WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA ALKARYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
“Tir” ya fada tare d gyara kwanciyar shi, nan ya shiga mishi bayani, tare da kafa mishi duk wani abinda ya dace.
Tsaki yayi tare da komawa wurin zaman shi, yana jinjina yadda Faisal yake jure mugun halin Bilal, domin ta fara kai shi matakin da sai ya zabga mishi naushi kafin a zauna lafiya, share shi yayi tare da saka Earpies a kunnen shi. Ji yake kamar yayi ta Masifa har su isa Russian.
Karfe biyar agogon GMT suka isa garin Moscow, suna saukowa daga jirgi suka samu masu saukar su, sun zo.
  Wannan zuwan Bilal Moscow ita ce sanadiyar mai dashi wani irin mutum, (zaku fahimci haka a gaba)
**
Lagos.
Jikamshi House.
Bude mishi kofa aka yi, a nutse ya shiga yana tafiya security service na gidan suna gaishe shi, a yadda yake tafiya zai tabbatar maka da cewa shi din mugun kwaro ne, har cikin hall din ya shiga, yana zuwa ya nufi kujeran da yake gefen na Hajiya Shuwa.
  Kallon agogon hannun shi yayi tare da cewa.
“Kun kira ni nan Mother ina son tafiya Southe Africa ne” gyara zama Faisal yayi tare da kallon shi kafin ya mike ya nufi kujeran da yake mallakar Bilal Ahmad Jikamshi, ya tsayaa bayan kujeran, sannan ya buga table din. Mikewa Khalil Ibrahim Khalil yayi tare da had’a majigin dakin da laptop din shi, sannan ya amshi wayar Faisal ya hada da laptop din take kiran da Bilal yake ta shigo.
    Yana tsaye cikin wasu manyan sweater suit, kan shi dauke da wata ƙatuwar hula. Sai da yaja iska sannan ga fesar kafin ya kalle su tsaf yana me tsayar da idanun shi akan su, zama yayi yana me daura kafar shi daya akan daya, mikewa suka yi dukkan su.
Wata shu’uman murmushi ya sake yana kallon yadda suke kafin tayi musu alamar su zauna, babu musu suka zauna.
“Ina jin ku, domin kuna da minti talatin ne, idan baku nutsu ba kamar yadda kuka sani zan bar ku sai na samu lokaci.”
  Mikewa Irfan Kabir Wazir yayi Uwar shi fa mai dashi ya zauna, tare da damke hannun shi. Alhaji Adamu Abbas Jikamshi ne ya kalle shi kafin ta ce mishi.
“Batun zab’an sabon shugaban kamfanin JF Groups muke magana, sannan ana magana ne har da sauran asibitin da abubuwan da suka shafi JF Groups” yayi shiru Yana kallon shi.
“Su kenan ko akwai wasu?” Ya tambaye shi,
“Babu iyakan su kenan!”
“Ok waye kuka tsayar a Chairman din?” Ya kuma tambayar su a karo na biyu,
Juyawa Faisal yayi tare da cewa mishi.
“Gong Yoo, kowa yana son aba shi damar zama Chairman din hatta matan suna son haka.”
“Eh toh me zai hana ayi tsarin karba-karba, shekara uku idan wannan ya amsa wasu shekaru uku wannan ya amsa.” Ya fada yana kallon su.
“Haka ba zai yiwu ba, domin mahaifiyata muke son ta zama Boss Lady. JF Groups akwai hannun jarin mahaifiyata akwai nawa, akwai na kannena, sannan idan Gong Yoo bai manta ba, akwai na Alhaji Ahmad Abbas Jikamshi, kuma ita ce matar shi da duniya ta shaida, kasu mafi girma muke dauke da shi É—an haka mune zamu zabi wanda muke bukata ya zama Chairman ba kai ba” inji Irfan Kabir Wazir.
   Sosa goshi yayi sannan ya ce musu.
“Ok! Haka ma yayi amma let me bit more. Faisal Abdul Hadi Shema bude mana map na stockholders din mu ga su waye mafi hannun jari a kamfanin sannan mu zuba yadda za ayi vote din” ya fada yana duba agogon hannun shi. Bai gama duba agogon ba aka data din, shiru hall din ya dauka, kafin Bilal ya tafa suka juya gare shi.
   “Ok a ajiye kome nan da kwana uku ina hanya sai a shirya yadda za’a yi kome cikin mutunttawa.” Yana gama fadar haka ya mike tare da kashe wayar shi, suma dakin yayi duhu sai da Khalil Ibrahim Khalil ya kunna hasken dakin, a fusace Irfan Kabir Wazir ya fita daga dakin taron. Haka bai yiwa Hajiya Shuwa dadi ba, dan tasan zai zame mata ba a wurin mutanen da take nuna musu ta isa, dan haka ta mike tana faÉ—in.
“Ai wannan zalunci ne taya zaa ce matar da bata tare da mu, kuma arniya ba musulma ba ita ce take da hannun jari sama da talatin a kamfanin, sannan a kuma nuna na mu hannun jarin bai kai nata ba, gaskiya ba zai yiwu ba a sake lale”
  “Zaki iya shigar da kara kotun cinikayya da kasuwanci, sai dai kafin nan akwai wasu cike cike, kafin a samu alkalin da zai tsaya a yi Shari’a zai dauki wata uku zuwa shida, sannan lauyar da zai kare ki yana bukatar shaidu da kwararran bayanai da hujjojin ki masu kyau daga nan sai na tsayawa Gong Yoo” ya fadi haka yana had’a wasu abubuwan shi kafin ga kalli Mahaifiyar shi ya ce mata.
“Ummin mu muje ko” ya sakata a gaba, Khalil Ibrahim Khalil yana bin shi.
  Har wurin motar Hajiya Atikah ya kaita sannan ya kalli Khalil Ibrahim Khalil ya ce mishi.
“Kayi kokarin gyara gidan shi da yake can cikin gidan, ayi kome cikin nutsuwa da tsari, sannan ina babu jeka kawai” bude mishi motar shi akayi ya shiga ya zauna tare da watsa takardun a gefen shi, yana me daukar wayar shi da yaji tana ring.
“Hello! Kai dai Allah ya ganar da kai naga sakon ka, karka damu sai dai dole zaka yi wani abu karka zama azzalumi domin ta haka ne kawai zaka iya taimakawa Familyn Jikamshi. Yes haka ma daidai ne sai dai kuma gaskiya zaka gurbattani domin, toh kace ka zama boss Allah ya dawo da kai. Na fahimta dole mu musu yadda zai tafi da tunanin su gaskiya kenan, ina tare da kai a koda yaushe.”
   Sannan ya katse wayar, bai ajiye ba yaga Hamid ya kira shi.
“Ya dai?”
“Yallabai muna JF Hospital Asthma madam ya tashi wallahi.”
“Ok gani nan zuwa” ya fada da Æ™arfi, yana kashe wayar shi.
“Maza wuce dani, JF Hospital” dole suka kuma canza hanya tare da nufar asibitin su. Suna isa ko parking me kyau ba ayi ba ya fita a motar ya nufi cikin asibitin da gudu, tsabar ta rufe ko gaban shi baya gani,suka yi wani irin karo da Rahmah, kamar wacce aka cillata ta fadi tare da buge bayan ta.
“Kai makaho ne? Ji dalla zai karya ni.” Ta fada kamar zata yi kuka, cizon lip dinta na kasa tayi tana jin kamar ta zunduma ihu, bai bi ta kanta ba, escort din shi ne suka taimaka mata, ta mike, tana ture hannun su. Cikin Masifa tabi bayan shi. Koda ta isa inda yake tsaye, baki daya ya gigice musamman yadda suke mishi bayanin. Fitowar Dr Namir ne ya kira sunan ta.
“Rahmah ya dai? Jamilah ko?” Ya shiga tambayar ta a rude. Girgiza mishi kai tayi tare da cewa.
“A’a Nazo zan fita wancan ya ture Ni, kuma bai tsaya ba shine nazo naji baasin haka?”
“Ayya Kiyi hakuri, Mahaifiyar shi ce Asthma ta ya tashi shi yasa yayi haka bai tsaya ba amma ba halin shi bane.”
  “Ayya babu kome, amma kayi mishi magana ya daina yin kome a guje badan Allah ya kare ba, ai sai ya karya ni yaja min jinyar wata..”
“Namir ya jikinta? Ta manta da inhelarta ne a gida.” Murmushi Namir yayi mishi tare da cewa.
“Banza kanwar Mahaifina ce, idan ban kula da ita ba Meye amfanin aikina, karka damu zuwa gobe zata koma gida. Kafin nan ga wannan ka ture ta kafin ka shigo shi yasa ta biyo ka”
Wani jijjiga kai tayi tana faÉ—in.
“Eh ba wai bane, idan kana da karfi kamar super Man sai kayi tafiya a hankali saboda irina da ko kyakkyawan iska aka yi zai makam ya da kasa, haka ka tsallake ka wuce ko a jikinka….
3/1/22, 18:55 – Nuriyyat: 23