WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
Mai_Dambu
3/1/22, 18:53 – Nuriyyat: 20
“Amma sai suka kasance butulai marasa tsoron Allah, shi yasa na yanke shawarar kawo ku nan domin dukiyar shi tana nan, ko kafin rasuwar shi zuwan da nayi ya ce min matukar ya samu lafiya zai bar DaÆ™ayyawa, sai shi Allah yayi ikon shi akan shi dan haka ga shi duk yadda kika so kiyi wannan naku ne da Yaran ki” ya kai karshen maganar yana mikawa Aaman takardun gidan ya bata, zubewa Ammyn tayi a kasa tare da sake wani irin kuka, a yanzu mutuwar Mijinta ya dawo mata sabo fil, dan haka take kuka har ta fara cewa bata gani.
   “Bani gani, kome duhu yake min. Innalillahi wa inna alaihil raji’un allahumma ajirni fii musibati wa’akhlifni khairan minha, Ya Allah ka dubi halin da Yarana suke ciki karka raba mu da su, basu tsaya da kafar su ba, Ya Allah rayuwa da mutuwa taka ce Ya Allah.” Ta fada tana kuka, kamar karamar Yarinya.
“Maza dauko mota a kaina JF Hospital.” Da sauri Alkasim ya fita shi kuma Aaman da Rahmah suke rike ta, aka fita da ita, yana saka ta a mota ya juya tare da shiga gidan yaga Jamilah zaune a can gefe ta takura kanta, yana isa gabanta, ya saka hannun d’ago ta. Kauda kai tayi tana kokarin kwace kanta.
“Malama ki saurare ni, ban miki haka dan cutarwa ba, amma tabbas shirun ki yana cutar da zuciyata, dan haka zamu tafi asibitin Kema a duba baki dan ban yarda da wancan tsohon najadun ba, ba mamaki garin yawon bin matan shi ya kwaso wani wani abu ya makala miki.”
  Cikin wani irin kuka da Masifar tsoro ta fara kokarin kwace kanta, shi kuwa ganin zata b’ata mishi lokaci ya sab’ata a kafadar shi yayi waje da ita, tana ihu tana kome, ya fice da ita daga gidan. Yana isa waje ya sakata a motar da karfin tsiya, sannan ya rufe motar ya koma ya rufe gidan ya saka Wasilah a gaba sai da ta shiga cikin gidan, sannan ya juya ya nufi wurin da motar shi take.
Tunda ya shiga yake jin sautin kukanta, haka bai saka shi kula ta ba har suka bar unguwar, tare da nufar asibitin. Koda ya isa ya samu ana ta fama da Ammyn dan haka ya kira abokin shi da suka yi Jami’ar Canada tare ya gaya mishi gashi nan da kanwar shi. Ya mishi kwantaccen office din shi.
   Sannan ya nufi office din da ita, sai da suka shiga office din har zuwa lokacin bata daina share kwalla ba.
“Wow Danbatta nayi kamu, so cute zaka bani aurenta? Wallahi ina son ta da gaske.” Wani uwar harara Aaman ya jefa mishi, a hankali yayi mishi bayani, kamar wacce ake dukarta dan haka ta cigaba kukanta. Kallon ta yayi tare da zare madubin shi sannan ya danna wayar office din shi, ya kira nurse. Ya cigaba da rubuce rubuce, kafin ya d’ago kai yana kallonta.
  Cikin wani irin tausayinta, sannan ya ce mata.
“Ya isa haka, you are safe Babu wanda ya isa ya kuma tab’a kimarki matukar muna raye.” Shigowar nurse ya nuna mata Jamilah haka ta sakata a gaba, suka fita. Mai da dubar shi yayi kan Aaman.
“Ina son Yarinyar don Allah ka shige min gaba na aure ta mana” shiru Aaman yayi yana kallon shi, ya rasa ma me zai fada baki daya Dr Namir Adamu Abbas Jikamshi ya daure shi da jijjiyar shi.
  “Hmm!” Aaman ya ce, tare da mikewa daga kujeran ya fita daga Office din, wannan shine tashin hankalin da ba a saka mishi rana, da yasan cewa abinda zai faru kenan wallahi da bai fara kawo ta asibitin ba, dan hakan ya nufi dakin da aka kwantar da Ammyn, ya zauna, tare da kallon Rahmah da suke hira ita da Alkasim.
  Juyawa yayi a sanyayye ya koma bakin office din Dr Namir ya xauna, har bayan minti arba’in yana zaune kafin suka dawo da nurse din, suka shiga office din, dakyar ya mike tare da nufar cikin office din yana me shiga da sallama, takura tayi gefe tana kallon kasa.
“Dambatta baka da mutunci sam, daga shigowar ka, zaka saka baby cute kuka, idan kayi wasa sai na maka allurai dari kafin ka bar asibitin nan, maza juya ka daina kallonta.”
   A sace ta kalli Dr Namir, sanan ta juya ta kalli Aaman. Ganin yadda ya sake fuskar shi ya sata itama saurin sunkuyar da kanta, haka Dr Namir ya shiga janta da wasa yana duba takardun, yana gamawa ya kalli Aaman ya ce mishi.
“Zaka iya kai ta waje ta zauna kafin na gama maka bayani!”
“Ok bari na kaita dakin Ammyn domin su biyu ne basu da Lafiya” ya fada tare da sakata a gaba, sai da ya kaita dakin sannan ya koma suka zauna. Kafin ya ce mishi.
“Kace fyade aka mata ko? Toh gaskiya babu wani abu na tashin hankali, sai dai yawan tsoron da take ji, sai kuma infection wanda naga kamar ana Æ™oÆ™arin dakile shi ko ta hanyar shan magani, sannan zan rubuta maka manyan magani antibiotics wanda zata sha na tsawon watanni, sannan zata na zuwa ganina duk bayan sati biyu. Insha Allah babu abinda zai faru sai ikon Allah ka yarda dani ba..”
Murmushi Aaman sannan ya mike yana faÉ—in.
“Toh babu damuwa, amma bana jin zan barta ita É—aya tana zuwa ganin baligin tuzuru irin ka ba, ka dai duba al’amarin, zan had’a ta da Rahmah ko Jawahir suna zuwa tare”
   “Dan iska kace bai yarda da ni bane, kawai amma meye zan mata ban da na duba lafiyar ta ” inji Dr Namir,
“Aifa abinda ba zai yiwu ba kenan na bar maka baligar mace tazo office dinka bayan kasan case din ta, da dai wani abu ne babu matsala zan iya banda haka kai ni da kaina zan kawo ta, karshen dan iska kenan.”
 Ya fada yana me barin office din,. Shi kan shi yasan waye Namir Adamu Abbas Jikamshi, wanda suke mishi lakabi da N.A.AJ bai da mutunci akan mace matukar ya ganta Masha Allah toh magana ya kare, balle kuma wannan da yaji case dinta na fyade ne. Dan haka haka zai nisanta ta dashi dan yana tsoron kar ya yaudare ta, ya kuma sakata kukan da tayi har sau biyu.
Dakin da aka kwantar da Ammyn ya shiga ya samu Mammyn da Momma sun iso, tsayuwa yayi yana jin hiran su, sama sama.
“Toh yanzu Rabi’ah tana can arewa kenan. Wannan zalincin da me yayi kama, gaskiya ya kamata hukuma ta shiga lamarin, domin zalincin tayi yawa.” Inji Momma.
Gyaran murya yayi sannan ya ce musu..
“Kunga halin da take ciki ku bar maganar Allah ya basu lafiya” ya fada tare da barin dakin.
  Maganin Jamilah ya sayo mata, sannan ya kawo mata, abincin da aka kawo ya umarci Rahmah ta zuba mata, taci ta sha maganin.
Haka Rahmah ta mike tare da gabatar da kome, sannan ta zauna kusa da ita ta fara bata, tana ci suna kallon juna abin tausayi.
  **
Bayan kwana goma, za a iya cewa jikin Ammyn Alhamdulillahi, tunda ta farka Mammy take mata nasiha da tuna mata da Allah, yasa jikinta yayi sanyi. Dan haka ta watsar da kome ta rungume Yaranta,. Yanzu haka dakin cike yake da yan dubayya, gefe guda Jadwah da Jawahir tare da Rahmah, sai hira suke, Jamilah ta can gefe tare da Wasilah tana shafa kanta.
  Shigowar Dr Namir Adamu ne ya sasu kallon shi, yana murmushi idanun shi fes akan Jamilah, a hankali ya juya tare da kaida mutanen dakin, sannan ya mika laida a bawa jamilah, tare da wani katon teddy bear.
     Mika mata Wasailah tayi tana kallon yar dollin, kafin ta mikawa Wasilah ta shige ban daki har ya karaci zaman shi bata fito ba, a tare suka fita da Aaman.
“Namir Adamu Abbas Jikamshi, ka rabu da yarinyar nan bata son alaka da da namiji please a tsayar da abun tun yanzun.”