WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
   Zai bude baki yayi magana, wayar shi tayi kara. Dauka yayi tare da cewa.
“Na’am Abba? Toh gani nan zuwa.” Yana kashe wayar ya Zubawa Aaman idanu kafin ya ce mishi.
“Ban sani ba ko kana ciki ne, idan kana ciki sai na ja da baya, dan zata dace da kai” murmushi yayi sannan ya ce mishi.
“Idan ina ciki koda wasa ba zaka tab’a samun damar kallon ta ba, domin killace ta zan yi har karshen rayuwata, dan hakan na gaya maka ni da kai ne, ka rabu da ita na san Yaudaranta zaka yi please zuciyarta yayi rauni”
Cikin jin haushi Namir ya zuba mishi ido, kafin ya sake murmushi ya ce mishi.
“Ina sonta kuma zan cigaba da sonta, ban tab’a ganin mace lokaci guda ba kamu da kaunarta ba, sai Jamilah dan haka na tsunduma a kogin kaunarta Aaman Dambatta akan idanun na zan samu soyayyar ta.”
  Yana gama fadar haka ya bar Aaman a wurin, shi kuma ya dawo dakin. Yana kallon Jamilah da Ammyn ke mata fada.
“Mutum ya kawo Miki abu ai sai ku mishi godiya ba ki tashi ki shiga ban daki ba, wannan dabi’ar babu amfani ko kaÉ—an, akwai mutanen da Allah ya jarabce su da lalura har karshen rayuwarsu haka suke komawa ga Allah basu sun Meye farin cikin rayuwa ba, kuma har su mutum basu san farin cikin ba, me yasa Allah ya baki damar farin cikin zaki dakile shi. Idan har kina son nayi farin ciki dole kema ki yarda da kaddara me kyau ko mara kyau, don Allah ki daina saka ni ganin laifin kaina a matsayin wacce ta gaza baki kulawar da ta dace.”
   Haka Mammy itama ta saka baki suka mata magana, ita kan ba wai dan bata son jin dadi bane a’a tsoro take ji, indai wanda ya dace ya baka kariya zai iya maka haka waye zaka yarda da shi? Shi yasa baki daya take tsoron mutane dan gani take kamar suma zasu cutar da ita da zuciyar ta, ba wai dan tana jin daÉ—in haka bane, kuma babu wanda zai fuskanci halin da take ciki dole sai wanda abun ta faru da shi, shi yasa suke ganin laifin ta.
**
Dutse.
 Shiru Yar duwala tayi tana kallon Dr Musa, yadda yake kwantar da murya yana rokonta ta bashi Rabi’ah.
“Eh toh zan baka ita nawa zaka ba biyan kudin aikin ta?” Cikin rawan jiki ya kalle ta kafin ya ce mata.
“Dubu takwas” shiru tayi tana kallon shi kafin tace Mishi..
“Kafin na baka ita bani kudin da zamu turawa iyayenta?” Ta mika mishi hannu, tana zukare sigari.
   “Toh nawa ne?” Ya tambaye ta,
“Dubu sha biyar ne? Idan ja kara lissafa da dubu uku ukun kai ya tashi nawa kenan.?” Ta fada tana kallon shi da kyau, tasan yana da kudin da zai biya amma bata son yarinyar ta fada hannun shi ne, domin tasan zai iya rike ta ta zame musu sharri.
“Ya tashi dubu ashirin da hudu” ya fada tare da shafa kan shi.
“Yanzun tunda tana amsar magani sai kayi hakuri yau kwanaki ashirin da daya kenan dai kayi hakuri ta gama sha ko?”
 “Toh gashi ki kirga ki gani idan bai cika ba sai na duba.” Ya kwashe kudin jikin shi kaf ya mika mata, kirgawa tayi sannan ta ce mishi.
“Ya cika zaka iya tafiya, ka kula da kanka da kuma harkokin ka, irin wannan al’amarin ba kowa yake tura kanshi cikin shi ba, kai kuma yarda da muka yi da kai tasa ka Turo kanka cikin shi, muna da goyan bayan manyan jami’an gwamnati, muna da hannu da manyan mutane, dan haka wani lokaci muna ganin abu ne mu kauda kai bawai dan bamu da yadda bamu sai dan babu wanda ya isa ta dakatar da wannan yanayin. Imma a tafi a tare Imma a zubda jinin wanda bai ji ba bai gani ba, ka ga kenan kuskure ne shiga abinda babu ruwan ka tunda ba shi kaso da mutum ba, idan lokacin yayi kazo ka É—auke ta.”
  Ta fada mishi tana me nuna mishi hanya,.dan gaskiya tana son Dr Musa, babu likitan da yake bata hadin kai irin shi, yanzn ma tayi mishi kashedi ne…
3/1/22, 18:54 – Nuriyyat: 21
“Hajiya ya zaki bar shi ya tafi bayan kin san yana Miki zagon kasa?” Inji Na maroko, murmushi tayi sannan ta ce mishi.
“Idan na dauki mataki akan shi ba zan kuma yarda da kowa bane, kuma Ba zan samu likitan da zai min irin hidimar da yake min, idan yana da hankali zai fahimci gargadin da nayi mishi.
  Sanan masu iya magana sun ce wawa ba mahaukaci bane, idan ya ci kasuwa gida zai koma, zuba mishi ido muga iya gudun ruwan shi kafin mu taka mishi birki.”
Na maroko bai so haka ba, yaso ta ce ya je da Yaran shi su, Dr Musa da iyalan shi, amma taki yaji Masifar haushi babu yadda ya iya ne kawai amma yasan while time kome zai faru kuma sai ya kaddamar mishi.
   …. Lokacin da Dr Musa ya bar gidan sosai yake juya maganar Yar duwala, shiru yayi yana nazarin abin kafin ya cigaba da tafiyar kenan tana sane da abinda ya ke faruwa ta zuba mishi ido ne kawai, dan haka ya kamata ya rufawa kan shi asiri domin fada da irin ba nasara. Idan kuma ya nace tabbas zasu kashe shi ko su illata shi ta yadda ba zai moru ba.
  Da wannan tunanin ya isa gida, yana zare idanu kamar wani mara gaskiya.
Busan. Korea republic
Yana sane yaki d’ago kai ya kalle ta, domin zata iya da shi fasa tafiyar da ya yi niyya ne, dan haka yana ta had’a kayan shi, har ya gama Um Ma bata ce kome ba, sai ma bin shi take da idanu.
“Ya kuka yi da Wango?” Ta jefa mishi tambayar.
“Babu” ya fada mata a takaice, yana d’aga suitecase din shi da wasu manyan manyan jakunan shi, yana kallon ta.
“Bilal baka ce min kome ba sai babu?” Ta tambaye shi muryan ta na rawa,
“Umma kin san zan tafi! Kuma tafiyar nan zan dawo inshallah don Allah ki barni na tafi”
    Ya fada bayan ya rungume ta, gyada mishi kai tayi tare da d’ago kan shi tana shafa fuskar shi, ta sunkuyo da goshinsa ta sumbata, sannan ta ce mishi.
“Allah ya kare ka” daga hakan ta bar shi a wurin, shima ya fito. Sannan driver da escort din shi, suka shiga kwaso kayan shi. Yana fita NaNa da Seyo Na suka rungume shi, rungume su yana jin kaunar kanen shi, kamar ya tafi da su, amma haka ba zai samu ba, sai ya magance matsalolin gaban shi kafin su samu saken rayuwa inda yake. Yasan a nan Korean dan gidan su akwai tsaro ne, shi yasa ba a iya farmakar su ba, da babu tsaro kwanan su da ya jima da karewa. Dan haka dukkan kulawar su zai tsaya anan korea bai isa a kashe masa a hali ba.
  ..
Lokacin da ya isa airport, Wango ya samu yana jiran shi, mika mishi hannu yayi suka gaisa sannan suka wuce inda private jet din shi yake ya zauna. Kafin ya ciro wata takarda me kama taswira.(map) ya baza a kan wani table da yake cikin jirgin. Sannan ya dauki pencil ya fara kallon Bilal yana fada shi.
“Wannan shine iyakar tekun atlantika zuwa Nigeria, idan har aka ce zaka shiga wannan harkallar ya zaka ji? Sannan dole fa yadda na gaya maka zaka shiga cikin su.”
   Kurawa Wango idanu yayi, shi musulmi ne baya son yayi abinda zai tab’a addinin musulunci, amma babu yadda ya iya. Dole koma meye ta shiga harkokin siyasa da kasuwanci. Idan yana son samun yadda yake bukata.
“Ok na amince, amma baka ganin haka zai tab’a darajar addinina da kimar mahaifina?”
“Ko daya idan ka isa ka tattauna da Faisal.”
“A’a bana son Faisal ya sani”
“Amma naga kamar shakikinka ne, kuma zai taimaka wurin warware wasu abubuwan, babban lauya ne ko baka yarda da shi bane?” Wango ya tambaye shi.
“Na yarda da shi!” Ya fada tare da jingina kan shi da kujeran, saukar mishi da kujeran Wango yayi sannan ya ce mishi.
“Zaka iya amfani da wannan damar domin ka nime waye yake maka b’arna.”
“Yes”
“Kuma dole zaka cire duk wani abinda ya shafi addini kayi rayuwar da ake bukata”
“Hm! Dole sai da Mata ne?” Ya tambayi Wango,
“Eh toh ruwanka ka hana little baby dinka motsi ko kuma a kiraka dan homo” zaro idanu yayi yana kallon Wango.