  “TOH Allah ya nufa,” ta fada tana me danne kwallar da yake kokarin sauko mata. Haka suka kwana washi gari karfe tara suka bar Jigawa, cike da kewar yar autarta, wanda take jin ta rasa ta kenan idan ba wani ikon Allah ba.
**
Lagos.
Sun sauka lafiya, Alkasim da yazo hutu yaje ya dauko su, sai wani rawan kafa yake akan wasilah tun da ya ganta y wani sussuce, har suka iso gidan, sai da suka fara yada zango a gidan Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, suka huta. Har zuwa washi gari. Kafin shi da iyalin shi suka rako su wani gida da yake jikin na Alhaji Muhammad Lawal Dambatta, sak iri daya babu abinda ya raba da nashi, suka shiga cikin gidan, ya bude musu kome, har da furniture.
Kallon gidan tayi a dame kafin ta ce musu.
“Me zan yi anan?”
“Zaku zauna ne anan ke da Yaranki, wannan gidan ba baku nayi ba, Ishaq ne ya saya da gumin shi, babban burin shi ya yaran shi su samu tarbiyyar arewa, sai daga baya ya kawo su nan su yi karatu duk da can akwai makarantun amma yafi son nan sabida damuwar da kike samu da Yan uwan shi, Harirah Ishaq kamar yasan zai mutu yayi muku tanadin da babu wani abinda zai tab’a darajar Yaran shi. Ni na tura Aaman domin ya zauna da ku yaga halin da kuke ciki, da ace yan uwan shi sun rike ku da amana da nayi musu ihsani.
300â‚?… Insha Allah’
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A’ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank